Yunkurin warware rikicin Cyprus a Geneva

Shugaban Kasar Cyprus bangaren Turkiyya Mustafa Akinci da na bangaren Girka Nikolas Anastasiadissun halarci taron kasa da kasa na kwanaki don warware rikicin tsibirin a birnin Geneva inda aka kammala lafiya tare da bayar da hutu.

Yunkurin warware rikicin Cyprus a Geneva

Shugaban Kasar Cyprus bangaren Turkiyya Mustafa Akinci da na bangaren Girka Nikolas Anastasiadissun halarci taron kasa da kasa na kwanaki don warware rikicin tsibirin a birnin Geneva inda aka kammala lafiya tare da bayar da hutu, kuma za a ci gaba da zaman a ranar 18 ga watan Janairu.

Tun daga ranar 18 ga watan Janairu kwararru tare da ministocin kasashen waje na kasashen da suka tsayawa bangarorin biyu za su ci gaba da tattauna wa inda matukar an samumatsaya toz a a gayyaci firaministocin kasashen su ma.

Babban dai abin da aka fi mayar da hankali shi ne, shin za a samu wata matsaya a yayin taron ko kuwa a a.

A jawabin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi ga manema labarai a Geneva ya ce, “Dauloli 2 da Hukumomi 2 na tsibirin Cyprus na kan teburin sansantawa kuma ana gafda cimma matsaya.”

Babban abin ban sha’awa ga tattaunawar ta Cyprus da aka dauki watanni 20 ana yi shi ne, yadda shugabannin bangarorin biyu suka ki rufe wa juna kofofinsu tare da ci gaba da tattauna wa cikin sa ran cimma matsaya.

A Geneva ma lamarin ba wai ya sauya ba ne. Ba wai an je ba ne a ce an zauna an samu sakamako mai kyau an dakko an dawo gida ba. Kwararru da masana da suka dae suna bibiyar lamarin na Cyprus, sun san cewa, babu wani sakamakon da za a cimma a zaman na Geneva. Amma kuma yana da matukar muhimmanci a yi zaman tare da sake tabo batun a kowanne mataki.

 Za a iya cewa, a zaman da aka yi na kwanaki 3 a Geneva, Akinci da Anastasiadis sun nuna shirin su tare da sa ran za a sasanta juna.

Duk yadda wasu mutane za su ce ba za a iya cimma wata matsaya a yayin taron na Geneva ba a tsakanin bangarorin Cyprus biyu, to kar a manta cewa, a karon farko kowanne bangare ya kawo taswirar kan iyakarsa kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin tsare kowanne bangare.

A dai wannan tattaunawa ta sasanta rikicin Cyprus, akwai muhimmancia bayyana cewa, a karon farko an tattauna daya daga cikin batutuwan warware rikicin tsibirin, wato batun “Tsaro da Tsayawa bangare”.

Tsaro da Tsayawa ko garanti na da matukar muhimmanci sosai a wannan tattaunawa. Ana bayyana cewa, idan Turkiyya ta cire hannunta daga tsayawa tsibirin na cyprus a tattaunawar, t oba za a sake samun wasu abubuwa da suka faru a tsibirin a baya ba,  

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu ya bayar da wata amsa game da wannan batu inda ya ce, ra’ayin cibirin Cyprus bangaren Turkiyya daya da na kasar kanta. Turkiyya za ta ci gaba da zama garanton kasar Cyprus. Sojojin Turkiyya za su ci gaba da zama a tsibirin. Wannan bukatar al’umar tsibirin Cyprum bangaren Turkiyya ce wadda ba za su taba janye ta ba. Wannan abun na da matukar muhimmanci a rayuwarsu. Kuma mun bayyana matsayinmu karara kan wannan batu.

Antonio Guterres na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, ana gaf da kafa gwamnatin tarayya ta al’umu biyu. Wannan wani abu ne da al’umar za su jefa kuri’ar raba gardama a kansa. Ba abu ne mai sauki yin hakan ba. Kar a tsaya ana jiran sakamako yau ko gobe. Za a y izama ko ma sau nawa ta kama. Yanzu aka fara wannan tafiya. Idan muka kalli wadannan kalamai na Guterres za mu fahimci cewa, za a ci gaba da kokari da gwagwarmaya har sai an samu sakamako mai kyau na adalci.

Minista Çavuşoğlu da kansa ya bayyana cewa, ministocin kasashen da suka yi wa bangarorin na Cyprus Garanto sun gana a ayin taron Geneva kuma za su sake wani zaman a nan gaba. Bayan miistocin harkokin wajen sun samar da sakamako mai kyau a taron da za a fara a ranar 18 ga watan Janairu, Watakila to an kusa sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin tsibirin na cyprus, a wannan lokaci za gayyaci shugabannin bangarorin zuwa kasar Swidin.Labarai masu alaka