Batutuwa game da birnin Kudus

Jama'a barkanmu dai da kuma sake kasance wa a cikin shirin Matsalolin kasashen duniya daga nan TRT Hausa Muryar Turkiyya.

Batutuwa game da birnin Kudus

A wannan makon za mu yi nazari kan sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara. Kuma babban malamin namu ya yi mana sharhi ne kan birnin Kudus, matakin da Amurka ta dauka da kuma martanin da aka mayar mata.

Kudus gari ne Mai Tsarki a wajen Musulmai, Kiristoci da Yahudawa. Nan ne Alkibilar Musulmai ta farko. Nan ge garin da Annabin Rahma ya je don yin Mi’iraji. Kamar yadda mawaki Sezai Karakoch ya ke fada “Gari ne da aka kirkiri duniya aka sakko da ita ta kansa”.

Gari ne da mabiya Addinai daban-daban suka rayu a cikinsa da zaman lafiya tun bayan da Sarki Yavuz Sultan Selim ya bude garin a shekarar 1516 zuwa 1917. Wato tsawon shekaru 401 Kudus ya zauna lafiya karkashin Daular Usmaniyya. Hakan na nuni da cewa, Kudus tare da Makka da Madina ya ba wa Gabas ta Tsakiya da Sauran Sassan Duniya zaman lafiya, ba kamar yadda lamarin ya ke a yau ba. A yau Isra’ila ta mayar da Kudus kogin zubar da jini inda wasu suke wa Gabas ta Tsakiya Kallon ta kusa dilmiyewa.

Yadda Amurka ke fama da matsalolinta na cikin gida’ da yadda ta ayyana Kudus a matsayin helkwatar Isra’ila tare da daukar bangarenci ya sanya ta hade kan duniya. Duk da rashin ta ido da barazanar da Amurka wa ta yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, amma sai dukkan kasashen duniya suka yi tsayin daga wajen watsi da matakin na Amurka. A kWamitin Tsaro na Majalisar ma kasashen duniya 14 suka nuna ba sa tare da Amurka inda ta zama ita kadai. A zauren Majalisar kuma ban da Amurka kasashen duniya 8 ne suka bi ra’ayinta. Kasashen Musulmi na Duniya, KAsashen Afirka, kasashen Tarayyar Turai, na Gabas Mai Nisa da Latin Amurka duk sun hada kai waje guda.

A Amurka da Isra’ila da sauran kasashen jama’a sun la’anci wannan abu ta hanyar zanga-zanga. Kai za a iya cewa a wannan karon duniya ta samu hadin kai.

Akwai bukatar a nuna irin raar da Turkiyya da taka a wannan gabar a matsayinta na kasar da shugaban Kungiyar Kasashen Musulmi a yanzu. Yana da matukar muhimmanci yadda shugaba Erdogan ya tattauna da shugabannin kasashen Turai, Papa, Putin da sauron mahukunta inda suka dauki mataki irin daya. Kudus ya hade kan wasu kasashen Musulmi da suke da matsala da juna a baya. Ya sake samar da wata matsaya tsakanin Kasashen Tarayyar Turai da Kasashen Musulmi.

Hukuncin AMurka game da Kudus, za mu yi fatan ya zama wani abu da ya farkar da duniya game da kasar Falasdinu. Yadda Kasashen duniya suka yi watsi da ra’ayin Amurka, muna fatan su yi amfani da irin wannan hali wajen cewa, ana karar da Falasdinawa sannan akwai bukatar tabbatar da hakki a yankinsu.

Da a ce duniya ba ta jajirce ba? Ko kuma da Kudus ya rushe…..

Matakin da Amurka ta dauka kan Kudus ya zama babban misali na abun daka yi masa kallon sharri ne amma kuma Alheri ya fito daga cikinsa.

Da a ce ba a nuna kafiya da jajircewa ba, kamar yadda marigayin Erbakan ya ding ajan hankali da cewa, wata rana Isra’ila sai ta mamayi dukkan kasashen yankin tare da kai wa ga gabar tafkin Dicle da Firat. İdan aka yi tunani da duba da irin barazanar da ake wa yankin, to lallai Isra’ila na son kasaita kuma za a ga irin barazabar da ta ke yi sosai.

Yahudawan Zionist ‘yan kama guri zauna da ke tutiyar bin tsai mai kyau tare da cewa, su ne jinsin dan adam mafi daraja, to Yahudawa da ba sa zalunci da nuna wariya sun gano su tare da yin farga. Kowa yana sane da yadda ra’ayin Hitler na Nazi da ke cewa, al’umar Jamus su ne suke gaba da kowa ya janyo matsaloli ga duniya. Da a ce ba a nuna kafiya da jajircewa wajen watsi da matakin Amurka kan Kudus ba, to da an samu wasu jinsin mutane da ke jin sun fi kowa daraja da kima a doron kasa.

Yadda Kasashen Musulmi da na Turai suka mayar da martani ga matakin da Amurka ta dauka kan Kudus, ya nuna cewa, kasashen Musulmi da na Turai na da alakarsu da ba ta bukatar lallai sai an sake kulla ta.

Da a ce ba a nuna kafiya da jajircewa wajen watsi da matakin Amurka kan Kudus bat o da an samut sarin da ba na taimakawa wanda aka zalunta ba, a a na mai karfi ya sake yin karfi. A yanzu yankunan da ake zalunta za su sami karfin jajircewa da bijirewa azzalumai.

Da a ce kasashen duniya ba su nuna karfi game da Kudus ba, to da rashin katabus sun kara karfi, kuma wadanda ake zalunta sai su sake fitar da rai daga samun mafita.

Da a ce al’uma sun zauna kawai suna kallon wannan hukunci, ta ya ya za a yi sojojion Isra’ila su iya kallon idanuwan jarumar Falasdin Aheed?

A lokacin da ake bijirewa rushe gidajen Falasdinawa da Isra’ila ke yi a Gaza, to waye ya ke da alhakin tatsile Ba’amurke mai shekaru 24 Rachael Corrie.

Bai kamata Tsarin Yahudawan Nazi ya dawo ba, döle ne a magance Yahudancin Nazi…

Shin tsaya wa a iya haka ya wadatar?

Hakika bai wadatar ba, saboda idan Kudus ya fado ya rushe to duk wadannan abubuwa da aka zayyana a sama m aza su fado su rushe.

Domin kar birnin ya rushe döle ne Yahudawa masu rajin ba wa kowa ‘yanci su jajirce. İn ba hak aba to su ne za su fara yin asara. Kamar yadda Jamusawa masu ra’ayin ‘yanci ne suka fara asara a lokacin Nazi. ‘yan adam sun sha wahala sosai saboda ra’ayin Nazi na Jamus. Bai kamata a sake fuskantar wanna matsala ba saboda son zuciyar Yahudawan Nazi.

Kamar yadda aka gani matsalar Kudus ta Musulmai, Kiristoci da Yahudawa kawai ba ce, matsala ce da ta shafi dan adama baki daya.

Idan Kudus ya rushe to adalci, hankali da Insaniyya ma za su rushe….

Sharhin Farfesa Dakta Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke AnkaraLabarai masu alaka