Matafiyi a Zamanin Batacciyar Sakafa: Fuat Sezgin

Sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim beyazit da ke Ankara ya yi mana.

Matafiyi a Zamanin Batacciyar Sakafa: Fuat Sezgin

Matsalolin Kasashen Duniya: 27

Farfesa Fuat Sezgin da ya shafe rayuwarsa wajen bayar da gudunmowar Musulmi a fagen kimiyya ya rasu a makon nan yana da ahskearu 94 da haihuwa. Irın abubuwa da ya bari da za a gada wanda ya samar a cikin shekaru 94 na da wahala a samar da su a rayuwar mutum da ya yi ta wannan lokaci. Fuat Sezgin mutum ne ya dinga aiki kamar agogo ba dare ba rana kuma ya dakata kawai a lokacin da ajali ya yi halinsa.

Mene ne abin da ya bambanta wannan malami?

Tafiya zuwa Duniya a Bitlis..

An haifi Malami Fuat Sezgin a shekarar 1925 a Bitlis. Ya fara samun Ilimin Arabiyya da Addini a wajen mahaifinsa wanda ke aiki a ofishin bayar da Fatawa na gundumarsu. Bayan shekarar 1943ya halarci sashen nazarin adabi na jami’ar IIstanbul, inda ya ci gaba da nazari a sashen nzarin Gabas t sakiya. A wannan waje ne ya hadu da dan kasar Jamus Helmutt Ritter da ke nazari kan Kasashen Gabas da Al’umunsu.

A wasu lokutan abu mara kyau na haifar da alheri

A lokacin da Fuat ke ci gaba da aiyukansa na karatu, bayan juyin mulkin 1960 an kore shi daga jami’arsa kamar saura malamai. Laifinsa kawai shi ne dan uwansa ne shugaban jam’iyyar DP na lardinsu.  A lokacin da Malam ya ke shekaru 36 kuma ya ke da ilimi ya zama matashi mara aikin yi a kasa kuma ya rasa yadda zai yi. Amma kamar kowanne lokaci, mutanen da suke da jajircewa, dabara da fasaha, ilimi da nagarta ko da an rufe dukkan kofofin da suke kasarsu, to za su samu damar bude wata kofar. Bayan wasu shekaru Malam Fuat ya zama mai godiya ga sojojin da suka kore shi daga aiki. Ya fada musu cewa “Ba na kaunar siyasarku amma ina gode muku bisa korata da kuka yi daga aiki domin da ba ku kore ni ba da ba zan yi aiyukan Ilimi da nja yi a Jamus ba.”

A duk lokacin da aka rufe masa kofofi sai ya samu gayyata daga Jamus da Amurka. Ya zabi zama a Jamus yadda zai iya zuwa Turkiyya ya tafi. A aiyukan da ya yi a wannan waje ya yi su kan tarihin Musulunci da kimiyyarsa, watakila a duniya wannan ne kimiyyar dan adam mafi daraja da aka taba gani.

Shin babu Musulmai a tarihi?

Idan aka kalli rayuwar Malam Fuat za a ga mutum ne da ya bude dukkan duniya a ilmance. Ya kasance yana kai komo daga wannan dakin karatu zuwa wancan. Bai ba wa wani abu muhimmanci ba, tsawon shekaru kawai aiyukan kimiyya ya mayar da hankali a kai. Kamar yadda ya fada yawancin lokacin yana cin biredi da cukwui ne kadai a lokacin cin abincin rana.

Shin ne mene abinda ya sanya Malam Futa aiki fiye da yadda dan adam ya saba? Kamar yadda ya ba wa kimiyya da ilimi muhimmanci, to haka ya amnce da wasu abubuwa da suke faruwa a zamanin yau na kmiyyar ilimi.: wato cewar a wannan zamanin Musulmai ba su bayar da gudunmowa a duniyar kimişyya ba kuma kimiyya da fasahar kere-kere ta yau ta shafi Girka da Turai ne kawai. Ya ce, ya fara samun wannan abu na karya a lokacin da ya fara makarantar Firamare: “A mako na 2 ko na 3 na aji 1 na maakarantar Firamare malamarmu tana koya mana wai duniya a dunkule ta ke waje guda kuma wai malaman Musulunci sun amince cewa duniya na nan a kan wuyan wani bijimin sa ne. To ne yaro talaka ya akai bayan shekaru 30 na samu damar fahimtar Musulmai tun a akrni na 9 sun auna tsayin layin da ya raba duniya biyu na Equador wanda ke da tsayin kilomita dubu 40?

A aiyukan da Malam Fuat ya yi a rayuwarsa ya bayyana irin gudun mowa da Musulmai suka bayar a fagen kimiyya. Ya bayyana karara irin tsantsar gudunowar da Musulmai suka bayar da ma yadda falsafar kimiyyar Girka ta samo asalidaga Musulmai zuwa zamanin yau.

Duk da wadannan rayuwarsa ba ta tsaya a tarihi kawai ba. Abin takaici ne yadda a kasashen Yamma aka fi kasashen Musulmi duba da amfani da Aiyukan da Malam Fuat ya yi a bangaren ilimin tarihin Musulunci.

Mutumtaka, tsari da gudunmowarsa

Fuat Sezgin ya tasirantu da ra’ayi da tsarin yin aiki irin na Ritter. Bayan ya hadu da Ritter ya ji sunan Malaman Musulunci da bai taba jin su a baya ba. Da ya fara aiki da Ritter ya tambayi Malam awa nawa ya ke aiki a rana. Sai ya ba shi amsa da cewa 1314 sai ya ce masa to ba za ka zama Malami a haka ba. Bayan Malam ya kara shekaru sai ya kara awannin aikinsa zuwa 17-18 a kowacce rana. A saboda haka mutuntakarsa ta fako da za a iya fada ia c mutum ne da ba ya gajiya ko tsaya wa hutawa idan yana aiki.

Wani abu da za a iya sake gani tare da Malam Fuat shi ne, yadda wani abu da ake yi  ‘Yan shekarun nan na nuna adawa da Sakafa da Kimiyyar Musulunci a kasashen yamma,amma shi sam bai ba wa wannan halayya muhimmanci ba. Malam Fuat na nuna cewa a zamaninda Malaman Musulunci suka yi fice a bangaren Kimiyya suna da dogaro da kawunansu. Saboda haka koma wanne yare, Addini ko launin fata malaman kimiyya suke da shi dole ne a ba su matsayinsu na irin gudunmowar da suka bayar.  

Babu kokwanto Malam ya yi rubuce-rubuce na mujallai da dama game da irin gudunmowar da Malaman Musulunci suka bayar a duniya kimiyya. A tare da hakan, Malan ba wai Malamin Kimiyya ne kawai ba. Mutum ne da a bangaren nazarin jami’a a Frankfurt ya kafa “Cibiyar Nazarin Tarihin da Kimiyyar Larabwa-Musulunci”. Ya kashe dukkan kudaden da ya ke samu a wannan hanya. Hakan bai isa ba, sai da ya kafa gidajen ajje kayan tarihi na Gudunmowar Malaman Musulunci a bangarorin Kimiyya da fasaha a Frankfurt da Istanbul.

Jamus Biyu

 Lokacin rayuwar Malam Fuat Sezgin yana da wuraren zama da yawa a Jamus. Da fari bayan an yi juyin mulkin 1960 a Turkiyya tare da rufe kofofi, yana da bashin da zai biya Jamus da ta ba shi dama a bangaren tarihin kimiyya. Malam Fuat yana yawan yin godiya game da wannan abu. Jamus ta amince da shi tare da ba shi gudunmowa kan wannan aiki ba tare da samun wata matsala ba. A saboda haka dole ne a yaba wa Jamus ta wancan lokacin. Amma matakin da Jamus ta kawo a yau ya nesanta da tsrin da ta ke kai a baya. A lokacin da aka so daukar dakin karatun da ya kafa don dawo da shi Turkiyya sai Jamus ta ke inda ta ma shigar da kara kotu. Ta saka muklli ta rufe dakin karatun tare da hana kowa shiga. Amma duk da haka Malam Fuat ya ci gaba da kokarin gtanin kar a siyasantar da wannan abu. Bai dauki batun ga idaniyar jama’a ba. Idan aka kalli jamus a da, da kuma abinda aka yi malam Fuat a yau  za a ga cewa, jamus na kara gaba amma kanta na shige wa duhu ne.

Nan da wasu lokuta masu zuwa duniyar Turkawa da ta Musulunci ba ta gama gtano waye Malam Fuat Sezgin ba. Saboda wannan duniya ba ta gano abubuwanda ta rasa sanna ba ta gano abubuwan da Malam Fuat ya samar ba. Duk da aiyuka da rubutun da Malam Fuat Sezgin ya yi amma ya bar duniya ya tafi ya kyale mu.

Allah ya sa Aljanna ce makoma Ameen!

Sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim beyazit da ke Ankara ya yi mana.Labarai masu alaka