Tarihin garin Çanakkale da yankin Anatoliya

Labarai  da aka rubuta a cikin yaren Ozan yana bada tarihin jaruman yankin Anatolia. Ko da yake mutanen ozan sun yi gyare-gyare a lokacin da suke rubuta tarihin jaruman ama sai dai yawanci al’amurran gaskiya ne.

Tarihin garin Çanakkale da yankin Anatoliya

Da yake ba a son mutane su manta da labarin ozan, sai aka bada labaran wasu mutane da na ozan. Amma har yanzu, al’adun mutane daban-daban na cigaba da bullowa da wasu abubuwa masu kayatarwa. Ta wannan hanya ne aka samar da yadda za a yi rubutu a cikin tarihi. A yankin Anatolia, akwai tarihi mai kayatarwa da duniya baki da ke gudanarwa. Shi ya sa muka ce zamu fara wannan shirin Tarihin yankin Anatolia da baku labarin tarihin ko kuma muce taskar Troy.

Troy wani tsohon gari ne da yankin Çanakkale  a Anatolia. A yau yankin Yamma, Labarin İlyada da Odysseia da Homeros ya rubuta a yankin Izmir na daya daga cikin labaran adabi masu muhimmanci na yankin. Wannan littafin adabi na bada labarin yadda mutanen Aka da ke Girka suka kaiwa Troy hare-hare da kuma yadda kuma aka yi anfani da dokin Troy wurin mamayesu. Zai iya yiwuwa wannan shi ne farkon tarihin adabi da ya hada Gabas da Yamma wuri daya. Labarin Troy da aka dauki tsawon shekaru ana tunanen cewa wani tasuniya ce, ya zamo gaske a cikin shekarar 1880 bayan da mai tone-tonen kasar Jamus Schliemann ya gano tarihin. Shi ne farkon mutanen da ya gano inda garin Troy yake tare da yin aikin tone-tone. Ta haka ne duniya baki daya ta fara tunanen cewa rubutun Homeros ba wata tasuwaniya ba ce, al’amarin gaske ne da ya faru.

Garin Troy yana yammacin tudun Kaz. Wannan wuri da a da ake kira da Ida, inda mutum ya kalleshi a nisa, zai ga kamar tudun ya rungume Troy. Wasu labarai sun nuna cewa, haifuwan dan sarkin Troy zai zama sanadiyyar janyo matsaloli a garin Troy. Da sarki Priamos ya samu wannan labari hakan, sai a lokacin da aka haifi dan sa Paris sai ya yanke shawarar barinsa a tudun Kaz domin namun dajin sun cinyesa saboda baya son ya rayu. A lokacin da aka bar Paris a tudun sai wani mutumi ya raineshi wanda hakan ya sa ya fara rayuwa tare da wannan mutumi da bai sansa ba.  A wurin mutumin nan ne Paris ya yi rayuwa har ya girma. A wannan lokaci sai sarki Zeus ya shirya liyafa domin girmamawa ga jarumin kasar Girka Akhilleus. A lokacin da aka shirya wannan ziyafa sai aka ki kiran sarki Eris domin irin bakin cikin da yake yi. Da Eris ya samu wannan labari ya sai ya yanke shawara a fusaci akan cewa zai halarci ziyafan. A lokacin da ya halarci taro sai ya dauki daya daga cikin tuffa mai kyau a wurin taron ya yar a kasa sa’anan sai ya gudu. Bayan guduwar sa sai mutane suka fara gardama akan al’amarin da ya faru. Sai sarki Afrodit ya ce, babu wanda ya kaishi jarumta. Sai jarumi sarki Athena wanda sarki Zeus ya auri kanwarsa Hera kuma ya bayyana cewa shi ma ya fi kowa jarumta. Amma sai dai aka kasa zaban wanda ya fi kowa kyau da kuma jarumta. Sai aka ci gaba da gardama har hakan zai kai ga yaki tsakaninsu. Sai Zeus ya yanke shawarar cewa a je samu dansa Paris da ke rayuwa a tudu Kaz domin shi ya warware gardamar. Ta haka ne sai sarakai ukun suka hada kai suka shiga tudun Kaz domin neman Paris sun tambaye ya zabi sarki mafi kyau kuma jarumi. A lokacin da Paris ya bada zabinsa sai aka fara gasar kyau. An ba Paris tuffan zinariya sai sarakai uku suka fadi abinda ke ransu. Gasar da za a yi a tsakanin shi ne, Athena zai nunawa Troy yadda ake yaki inda Here kuma zai ya koya masa hanyoyin sa zai bi domin ya zama sarkin Asya da Turai. Bayan haka sai Paris ya zabi matar Athena wato Helena a matsayin mace mafi kyau kuma Afrodit a matsayin mutumin kirki. A cikin ‘yan karamin lokaci sai Paris ya kai ziyara a matsayin yarimar Trou inda zai ya sace Helen na Atina inda ya sake dawowa a garin Troy. A lokacin da Aka ya zamu labarin al’amarin da ya faru sai ya yi fushi inda ya kira jarumi Akhilleus domin ya rakashi zuwa Troy. A gefe guda kuma sai Athena ve Hera suka yi hushi saboda hukuncin da ya yanke akansu, shi ya sa sai suka goyi bayan Aka. Zaben da Paris yayi shi ne dalilin kawo karshen Troy.

To jama’a masu sauraoronmu, abokin aikin namu ya kusancemu wato lokaci kenan, shi ya sa anan zamu zuge labulen shirinmu na wannan mako sai mu hadu a mako mai zuwa domin samun labarin abin da ya faru a yakin Troy.

 Labarai masu alaka