Sojojin gwamnatin Siriya sun nufarwa garin Dera

Gwamnatin Siriya dake samun taimakon gwamnatocin Rasha da lran na ci gaba da kai hare-hare a yankunan Dera dake kudancin ƙasar.

Sojojin gwamnatin Siriya sun nufarwa garin Dera

A yayinda dakarun Siriya ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan Dera fararen hulan yankin tuni suka fara ƙaura zuwa iyakokin Jordan. Kasancewar iyakokin Jordan da Siriya na rufe ya sanya fararen hulan yankin cikin halin ƙaƙanikayi. Duk da waɗanda ke ƙalubalantar gwamnatin Siriya sunyi wata haɗaka, amincewa da Rasha a  matsayar ƙasa mai shiga tsakani da kuma rashin ƙalubalantar sojojin Siriya ya baiwa dakarun Siriyar damar karɓe ikon wasu birane ba tare da wata ƙalubale ba. Wani lamarin dake jan hankali a Siriya shi ne rigingimun dake tsakanin lran da lsra'ila, kusantar da Isra'ila ke yi wa yankin Siriya ya sanya magoya bayan lran ƙalubalantar ta abinda ke haifar da tashin hankula a yankunan.

Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da ferfesa Yazar Can ACUN dake Cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA.

Hankula sun koma akan yankin Dera bayan dakarun Siriya ta fara kai farmaki a yankin a watan Yuni. Duk da irin wannan yanayin ba'a samu wata ƙalubalantar juna ba tsakanin masu adawa da gwamnati da dakarun gwamnatin kasar ba. Saɓanin haka Rasha da Amurka sun dauki matakan rage fitinu a yankin, amma daga lokacin da dakarun gwamnatin Siriya suka soma kai farmaki a yankin Amurka ta ja baya akan yunkurinta na kare rundunar adawa dake yankin, bayanan da aka aika wa madugan adawar Siriya daga ofishin jakadancin Amurka dake Jordan na nuni da cewa duk da yarjejeniya samar da lumana aka yi Amurka da Rasha na yunkurin kare kansu ne kawai, haka ita ma Rasha kalamanta na nuni da ja baya akan tabbatar da tsaro a yankin.

Kasancewar yadda yankin Dera ya kasance cikin lumana na tsawon lokaci ya sanya al'ummar yankin kasancewa cikin kwanciyar hankali. Amma bayan gwamnatocin Asad, lran da Rasha sun fara kai hare-hare a yankunan waɗansu al'umar yankin tuni sun fara ƙaura. Kimanin mutane dubu 270 suka yi ƙaura daga yankin su. Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewar daga cikin waɗanda suka yi ƙaura akwai dubu 40 da suka isa iyakokin Jordan. Duk irin gudummawar da Jordan za ta baiwa Siriyawa dubu 650 dake ƙasarta kasancewar kofofinta da suka yi iyaka da Siriya na rufe ya sanya siriyawan cikin halin ni ƴasun da MDD tuni ta nemi ƙasar Jordan da ta buɗe iyakokinta.  

Hare-haren da dakarun kasashen Rasha, lran da Siriya suka kaddamar a yankin Dera ya haifar da ba hamuta iska tsakanin su da madugan dake adawa da gwamnatin Siriya, a daidai lokacin da dakarun Siriya ke ƙoƙarin kwace ikon yankin Lacat da yawan masu adawa da gwamnatin Asad sun aminta akan samar da lumana karkashin jagorancin Rasha inda suka sallamawa gwamnatin ƙasar yankunan Dael, Bosra al Sham da lbta. Kasancewar yadda Rasha ke ƙara ƙwarin gwiwa wajen kai hare-hare ta sama da kuma yadda Amurka ta ja baya daga tallafawa ƴan adawar gwamnatin Asad na sanya raguwar kaifin adawa a yankin.

Ɗaya daga cikin lamurkan dake ƙara dagula al'amurra a kudancin Siriya shi ne katsalandar ɗin lsra'ila. Kasancewar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a yankin da kuma yadda lran da kungiyoyin dake goyon bayan ta ke ƙalubalantar harkokin lsra'ila a yankin sun ƙara sanya dagule matsalolin tsaro da ake fama dasu a yau da kullum.

Wannan sharhin mal Yazar Can ACUN ne daga cibiyar nazarin Siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin Turkiyya.

Sinyal

 

 Labarai masu alaka