Matsalolin Kasashen Duniya

Jama'a barkanmu dai da kuma sake kasancewa a cikin wannan sabon shirin namu na batutuwan kasashen duniya.

Matsalolin Kasashen Duniya

Idan Allah ya yarda a kowanne mako za mu dinga kawo muku wannan shiri. Za mu yi tafiya mai nisa tare. Tafiya ce da mai karatu da mai rubutu da rubun kansa da ma mai sauraro za su yi tare. Ana bukatar mutumin da ka amince wa don yin tafiya tare.

Rubutu na bukatar juriya da jarumta da ma aminta da kai. Idan kuna rubutu za ku bayar da duk wani abu da kuka sani ne. Za ku be wa kanku tunaninku da zukatanku.

Rubutu ba abu ne da ya ke tafiya zuwa bangare daya ba. Abu ne da ke da madogara. Yana zuwa ne daga irin dimbin abin da aka karanta.

Rubuta abu na nufin gano sabbin wasu abubuwan. Rubuta n aba wa mai ytin sa damar fitar da abubuwan da ya sani a baya tare da karanta su. Wata tafiya ce da ke kai mutum da tudun mun tsira.

Rubutu wani balaguro ne. Ba ka san ina rubutunka zai kai k aba. Haka m aba ka me z aka fuskanta ba bayan ka gama rubutun, ba ka san ina ne z aka tsaya ba.

A wannan makon za mu kawo muku sharhin Shugaban Tsangayar nazarin Siyasa na Jami’ar Yildirim beyazit da ke Ankara Farfesa Kudret Bulbul.

A wannan tafiya da za mu yi da ku za mu zaga wurare da dama tare. Wani lokacin za mu je kasashen,  Gabas ta Tsakiya, caucasia, Afirka, Balkan, Falasdin, kremiya, Ahiska, Moro, Arakan, da duk yankunan daake zalunta na Musulmai tare da duba halin da suke ciki. A wani lokacin kuma za mu je nahiyar Turai inda za mu duba rayuwar yaran da aka raba da hannun iyayensu. Za mu zama muryar matasan da aka yi watsi da su a Turai wadanda suka yi gudun hijirta tare da neman wajen zuwa. Za mu duba yadda za a nemi mafita ga dan adam ba tare da duba Addini, yâre ko launin fatarsa ba. Saboda a yanzu halayyar da ake nuna wa a Turai tana da ban damuwa.

Amma kuma a kowanne lokaci za mu yi kokarin kallon batutuwan daga mahangar Turkiyya. Ba wai matsalolin Turkiuua ba ne, a a za mu dauki matsalolin duniya ne mu kawo su Turkiyya tare da duba su. Sau da yawa muna kallon matsalolin cikin gida tare da barin na waje. Sakamakon yadda ba mu san wacce waina ake toya wa a wasu kasashen ba, sai mu kasa ganin irin ci gaban da muka samu. Dukufa kan matsalolin cikin gida ne ya ke sanya mu kasa ganin irin albarkar da muke da ita. Akwai bukatar mu kalli abubuwan gado da aka bar mana, darajantasu tare da duba yadda suka mayar mana da Turkiyya a yanzu.

Shin a wannan batu namu ina ya kamata mu fara kalla? Wanne batu ya kamata mu fara dauka?

A yau, idan muka kalli duniya za mu gam una fuskantar manyan matsaloli guda 3 n3. Rashin Adalci, Rashin taimako da rashin rayuwa tsakanin al’adu daban-dban a waje guda. Dukkan wasu matsalolin dan adam za a iya tattara su a karkashin wadannan abubuwan 3. Shin dan Adam yana da iko ko damar warware wadannan matsaloli? Shin kowa n ayin adalci, na ciyar da makocinsa tare da zama tare da amince wa da muane ba tare da kallon Addini, launin fata ko yâre ba?. Idan da a ce dan adam na da wannan al’ada, toz a mu tafi tare a cikin jin dadi kuma zuuwa tudun mun tsira.

Adalci, Taimakekeniya da zama tare ba abubuwa ne da za mu iya daukarsu ba a cikin wayewar kasashen Turai ba. Amma irin wayewarmu za ta yi mana jagora sosai kan wannan batu. Tafiyarmu ta dubunnan shekaru daga Horasan zuwa Balkan, za ta zamar mana kamar fitilar haska teku wajen warware matsalolkin da za mu fuskanta a hanya.

Za a iya cewa, idan muka kalli shekaru dubunnai da suka gabata Istanbul ya zama daya daga cikin cibiyar bil’adama. Ba waje ne da za a ce wata al’uma daya mai tunani kwaya daya ta zauna ba, a wajen da mutane mabambanta suka rayu an fi samun riba da sosai. Saboda wadannan bambance-bambance za su taimaka wa jama’ar wajen samun damar karfi sosai. A zamanin kafa siyasa da ma kafinsa har zuwa lokacin da aka kafa sabuwar turkiyya al’uma mai tunai daban-daban ta rayu a Istanbul kamar yadda tarihinmu na kusa ya nuna. Waje ne da ya dauli Musulmai, krista, yadu da maguzawa, sanna  akwai Larabawa, turkawa, Kurdawa, Albaniyawa da na Bosniya da sauransu. Idan aka ce duba da wadannan abubuwa za a iya tattauna matsalolin ıstanbul na yau t oba abin musu ba ne.

A karni 20 da suka gabata idan aka ce mun dilmiye a cikin wayewa irin tamu, toz a a ce wayewar Turkiyya ta fi ta yammacin duniya. A nan kusa kusa wannan abu ya shafi bullar tunani a kasashen Masar, ıran da Pakistan. Babu kokwanto bibiyar abubuwan da ke faruwa a yammacin duniya tare da yin sharhi kan batutuwa na da amfani sosai. Amma sai dai masanan Turkiyya da ke bibiyar wadannan batutuwa, ba za a iya cewa sun isa su wadatar ba game da nazarin zamantakewa waje guda da zurfafa tunani kan yadda aka zauna a Istanbul ba a baya tare da warware matsalolin da ake gani. Mayafin da aka lullube Istanbul da shi a zamanin jamhuriya har yanzu ba a iya kawar da su ba.

İn haka ne, shin garuruwa nawa ake da su wadanda dan adam zai je ya rayu cikin ‘yanci ba tare da nuna masa bambanci ba. To a yanzu inda za mu ce ana bukatar haka tare da warware mtsaloli shi ne birnin ıstanbul. Dukkan abubuwan da za su zamo mana fitilar haskaka hanyar warware mtatsalolin na Istanbul. Watakila kamar yadda shahararren masanin tarihi Toybee ya fada cewa, “Sakafa da aka dakatar” ce abinda birnin Istanbul ya tara.

Birnin Istanbul da ya zama matattarar gabas da yamma a lokacin da ba a daskarar da wayewarsa ba, to zai iya zamar mana jagora wajen warware matsalolin da muke fuskanta a yau. Amma kuma a ya umun kasance ba tare da wannan abu da Istanbul ke da shi ba a wancan lokacin.

Akwai bukatar mu dawo kan wadannan darajoji tare da tafiya tare da su.

Ta haka ne za mu yi tafiyar wannan bangare.

A gefe guda mu samu zuzzurfan bincike, a daya gefen kuma mu yi amfani da haskensa wajen warware matsaloli.

Za a fassara wadannan bayanai a yaruka da yawa. Ko ma a wanne yâre, Addini kuke ko kuma wanne launin fata kuke da shi, kuma idan za ku ce za ku zo a yi wannan tafiya ta duniya tare da ku. Ku taho to mu tafi, tafiyarmu na da tsayi kuma lokacinmu kankani ne.

Mu je zuwa

Karshen shirin na wannan lokaci kenan sai mu hadu a mako mai zuwa don jin wani sabon shirin daga nan TRT hausa Muryar Turkiyya.

Mai Sharhi: Farfesa Dakta Kudret Bulbul. Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin kasa da kasa a jami'ar Yildirim Beyazit da ke Ankara.

 Labarai masu alaka