15 ga Yuli: Yunkurin mutum-mutumai masu zubar da jini

Sharhin Farfesa Kudret BÜLBÜL shugaban tsangayar ilimin siyasa ta jami'ar Yildirim Beyazıt da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

15 ga Yuli: Yunkurin mutum-mutumai masu zubar da jini

Matsalolin Kasashen Duniya: 28

Wadanda ke rayuwa a ketare, mutum-mutumin da suka gagari kowa, mutanen da aka dasa wa kwayoyin cutar bairus, ko kuma kasancewa barazanar da ta fito daga darikoki masu muguwar manufa ta musamman da kuma gaggarumar mujadalar  kauda wannan  barazanar, abu ne da yake yiwuwa a fina-finai ne kadai aka taba ganin sa.

A ranar 15 ga watan Yulin shekarar 2016, shigen irin wannan lamarin ne ya afku a Turkiyya.Mambobin wata muguwar darika, masu fuskar jinjirai marasa zunubi,wadanda ke sauya kama don zama dodanni a duk lokacin da aka basu umarni,sun yi shigar burtu tare boyewa a madafan ikon Turkiyya,inda a suka yi yunkurin juyin mulki.

Shin ko me faru a wannan daren ?

A ranar 15 ga watan Yuli,mambobin kungiyar ta'adda ta FETÖ wadanda ke rike da manyan mukamai a ma'aikatun gwamnatin Turkiyya, wadanda a ciki har da ma'aikatar tsaro sun yi yunkurin yin juyin mulki kan umarnin da suka samu daga malalacin shugaban addininsu wai shi Fetullah Gülen, wanda ke rayuwa a Amurka.Tare da tallafin wasu da ke cikin Turkiyya sun karbe iko da wasu ma'aikatu da kuma kafofin kasar Turkiyya,a ciki har da TRT,CNN, da kuma wasu tashoshi Talabiji da Rediyoyin kasar.Sun yi hadarin bama-bamai kan babbar majalisar dokokin kasar Turkiyya, wacce ko a lokacin yaki ba ataba kai ma ta hari ba.Haka zalika, a matsayinsu na mutum-mutumin da ba su da ta-cewa sai na shugabansu, sun bude wa milyoyin mutanen da suka mamaye titunan kasar don nuna kin amincewarsu da wannan yunkurin na juyin mulki.Sun yi luguden wuta kan fararen hula da ma'aikatun kasar.Turkawa sun haye tankokinsu na yaki,sun kwanta a gaban su don kalubalantar su.Sakamakon kuma shi ne: A cikin sa'o'i kalilan, an samu daruruwan shahidai da dubunnan raunannu.

Darasi demokradiyya ga duk duniyya

A kan kira na Shugaba Recep Tayyip Erdogan, gwagwarmayar da mutanen Turkiyya suka yi don kare mulkin demokradiyya da kuma makomarta, ta kasance jarumtakatar da ko a fina-finai da wuya a gan irin ta.Miliyoyin mutane sun mamaye tituna a duk fadin kasar Turkiyya.Fararen hula sun kewaye ma'aikatun gwamnati da sansanonin soji.Duk da ruwan harsasan da sojojin Feto ke ci gaba da yi musu, babu wanda ya ja da baya,a wannan daren, ni ma kaina, na kasance a sahun wadannan mutanen.Daga cikin makusatana, abokaina, aminaina da kuma mutanen da na sani kud-da-kud,da yawa sun fito dafifi don nuna kin yardarsu da yunkurin kwace diyaucin mutane da karfi da yaji da malalatan mambobin haramtacciyar kungiyar, bayi kana makasa suka so yi.

A da can baya ma, Turkiyya ta sha fama da juye-juyen mulki.Amma a karo na farko kenan da ta taba yin karo da irin mummunan wannan juyin mulki wanda ya shafi rayuwar al'umarta kai tsaye.A tsawon makwanni,milyoyi mutane masu ra'ayi mabambanta sun zama tsintsiya madaurinki daya don ci gaba da mamaye titunan kasar.A tsawon makwanni da dama, milyoyin jama'a sun kasance a kan wadannan titunan, ba tare da  wata matsala ta kunno kai ba, ba tare da an zalunci ko da shinnake ba.Shin ko ta yaya talakawan Turkiyya, fararen hula suka bai wa duniya babban darasi kan yadda "Suka dakile yunkurin juyin mulki mafi muni a tarihin kasarsu, cikin ruwan sanyi da lumana ta hanyar amfani da Demokradiyya ?"

A wajejen shekarar 1990, a kafar yada labarai ta Tiananmen,wani jarumin matashin kasar China ya tsaya gaban tankokokin yakin kasarsa.Da yake babu wanda ya juya kwakwalwar sojojin na Sin, sai suka ja da baya.Duniya ta yaba kuma ta shaida wannan jarumtakar.Amma a Turkiyya, da yake mambobin kungiyar ta'adda ta FETO ba su da imani, sai suka dinka take mutane don bi kansu da tankokin yaki.Wannan gwarzantakar da ta fito daga illahirin al'umar Turkiyya, kusan babu wata kafar yada labarai ta duniya da ta gan ta.Duk da cewa,kasashen duniya sun rufe idanusu game da wannan tarihi,kare mutunci da diyauci da kuma gaggarumar tsayayya,dukannin wadanda suka shaida wannan lamarin ba za su taba mantawa da shi ba.

Shin mece ce Fetö?

Abun bakin ciki ne ganin yadda kawo yanzu kasashen duniya ba su fahimci ainahin ko mece ce FETÖ ba.Mambobin Fetö( Kungiyar ta 'adda ta 'yan Fetüllah) na da alaka mai karfi da masihu, maceci kana shugabansu malalacin malamin addini, wanda tare tallafinsa suka dukufa kan manaufarsu ta kafa wata duniya ta daban.Kungiyarsu na da'awar ceton duniya. Shi yasa suke da limamai a dukannin unguwanni, yankuna da kuma birane. Suna yi wa limaminsu kallon zabebben "Maceci".An yi amanna cewa, shugabansu Fetullah Gülen ba wai macecin Turkiyya kadai ba ne,an aiko shi dan ya ceci duniya ga baki dayanta.Shi yasa kungiyar ta'adda ta Fetö ta zama gama-gari tare da tanadar rassa a duk fadin duniya.

Don su kasance kan wannan turbar a kulli yaumin,mabobin Feto NA samun horon na musamman wanda ke da huwan gaske.A tsawon wannan lokacin ana nesanta su ne daga jama'a.Suna kasancewa a wasu wurare na musamman wadanda sai su-ya-su suka haduwa,don gudanar da ibadojinsu duba da abinda suka bai wa gaskiya ,gaba daya suna kasancewa a wata duniya ta daban.A wannan zamanin ne,ake nisanta su daga wasu ka'idojin zamantakewa, na muhallai, daga addinin Islama wadanda mutanen kasar Turkiyya suka share karnoni da dama suna rayuwa a cikinsa.Da yake kungiyar wacce ta samu kafuwa tun a wajejen shekarar 1970,ba ta da wanni tsayayye tarihi da kuma inagantacciyar al'ada,doka da manufa ta gari, sai mambobinta ba su tanadi komai face  gurbatacciyar akida marar tushe.Uwayen da 'ya 'yansu ke karatu a makarantu FETÖ, sun yi taka tsantsan,amma hakan bata tsinana musu komai ba, saboda sannu a hankali aka dinka nesanta hankalin yaransu daga gare su.

Bayan an kammala sarrafa kwakwalensu,mambobin na FETÖ sun kasance mutanen da ke tsammanin cewa, su zababbu ne don gudanar wani boyayyen aikin sirri na musanmman a cikin jama'a.Wai suna da "Tsarkakkun" manufofin da suka gaba.Shi yasa, don cimma wannan manufar tasu ba zasu taba fallasa umarni da aka ba su ba, ko da dan kankane ne, za su dinka boye shi ko yaya zata kaya.Don cim ma manufar da suka gaba da kuma kasancewa a boye, kowace hanya halatacciya ce a gare su.Saboda sun rigaye sun halatta komai idan dai hakarsu za ta cimma ruwa.Abinda suka yi imani da shi da kuma wanda suka sani, shi ne "Tsarkakke" a gare su.Shi yasa za a iya kacibus da su a kowane irin addini ko kuma kowacce akida.Tunaninsu ya yi hannun riga da fadar Maulava Jaludden Rumi wanda ya ce, "Ko ka gabatar da kanka kamar yadda ka kasance, ko kuma ka kasance kamar yadda ka gabatar da kanka".Domin su dai ba zasu taba nuna ainahin fuskarsu ba.Da yake kuma aniyarsu daban take, ba za su taba kasancewa kamar yadda suka gabatar da kansu ba".

Zamu ci gaba a mako mai zuwa.Labarai masu alaka