Hare-Haren Reshen Zaitun da Turkiyya ke kai wa a Afrin don yaki da ta'addanci

Turkiyya ta dauki matakin kare iyakokinta domin karfafa tsaron cikin gidanta dama kauda kalubalolin da ‘yan ta’addar PYD/YPG su ka kwashe shekaru su na aiyanarwa a kasar Siriya.

Hare-Haren Reshen Zaitun da Turkiyya ke kai wa a Afrin don yaki da ta'addanci

Turkiyya ta dauki matakin kare iyakokinta domin karfafa tsaron cikin gidanta dama kauda kalubalolin da ‘yan ta’addar PYD/YPG su ka kwashe shekaru su na aiyanarwa a kasar Siriya. Da hakan ne Turkiyya ta fara kaddamar da hare-hare a yammacin Afrin. Da izinin shugaban kasar Turkiyya rundunar sojar kasar  a ranar 20 ga watan janairu da karfe 5 na yamma sun ka soma kaddamar da hare-haren da akawa taken “Reshen Zaytun” domin kauda ta’addanci a yankunan Afrin din Siriya

Afri da ke makwabtaka da Turkiyya, a kidayar jama’ar shekarar 2004 ta na da al’umma dubu 64,758, a yayinda yankin gaba daya ke dauke da al’umma dubu 175.092. A dalilin gwamatain Asad bata kaddamar da hare-hare a yankin ba, ya sanya ‘yan gudun hijira yada zango a yankunan Afrin. A yanzu haka ana hasashen mazauna yankin sun kai kusan dubu dari uku.

Wannan yakin ya kasance gurin yada zangon kungiyoyin ta’addanci dake kwarara zuwa yankunan Madeterenian. Haka kuma kungiyoyin na ketawa ta tsaunukan Amanos domin isa Turkiyya da kuma fasa kwaurin makamai. Kawo yanzu dai sojojin kasar Turkiyya sunyi nasarar kashe fiye da ‘yan ta’adda 40 a yankin.

Haka kuma rundunar sojan kasar ta yi nasarar  tarwatsa maboya da ma’adanar makaman ‘yan ta’addar PKK/KCK/PYD-YPG har kusan 108 ta amfani da jiragen yaki 72.

Wannan hare-hare mai taken reshen zaitin da Turkiyya ta soma tare da haddin gwiwar sojojin Siriya ma su zaman kansu, ta yi nasarar kauda ‘yan ta’adda daga yankunan da dama. Tsaunukan yankunan na daga cikin muhimman guraren da ake neman karbewa daga hannun yan ta’addar; a yayinda kawo yanzu anyi nasarar zagaye tsaunukar domin kange yan ta’addar YPG.

A dai-dai lokacin da aka shiga cikin kwana na biyar da fara hare-haren, ‘yan ta’addar PKK/YPG sun fara buya a cikin fararen hula domin batar da sawu. Hana fararen hula kaura daga yankin da ‘yan ta’addar ke yi na gaskanta cewar su na amfani da su domin kange yakar su da ake gudanarwa.

Baya ga matakan soja, ana kuma daukar matakan diflomasiyya domin samar da lumana a yankunan. Rasha na ci gaba da kare wasu sarararin samaniyar Siriya kamar yadda ta yi yarjejeniya da kasar. A yayinda Turkiyya ke kara dauklar matakan kare yankunan Afrin daga dukkan yan ta’adda.

Turkiyya ta tattauna da kasashen Nahiyar Turai, kasashen yankin  Gulf, Rasha da Amurka akan lamarin. Bugu da kari ta kira jakadojin kasashe daban-daban dake kasar a ma’aikatarta ta harkokin waje domin sanar da su akan hare-haren. A dayan barayin kuma, ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta gana da Faransa akan yukurin ta na kai lamarin a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, inda kuma ta kalubalanci yunkurin wasu masu goyon bayan ‘yan ta’addar PKK dake niyyar karar hare-haren a kwamitin nahiyar turai.

Duk da Amurka ta fitar da bayanai daban-daban game da hare-haren reshen zeitin din, ana ganin cewa ba ta gamsu da hare-haren ba. Birtaniya, Jamus da NATO dai su na kallon hare-haren reshen zaitin din a matsayar halattacciya, A yayinda  Rasha ke zargin Amurka da hadasa rikicin kasar Siriyar.

Rubutun Can AcunLabarai masu alaka