Da ina samun nasara Bajamushe ne ni, da ba na samu dan gudun hijira

Sharhin Can ACUN daga cibiyar nazarin siyasa da tattalin arziki SETA.

Da ina samun nasara Bajamushe ne ni, da ba na samu dan gudun hijira

A zamanin yau, wariyar launin fata da ƙyamar lslama na ci gaba da ƙaruwa a nahiyar Turai. A ƴan kwanakin nan  jam'iyyar Socialist National ta ƙasar Jamus ta kasance tattare da waɗannan ɗabi’un da suka yi wa Tarayyar Nahiyar Turai katutu. Baƙadala akan kwararren ɗan kwallon Jamus mai suna Mesut Özil da lamurkan da suka sanya shi ficewa daga kungiyar kwallon ƙafar ƙasar na tabbatar da irin yadda ƙyamar lslama, ƙabilanci da wariyar launin fata ke daɗa ƙamari a Nahiyar.

Ɗaukar hoton da Mesut Özil ya yi tare da shugaba Recep Tayyip Erdoğan a yayinda yake ziyara a Birtaniya gabanin ƙaddamar da gasar cin kofin kwallon duniya, ya haifar da ka-ce-na-ce da cin zarafi daga manema labarai da ƴan siyasar ƙasar Jamus. Mesut Özil tun kafin ma ya dauki hoto da shugaba Erdoğan ya fuskanci ƙalubalolin nuna ƙabilanci tun shekarar 2010. Mesut Özil wanda a halin yanzu ke fuskantar wariyar launin fata da nuna banbanci ya tsayu tsayin daka akan muhimmancin hoton da ya dauka da shugaba Erdoğan ya kuma jajirce akan sahihancin Lamarin inda ya ƙi baiwa shugaban kungiyar kwallon kafar ƙasar Jamus Reinad Grindel hanƙuri kamar yadda ya nema.

Kafafen yaɗa labaran kasar Jamus da kuma shugaban kungiyar kwallon kafar ƙasar Reinhard Grindel sun dinga ɗora laifin rashin nasarar ƙasar Jamus a wasan cin kofin duniya akan Mesut Özil ba gaira ba sabar. Tun kafin ma ɗaukar hoton da Mesut Özil ya yi da shugaba Recep Tayyip Erdoğan hotunan da ya yaɗa yayinda yake umura a ƙasa mai tsarki ya sanya shi fuskantar wariyar launin fata da cin mutunci daga ƙasar Jamus.

A yayinda da Mesut Özil ya bayyana ra'ayinsa akan ƙalubalantar da yake fuskanta; ya rubuta wata sanarwa da ya yaɗa a shafinsa ta twitter inda ya bayyana ƙarara irin nuna banbanci, wariyar launin fata, ƙabilanci da ƙyamar lslama dake faruwa a Jamus. A jawabin na shi ya bayyana cewar: “ldan nayi nasara ni bajamuse ne; in kuma na rasa na zama baƙon haure” a yawabin ya bayyana kansa tamkar Muhammad Ali a gidan kwallon kafa. Ƙalubalantar baƙadalar nuna banbanci a ƙasar Jamus da Mesut Özil ya yi, ba wai daga gareshi kawai ba, ya zama martani ma daga Turkawa da Musulmin ƙasar Jamus marasa rinjaye.

 Manifeston da Mesut Özil ya fitar, ƙarara, ya ja hankali akan ƙabilancin da ya yi katutu a ƙasar Jamus, haka kuma ya bayyana asalinsa na Turkiyya da kuma yadda Jamus take a gareshi. Mesut Özil ya aiyanar da yadda hoton da ya dauka da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya sanya shi fuskantar ƙalubaloli iri daban-daban duk da bayanan da ya yi akan lamarin. Ƴan kasar; ƴan asalin Turkiyya sun bayyana Mesut Özil a matsayin jarumi sanadiyar kare asalinsa da mutuncinsa da ya yi duk da ƙalubalolin da ya fuskanta.

Abin kuma dubawa, a gefe guda kuwa, duk da bayanan da Mesut Özil ya fitar ya sosa wa Turkawa da Musulmin Jamus inda ke musu ƙaiƙayi, musulmai da Turkawan dake cikin majalisar Jamus sun kasance ko oho akan lamarin. A dai-dai lokacin da ƙyamar lslama da wariyar launin fata ke daɗa ƙaruwa a Jamus, ƴan siyasar kasar musulmi na yin ko in kula akan ɓatancin.

A halin yanzu, akwai bukatar Turkiyya ta dauki kwararan matakan siyasa a ƙasar Jamus domin kare mutuncin musulmi da Turkawan dake ƙasar. Matakan da Turkiyya za ta dauka ka iya ƙara wa musulmi da Turkawan kasar ƙwarin gwiwar ƙalubalantar ƙalubalolin da suke fuskanta a ƙasar. Hakan zai sanya a samu ɗaruruwan Mesut Özil a ƙasar. ldan Turkiyya ta yi shiru akan lamarin, toh ko shakka babu saɓanin hakan ka iya faruwa.Labarai masu alaka