HGK-1: Jirgin sama marar matuki mai hangen nesa na farko na Turkiyya

Muna gabatar muku da sharhin Tarkan Zengin, shugaban horo na kungiyar kwadago ta masana’antar kera makaman yaki ta Turkiyya.

HGK-1: Jirgin sama marar matuki mai hangen nesa na farko na Turkiyya

A wasu lokuta da suka gabata,yayin da ta ke kokarin tabbatar da tsaron kasarta da kuma gwagwarmayar kau da kungiyoyin ta’adda, Turkiyya ta sha cin karo da takunkumai kan  makamai da kayan yaki,daga kasashe abokan ittifakinta.Tana fama da matsaloli da dama ko a wajen amfani da makaman da ta saya da kudinta.Amma a kulli yaumin, Turkiyya ta yi nasarar amfani da wannan kalubalen tamkar wata dama ta cim ma manufofin da ta sa gaba da kuma magance dukannin wasu  matsalolin da ta fuskanta.A hakikannin gaskiya, abokan ittifakin Turkiyya na shakun sayar ma ta da jiragen sama marasa matuka.Shi yasa ta fara kera wadannan na’urorin da karan kanta.Saboda wadanda ta ke ganin cewa abokanta ne, basa son sayar ma ta da jiragen kunar bakin wake marasa matuka.Bayan kera makaman da ta ke bukata, Turkiyya ta fara sayar da su ga sauran kasashen duniya.A lokacin da “Abokanta na ittifaki” suka fara hana ruwa gud game da batun sayen jiragen sama marasa matuka masu hangen nesa wadanda ake yi lodawa bama-bamai,sai Turkiyya ta fara kera su.

Wannan matakin da Turkiyya ta dauka na da matukar muhimmanci, musamman ma wajen ‘yantar da kanta daga sayen makaman daga kasashen ketare.Alal misali,Amurka na da ‘yancin sa ido kan makaman da ta sayar wa Turkiyya,cikakken masaniya kan makaman da aka siya, aka yi amfani da su da kuma wadanda suka yi saura.Abin fahimta a nan shi ne, a yunkurin gwagwarmaya da kungiyoyin ta’adda da Turkiyya ke yi, Amurka na da cikakkiyar damar hana ruwa gudu a duk lokacin da ta ke so.An yi wani zamani, wanda Amurka ta ki sayar wa Turkiyya, irin wadannan na’aurorin yaki masu sarrafa kansu, don hana ta amfani da su kan ‘yan kungiyar ta’addar  PKK da ta PYD.Shi yasa, Turkiyya ta yanke shawarar kera makaman da ta ke bukata da karan kanta.

Shin ko yaya aka hana kera jiragen sama marasa matuka masu hangen nesa ?

Wasu kasashe sun yi ta kai ruwa rana don ganin sun samar da tsare-tsare marasa adadi wajen hana Turkiyya kafa kamfanonin kera makamai.Wasu kuma,don cimma manufarsa sun yanke shawarar kin sayar wa Turkiyya da makamai,haifar ma ta da kalubale game da irin amfani da za ta yi da su,ko kuma sayar ma ta da makamai a farashi mai rahusa. A duk lolacin da Turkiyya ta fara kera makaman da ta ke bukata da karan kanta, sai kasashen Yamma su fara sayar da nasun a farashi mai saukin gaske, don dagula lissafinta.Hana kera jiragen sama marasa matuka masu hangen nesa (HGK), na daga cikin manufofin da wadannan kasshen suka sa gaba.

Sojojin sama na Turkiyya sun daura damarar fara aiyukan ‘yantar da kansu daga sayen makaman kasashen Yamma a farkon shekarar 2005.Abinda yasa shugabannin lokacin suka bada umarnin fara kera wadannan makaman masu sarrafa kansu.Bayan wani matsakaicin zamani,a shekarar 2006,harkarsu ta cimma ruwa,inda suka  kera jirgin sama marar matuki mai hangen nesa (HGK) na farko.Kamar a zamaninnikan da suka gaba,”Abokan ittifakin” Turkiyya sun hade ma ta kai don hana ta cimma manufarta.

A da, Turkiyya na sayen kowane JDAM daya ,wanda daya ne daga cikin muhimman sassan jiragen sama marasa matukan da ta ke bukata a dalar Amurka dubu 120,000.A shekarar 2006, a lokacin da ta fara kera nata makaman, sai farashin kowane HGK ya haura dalar Amurka dubu 90,000,wannan farashin ya kara faduwa a lokacin ta fara kera su barkatai don sayar da su,inda sashen da a baya, Amurka ta yi zaman sayar da shi a dala dubu 120,000 ya tashi a dalar Amurka dubu 20,000.Abu ne mai matukar jan hankali, ganin yadda farashin wannan sashen ya fadi warwas a cikin kankanin lokaci, duk da cewa babu wani sauyin da aka samu a yawan kudaden aka kashe wajen samar da su.Daya daga cikin manufofin da Amurka ta sa gaba a wannan harkar ita ce, hana Turkiyya kera makaman da ta ke bukata.Nufin Amurka, shi ne karya farashin makamanta don kashe ninka yawan kudaden da Turkiyya za ta kashe wajen kera nata sau 4.5,wanda hakan zai yi matukar tsawaita wa’adin kera makaman Turkiyya.Amma duk da hakan,da yake ya zama tilas a gare ta ta kera makamai, cikin kiftawar ido,Turkiyya ta yi nasarar kaddamar da aiyukan kera makaman.

Turkiyya ta fara samar da samfuran makamai

An samar da jiragen sama marasa matuka masu hangen nesa, bayan da injiniyoyin Cibiyar Masana’antar Nazari da Bunkasa Dabarun Yaki (SAGE) ta Babbar Hukumar Binciken Fasaha da Kimiyya ta Turkiyya, (TÜBİTAK) suka yi namijin kokari tsawon shekaru 5. Ba dare ba rana.Jirgi na farko samfurin HGK-1 wanda sojojin saman Turkiyya suka samar, an kera shi ne a cibiyar kula lafiyar da jiragen sama na 3 da ke helkwatarsu.Manyan sojoji da sauran ma’aikatan wannan babbar ma’aikatar ta soja ta fara gudanar da aiyukanta a farkon shekarar 2013.A wani zaman da kwamitin tsara kasafin kudi na Babbar Majalisar Dokokin kasar Turkiyya ta yi a watannin da suka shude, ministan fasaha, kimiyya da na masana’antu,Faruk Özlü, ya yi albishir cewa, Turkiyya ta fara samar da sassan samfuran jiragen sama marasa matuka masu hangen nesa na HGK-1.A  baya, Amurka, Rasha da Isra’ila ne kawai suke kera wadannan muhimman makaman.Amma a yanzu, Turkiyya ta cim ma matsayar kasa ta hudu wacce ke kera su,inda ta yi amfani da jiragen HGK-1 a farmakan tabbatar tsaro na Firat, Reshen Zeytin da kuma a yake-yakenta na kawar da kungiyoyin ta’adda.

A cewar bayanan da wadanda ke kera wadannan jiragen suka bayar: “Yayin da sauran jiragen sama na yaki ke harbe bama-bamai a tazarar kilomita 5 zuwa 6, HGK na kai farmaki daga tazarar kilomita 25.Tare da karin fika-fikanta da kuma kirarta ta musamman, bama-baman da ta ke dauke su, na rage nauyi a sararin samaniya.Jirgin na gama aikinsa kafin ma ya iso inda barazanar ta ke.Tare da tallafin taurarun dan adam da magadisan da wadannan makaman wadanda aka kera ta yadda za a iya tsarkafe su kan sauran jirage marasa hangen nesa suka tanada, jiragen na tarwatsa duk wata barazanar da ta kasance a kusurwa mai fadinta mita 6”.Wadannan jiragen saman wadanda aka kera ta hanyar kashe kudade kalilan na ci gaba da jan hankalun kasashe da dama,wadanda suka hada da na yankin Gabas ta Tsakiya, Arewacin Afirka da Asiya.Labarai masu alaka