Nasarar Erdoğan da Manufofin Turkiyya a Kasashen Waje

A ranar 24 ga watan Yuni ne aka gudanar da zaben shugaban kasa dana ƴan majalisu a kasar Turkiyya. Duniya ta maida hankalinta akan sakamakon zaɓen da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya lashe da kaso 52.6 cikin ɗari a zagayen farko.

Nasarar Erdoğan da Manufofin Turkiyya a Kasashen Waje

Zaɓen da  zai haifar da sabuwar tsarin mulki a ƙasar, Jam'iyyar AK party da jam'iyyar MHP suka yi nasarar samun rinjayen ƴan majalisu. Duniya dai ta sanya ido akan zaɓen da zai haifar da tsarin mulkin shugaban ƙasa a ƙasar wanda ya samu halartar kaso 87 cikin ɗari, wannan nasarar da Erdoğan ya samu tare da jam'iyyun da suka yi haɗaka na nuni ga ci gaba akan bunƙasar da hurɗar Turkiyya da kasashen waje da kuma ƙalubalantar ta'addanci.

Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Malam Yazar Can ACUN daga cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA .

A ƴan shekarun da suka gabata, hurɗar Turkiyya da sauran ƙasashe da kuma harkokinta na cikin gida sun bunƙasa. Turkiyya wacce a gefe guda tana gudanar da ayyukan bai ɗaya da ƙawayenta na kungiyar NATO, ta kasance kuma a gefe ɗaya tana aiyuka tare da ƙasashen Rasha da lran, haka kuma Turkiyya ta na ci gaba da ƙarfafa hurɗarta da kasashen yankin nahiyar Afirka, Balkan, Gabas ta Tsakiya da Asiya. Ababen da suka ƙarfafa hurɗar kasar Turkiyya da sauran ƙasashe sun haɗa da irin tallafin da take bayarwa da kuma matakan da take dauka akan samar da tsaro. Turkiyya wacce take ta 13 a jerin kasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya, ita ce ta farko a fagen bayar da tallafi a yayinda Amurka ke binta a baya, Turkiyya na bayar da ire-iren waɗannan tallafin na bunƙasar dan adam kasancewar yadda take daukar bil adama da muhimmaci kwarai da gaske.  

A ɗayan barayin kuma, Turkiyya na daukar matakan samar da tsaro, lamarin dake ƙara ƙarfin hurɗarta da sauran ƙasashe. Sayar da jirgin yaƙi mai saukar ungulu kirar ATAK ga Pakistan da kuma damar sayar da motocin yaƙi ga kasashen gulf da kuma iya ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙa da Turkiyya ka iya yi sun nuna irin nasarorin da kasar ta samu a fannonin tsaro.

Sakamakon zaɓen ranar 24 ga watan Yuni bai kasance ba facce wani haske ga bunƙasa hurɗar ƙasar da kuma ci gaba da samar da tsaro. Zaɓen na nuni da al'umar ƙasar Turkiyya zasu ci gaba da baiwa mabukatar kasar Somalia tallafi.

Haka kuma sakamakon zaɓen na tabbatar da cigaba da yaƙi da ta'addanci da kwarin gwiwa. Bayan kauda kungiyar DEASH a yayin hare-haren Firat Kalkanı, an kuma gudanar da hare-haren reshen zaitun inda aka fatattaki kungiyar ta'addar YPG-PKK a yankin Afrin ɗin Siriya. Hare-haren da aka fara gudanar wa a lraqi domin kauda ƴan ta'addar PKK daga yankin Kandil za'a ci gaba da shi. Sakamakon zaben na dai kara nuni ga ci gaba da ƙalubalantar ta'addanci cikin gida da waje. Sabbin matakai uku da aka dauka domin kauda ta'addanci sun yi nasarar rage ƴan ta'adda daga yankunan kwaran gaske.

Haka kuma, Turkiyya ta kulla yarjejeniya da Amurka akan kauda ƴan ta'addar YPG daga yankin Membich. Ƙasashen biyu wadanda dukkanninsu mambobin NATO ne zasu yi haɗaka domin samar da tsaro mai inganci a yankin Membich. Wannan yarjejeniya da aka gudanar kafin zaɓen ranar 24 ga watan Yuni da ya baiwa shugaba Erdoğan nasara za'a ci gaba da aiyanar dashi da ƙwarin gwiwa a halin yanzu. Haka kuma, zamu iya cewa yarjejeniyar Astana da Turkiyya, lran da Rasha suka kasance kasashen lumana domin kawo karshen rikicin Siriya za'a ci gaba da aiyanar da shi. Daga karshe dai wannan sakamakon zaben zai kauda dukkan ruɗani da ƙasar Turkiyya ke fuskanta tare da samar da daidaito da kuma inganta dukkanin yarjeniyoyin da ta kulla da sauran ƙasashe.

Wannan sharhin Mal Yazar Can ACUN ne daga cibiyar nazarin ilmin siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.Labarai masu alaka