Halin da kasar Siriya ke ciki da barazanar da 'yan ta'adda ke mata

Jama'a barkanmu da sake kasance wa da ku,a cikin shirin Matsalolin kasashen duniya, daga nan TRT Hausa Muryar Turkiyya.

Halin da kasar Siriya ke ciki da barazanar da 'yan ta'adda ke mata

A wannan makon, za mu yi nazari kan sharhin Farfesa Kudret Bülbül,Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa na Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara.

A makon da ya gabata,babban malamin namu ya yi mana sharhi ne kan birnin Kudus, matakin da Amurka ta dauka da kuma martanin da aka mayar mata. A yau, shirinmu ya karkata ne kan rikicin kasar Sham.

A wasu lokuta, ana daukan manyan darussa daga biyan manyan diyyoyi, har ta kai ga mutum ya dinka nadama yana cewa: “Ina ma a ce ban biya wadannan diyyoyin ba, da ban dau wadannan darussan ba”.Fadawa a irin wannan halin, watakil zai yi nasaba ne da rikicin Siriya, wanda ya bai wa duniya manya-manyan darussa,masu cike makil da abin bakin ciki.Kamar sauran kasashen Larabawa,iskar juyin-juya halin da ta mamaye rufaffun kasashe, ya rusa da Sham.A daidai lokacin da al’umar siriya wacce ta kasance a karkashin inuwar bakin mulkin kama karya,ta yi kokarin daga kanta,ba ta yi kacibus da komai face karfin soja,wanda da aka yi amfani da shi a wajen murkushe ta.

Turai ta nuna aniyarta a karara”

Rikicin Sham ya yi matukar kazancewa,sabili da kusa kai da Iran ta yi tare da sojojinta a wannan yakin,tallafin da gwamnatin Asad ta samu daga Rasha, da kuma rashin kyaukyawar aniyyar kasashen Yamma a wajen warware bakin zaren fitinar da ta mamaye Siriya.Wannan lamarin ya zama sanadiyyar mutuwar daruruwan dubunnan mutune,wadanda da basu ji ba basu gani ba,da kuma tirsasa wasu milyoyi daga cikin su, yin hijira daga kasarsu.Kasashen Turai, kusan ba su tabuka komai ba game da rikicin Siriya, har ya zuwa lokacin da masu neman mafaka suka tunkari iyakokinsu.Bayan masu neman mafakan Siriya sun kwakwasa a kofofin kasashensu,halin da Turawa da suka nuna, babban abin kunya ne ga bil adama.Al’umar Turai wacce a baya take ci gaba da bai wa duniyya darasi game da zama tare,adalci, ‘yanci, da kare hakkokin bil’adama, ta fadi warwas a wannan jarrabawar farko,a lokacin da aka bukace ta da tabbatar da ababen da ta jima tana da’awa, a aikace.Ta nuna cewa,masu neman mafaka basu dace ba da wadannan hakkokin.Burin da turawa suka sa gaba kawai, ita ce hana masu mafaka kwararowa kasashensu.Bayan wannan matakin, garwawakin da teku ta amayar ,ba wai na jinjirai marasa gata,marasa karfi da dabara kamar Aylan (jaririn Siriya) ne ba,a gaskiya wadannan su asalin halayya da kuma dabi’un da Turai ke tunkaho da su.

Turkiyya: Kasa mai taka muhimmiyar rawa a demokradiyyar Turai

Bari mu yi tunanin cewa,kamar yadda kasashen Turai suka yi, Jordan,Lubnan da kuma Turkiyya ma, sun rufe wa masu neman mafakan Sham iyakokinsu.A wannan lokacin miliyoyin masu neman mafaka zasu yi kokarin tsallake iyayokin Turai.İdan muka yi la’akari da yadda, tunanin Farkisanci da na Naziyanci ke ci gaba da karuwa a kasashen Turai, wadanda masu neman mafaka kadan ne suka samu zuwa can,ga dukannin alamu, matsalolin da suka danganci halayya da kuma mutunci Turai zasu zurfafa sosai.Duk da Turkiyya ita daya tilo, ta karbi bakwanci Siriyawa milyan 3.5, kana ta gabatar da bayyananniyar siyasa game da rikicin Sham,kuri’un masu bin sisayar wadannan jam’iyoyyi na ci gaba da karuwa.Yawan masu neman mafakan da yankin Kilis na kasar Turkiyya ya karba, sun zarce yawan wadanda yawancin kasashen Turai suka karba.A lokacin da wata kasar Turai ta ce , za ta karbi bakwancin masu neman mafaka 130, gwamnan Kilis ya ba ta wata gaggarumar amsa wacce zata kasance a cikin tarihin duniya,inda ya :”Wannan kasar, kar ta matsa wa kanta,zan iya karbar bakwancin mutane 130 a gidana”.A Turai kuma, masu kaymar,bakin haure,da kuma Islama suna ci gaba da gogayya da juna su, don yin amfani da wannan damar a wajen samun yawan kuri’u.Jam’iyyar siyasa mai taken “Ba zamu karbi bakwancin bakon haure ko daya ba” ce ta zo ta farko a zabukan kasar Ostriya.A sassa da dama na Turai,jam’iyyoyin Frakisanci da kuma Naziyanci ne ke a sahun gaba,inda wasu a kasashen kuma, suka kulla kawance.A kasashe da dama,don kar jam’iyyoyin dama su yi karfi, ‘yan ra’ayin tsakiyar dama da ‘yan hagu,sun kara tsaurara ra’ayinsu.Ko shakka babu, wannan matsalar na kunshe da hadurra da dama,musammam ma ga Turai wace kowace safiya take ci gaba da kadaicewa tare da tsunduma makomarta cikin duhu.Idan a yau, a Turai, jam’iyyoyin siyasar da ke wuce gona da iri na iya hawa kan karagar mulki,wannan ba komai ba ne, face muhimmin matsayin da Turkiyya da wasu kasashen gabas ta Tsakiya suke da shi game da batun masu neman mafaka.Rashin zuwan kusan dan Siriya ko daya, kasashen Iran da na yankin Gulf,abu ne da ke bukatara yara tambaya.

Mummunar farfaganda game da hare-haren “Reshen Zaitun”

A cikin batu na gaba,duk da kungiyar ta’adda ta Daesh ta sha kashi,maimakon masu fada aji na duniya su samar da tsare-tsaren magance matsalar Sham,sai kara dukufa suke a wajen hura wutar rikicin.Abin takaici,wannan lamarin ba Siriya kadai ya shafa ba.Kamar a kasashen Afganistan,Irak da kuma Libiya,babu wata kasa daya tilo wacce ta samu kwanciyar hankali sabili da sa hannun gambizar kasahen duniya. Akasin haka, tare da mutuwa, kwalla, yawan hijira, wadannan kasashen na zama tamkar jahannama ga wadanda ke bukatar zama a cikinsu.Kuma kasashen wannan yankin ne ke biya diyyar wannan annobar.Shi yasa,idan ana son a magance irin wadannan matsalolin, to ba wai damawa za’a yi da kasashen duniya wadanda babu wata asara da zata shafe su, kamata yayi a nemi kasashen yankin da abin ya shafa.Duk da Daesh ta sha kashi,kana kurar yakin basasa na shirin lafawa,bai wa ‘yan ta’addar PYD/YPG dubban tireloli masu cike makil da makamai da kasar Amurka ta yi, tare da bayyana cewa, zata maida YPG wata babbar “Bataliyar Kan iyaka”,abu ne wanda kasashen Turkiyya da takwarorinta na gabas ta tsakiya suka ki amincewa da shi.

PKK da PYD kungiyoyin ta’addanci ne wadanda suka kashe daruruwan dubban mutane a Turkiyya da sauran kasashhen gabas ta tsakiya.Kamar yadda Amurka ba zata so a bai wa kungiyar ta’adda ta Al’Ka’ida ta Usama Ben Laden muhalli kan iyakarta ba,kamata yayi ta gane rashin yardar Turkiyya da sauran kasahen yankin gabas ta Tsakiya game da batun bai wa PYG makamai da kuma maida ita “Bataliyar Kan iyaka”.Don kare kanta,samar da kwanciyar hankali a gabas ta tsakiya,kubutar da mutanen wannan yakin daga sharrin YPG, da kuma yin riga kafi game da wasu milyoyin mutane da ka iya yin hijira zuwa kasarta, Turkiyya ta fara kaddamar da hare-hare “Reshen Zaitun”.Fara wannan halattatun hare-haren da Turkiyya ta yi,na ci gaba da cin karo da wasu cibiyoyi da dama.Daya daga cikin dalilin kaddamar da hare-haren “Reshen Zaitun” shi ne ,kare martabar Siriya a matsayinta na dunkulalliyar kasa daya tilo.Domin kungiyar ta’adda ta PYD/YPG mai samun goyon bayan Amurka, na ci gaba da mamaye daga Irak har ya zuwa Tekun bahar Rum,da nufin raba kasar Sham.

Ana ci gaba da nuna gwagwarmayar Turkiyya ta kauta ‘yan ta’adda, a matsayin yaki da kabilun Kurdawa.Kamar yadda yaki da Usama Ben Laden, ba yana nufin yaki da Larabawa ba, haka nan yaki da ‘yan ta’adda, ba yaki da Kurdawa ba ne.Turkiyya ba zata taba yarda wannan kungiyyar ta ‘adda wacce ta share shekaru da dama tana zubar jini ta samu mafaka kan iyakokinta ba.Sanin kowa, kungiyar ta’adda ta kasar Siriya PYD/YPG ‘yar uwa ce ga PKK,kana ta zubar da jinin Kurdawa da dama wadanda basu bata goyon baya su ba.PYG/YPG na ci gaba da yi wa Kurdawa,Larabawa,Turkmen da kuma wadanda ba Musulman na yankinta kisan gilla, sabili da sun ki mara mata baya.Milyoyin mutane da suka ceto rayukansu, na gudowa don zuwa Turkiyya da wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.Shi yasa,ainahin ayar tambayar da yakamata mu dasa anan, ita ce : Shin me yasa, Kungiyar ta’addar wacce ‘yar gabar goshin Amurka ce, ta ki yarda Siriyawa su koma kasarsu ?.Yana daga cikin manufofin Turkiyya, neman kofar mayar da Siriyawa kasarsu ta ainahi, ba tare ta nuna wariyar launi fata ko kuma addini ba.Kamar dukannin yake-yake, babu makawa wannan yakin ma zai kare.Amma muhimmin abu a nan shi ne, idan wata rana muka waiwaya baya,ko da yake a yawancin lokuta bama nasara,mu san a irin wadannan yake-yaken,wadanne daga cikin ababen da muka bar ‘ya’yanmu,zamu iya karewa ko kuma cetowa.

Sharhin Farfesa Dakta Kudret Bülbül,Shugaban Tsangayar Nazarin Harkokin Kasa da Kasa ta Jami’ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara ya yi mana kenan.Labarai masu alaka