Kungiyar FETO Mai Gwagwarmayar Mamaya da Afkawa Duniya

Za mu gabatar muku da sharhin Farfesa Kudret Bülbül na tsangayar ilimin siyasa na jami'ar Yıldırım Beyazit na Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.

Kungiyar FETO Mai Gwagwarmayar Mamaya da Afkawa Duniya

Matsalolin Kasashen Duniya: 29

A shirin da ya gabata mun ba ku bayanai kan ainahin ma'anar FETÖ da kuma yadda aka nesanta mambobinta daga iyalansu don ba su horo na musamman  wanda ya yi hannun  riga da zamantekwar al'uma da kuma ka'idojin Islama,wadanda kusan kowa ya yarda da su.Bayan sun bi ta wannan hanyar mai shimfide da wahalhalu marasa adadi,mambobin haramtacciyar kungiyar na makancewa wajen bin duk wani umarni da aka ba su.

Yadda FETÖ ke kafa kungiyarta.

Bayan ta wanke kwakwalensu da boyayyiya kana "tsarkakkiyar" manufa, Fetö na aika mabobinta  kasashen ketare da zummar yada bakar akidarta.Aiyukan da suke yi a wadannan kasashen sun yi kama da wadanda suka gudanar a shekarun farko da suka samu kafuwa a Turkiyya.Da farin farko za a gina makarantu da kungiyoyin farar hula, don badda kama da kuma nuna wa jama'a cewa basu wata muguwar manufa,wanda ta wannan hanyar ce zasu samu damar shuka tsirran ta'addancinsu.Wannan matakin na Farko na kunshe da maunfofi guda 2.Daukar sabbin mambobi a kasashen da suka yi kaka-gida da kuma tabbatar da kasancewar wadannan mutanen a muhimman mukaman kasashensu.Abinda zai ba su damar mulkar wadannan kasashen ta bayan fage.Ga wadanda suka yi nazari da kyau, za su gane cewa, dukannin yaran da suka yi karatu a makarantun Fetö,na cibiyoyin leken asiri,ma'aikatun soja da na tsaro,ma'aikatar firaminista,fadar shugaban kasa,manyan bankuna da dai sauran su. Ga wadanda ba su san dabarun FETÖ ba,ba za su gane cewa za a iya samun mambobinta a ko ina, a kowace ma'aikata ko kuma kasa, a fagen masu sassaucin ra'ayi da kuma masu akidar gurguzu,kirista da kuma zandikai.A yawancin lokutan da suka gane kuma, tuni reshe ya juye da mujiya.

Shin FETÖ barazana ce ga Turkiyya kawai ?

Daga bangaren akidar "Limancin shugabanninsu" har ya zuwa kokarin kafa kungiya da ta ke ci gaba da yi a illahirin kasashen duniya, komai na nuna cewa, FETÖ ba barazana ce ga Turkiyya kawai ba.Ana sanar da cewa akwai kungiyoyin FETÖ a sama da kasashe 170.Amma babu wanda ya san a takaimaime a kasashe nawa ne suka kasance cikakkiyar kungiya.Yawancin wadannan kasashen ba Musulmai ba ne.Da yake Turkiyya ta rigaye ta gano boyayyar aniyarta  kana ta dauki matakan kare kanta, wannan muguwar kungiyar za ta ci gaba da kasancewa babbar barazana ce ga kasashen da ba su gano ainahin fuskarta ba kawai.A wasu kasashen, Fetö na ci gabatar da kanta a matsayin kungiyar farar hula tare daukar sabbin mambobi,inda suke cusa musu dukannin bakaken akidojinsu da kuma gina wasu makarantun boko.Darasin da Turkiyya ta dauka ta hanyar zubda jini da saudakar da rayuka masu dumbin yawa,babban misali ne ga wadanda ba su kaunar su biyar diyyar da ta zarce ta Turkiyya.

Shin barazanar FETÖ ta gushe ?

A 'yan shekarun da suka gabata, abinda matukar wuya a ce mun wayi gari a yau.Abinda da matukar yuwa,ganin yadda daular barazanar FETÖ ke da fadi, abinda da matukar wuya a ce mutane su yi tsokaci kan irin wahalhalun da suka sha, fallasa sirrukan Fetö da kuma yin bayani kan wulakancin da suka gani a hannun haramtacciyar kungiyar.Da farin farko, kamata ya yi mu gode wa Allah kan dukannin wadannan ni'momin.Mafi girman kaso na karfi FETÖ ya samo asali ne daga kyaukyawar aniyar mutane.Yawancin jama'a na kallo fuskokin 'yan FEtö ne don tallafa musu da dukiyoyinsu.Amma daga yau, sun san da cewa kungiyar na da boyayyar manufa, tana gabatar da kanta a matsayin mai kyaukyawar akida,tana yin kulle-kulle,kisa da kuma samun kanta a kowace irin manakisa.Babbar nasarar Turkiyya da ma duniya ga baki daya, ita ce biya gaggarumar diyya don wayar da kan jama'a.Daga karshe, muna iya cewa 'yan Fetö sun kasance, mutum-mutumai ne masu kyaukyawar aniya a zahiri,bakar manufa a badini,masu fuskokin jinjirai marasa zunubi,wadanda tuni aka gano ubangidansu.

Namijin kokarin da Turkiyya da al'umarta suka yi don cimma wannan matsayar, yasa kasashe da dama rugurguje gimshikan kafa wannan kungiyar.Saboda wayar da kan al'uma da kuma ruhsewar gimshikanta, a yanzu haka zai wuya kungiyar ta kafa wani sabon tsari ta hanyar yin juyin mulki.Duk da wannan nasarar, Fetö na iya yin babbar barna da kauda duk wani wanda ya gitta gabanta.Mambobin Fetö wadanda kowanne daga cikin su ya kasance mutum-mutum marar imani kana bam,na ci gaba da wadaka a kasashen duniya, yayin da masarrafin wadannan bama-bamai kuma ke a hannun shugabansu da ke birnin Pensilvania  na Amurka.Kamar yadda ta kashe jakadan Rasha a Turkiyya, don hadassa  yaki tsakanin kasashen 2, kawo yanzu FETÖ na da karfin daukar rayukan mutane a sauwake.Wannan barazanar ba a Turkiyya kadai ta ke ba, tana ci gaba da kasancewa a dukannin kasashen da mambobinta ke gudanar da aiyukansu.A kasashe da dama,'ya 'yanta na boye a muhimman madafan aiki, tamkar bamai-baman da ke jiran lokacin fashewarsu.Amma da ya ke sun boye manufofinsu da kuma ainahinsu salsalarsu,sun kasance mutum-mutumai makasa masu zirga-zirga tsakanin mu.Bugu da kari suna dauke da gubar da a yanzu haka,akwai daruruwan dubban mutane wadanda suka dandana daga gare ta.

Ko da dukannin kwararru a fannin ilimin halayyar bil adama da na zamantakewar dan adam suka hada kai don sake halin wadannan mutum-mutumai masu kama da mutane, wadanda akalar shugabancinsu na hannun malalacin limaminsu da ke Amurka,babu abinda za su iya.Saboda tuni sun yi nisa, ba sa jin kira.suna iya aiki a ko ina, a kowace ma'aikata, a kowane hali da kuma kowa.suna da daurin gindi da tallafi kungiyoyin leken asirin kasashen da dama.Shi yasa za a ci gaba da kiran mambobin FETÖ, mutum-mutumai makasa.Idan muka kalli tarihin wannan kungiyar, sai mu gane cewa ba su taba kulla wata alakar dindindin da kowace kasa ba,saboda suna da manufar da suka kuduri aniyar cimmawa.kungiyar wacce kawo yanzu ta kasance tana yin amfani da dukannin wadannan mamboyin a matsayin bayi, wata babbar barazana ce ga mambobinta ga kuma wadanda ke zaton cewa suna amfani da ita don cimma burinsu.Fetö kungiya ce ta mutum-mutuman da ke ha'intar kasashensu, iyalansu.Cewa mambobin Fetö za su zama masu rikon amana ga kungiyoyin leken asirin da suke ciki, ko kuma kasashen da suka samu kansu a ciki, abu ne mai ban tsoro.

Ko da bai yi komai, dole ne duniya da Turkiyya sun jinjina wa shugaba Recep Tayyip Erdoğan kan yadda ya sadaukar da rayuwarsa da ta iyalinsa don waye wa mutanen duniya da na kasarsa kai kan wannan bakar kungiyar.
 Labarai masu alaka