Rufaffiyar Turai da Budaddiyar Duniya

Zamu gabatar muku da sharhin farfesa Küdret Bülbül Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami'ar Yıldırım Beyazit da ke Ankara, Babban Birnin Kasar Turkiyya.

Rufaffiyar Turai da Budaddiyar Duniya

Matsalolin Kasashen Duniya: 38

A wajejen shekarar ne na fara nuna kwankwanto game da akidar “Duniya a Tafin Hannu”, wato Globalization a Turance, a matsayin na matashin kwararre a fannin kimiyya da fasaha. Shin kowane irin tasiri ne wannan akidar ta yi kan Turkiyya, da ma sauran kasashe masu tasowa ? Shin yaya zamu fuskance ta? Shin yaya ya kamata mu kalubalance ta ko kuma mu rungume ta ?

Neman amsoshin dukannin wadannan su’alolin da na yi a baya da ma wasu makamantansu,yasa daga karshe na yi bincike-binciken da suka kai ni ga samun digirina na digirgir, wato PHD a Turance.A hakikannin gaskiya, a tashin farko ra’ayina shi ne samar da akidar “Duniya a Tafin Hannu” wanda ba ta yin katsa landan ga ‘yanci da mutucin bil adama .Za a iya shaida wannan tunanin nawa a sunan littafina mai taken “Wahala da Aminci, Turkiyya a tsaka-tsakiyar akidar duniya a tafin hannu”,wanda gidan buga litattafai na Küre ya wallafa.Globaliation,ba akida ba ce ba “gaba daya”, mai “Gaba dubu” ce, mai alakar wariya da kadaici ba ce, zaman cude-ni-in-cude-ka ne ko mu ce alaka ce ta ba ni manda in ba ka gishiri.Tare da wahalhalu,amincewa, da kuma damar da ta ke tattare, akidar na kunshe wasu kankana tsare-tsare,wanda kowane ke dunkule a cikin kowane.

Mahangar “Duniya a Tafin Hannu” a Jiya

Lokacin da fara aikace-aikacena, Yammacin duniya na ta safa da marwar yin tinkaho da wannan akidar.Tana ci gaba da da’awar cewa ta rastsa iko da iyakokin siyasar yankinta, zirga-zirga jama’a da na kayayyakinsu.Aiki tare, hade kai da kuma kin karbar harajoji, na a jerin ababen da ta yi matukar dasa aya a kansu.Tana kokarin samar da wata duniya,wacce babu batu kare hakkin mallakar fasaha,budaddiyar duniya wanda kowa za iya cin karansa babu babbaka.Amma a dai a wannan zamanin,akwai kasashe da dama da ke ci gaba da daga muryoyinsu don nuna rashin amincewarsu, musamman ma wadanda basu ci gaba ba a fannin tattalin arziki da kuma masu tasowa,inda suka ce “Duniya a Tafin Hannu” akida ce da kasashen Yamma masu cigaba a fannin tattalin arziki suka samar don cim ma manufofinsu.Yin kasuwancin kasa da kasa ba tare a karbi ko kwandala a matsayin haraji,bude kofofin kasuwannin duniya,kin kare hakkin mallakar fasaha, fadada aiyukan hadaka da kuma bai kasashen damar gindaya ka’idojinsu san ransu, abu ne da ba zai amfani kowa ba, face yammacin duniya.Siyasoshin da wannan akidar ta zo da su za su gurgunta cigabansu da kuma ruguza tattalin arzikinsu ta yadda ba zasu taba iya karawa da sauran takwarorinsu na duniya a harkokin cinikayya.Haka zalika, sun yi wa “Duniya a Tafin Hannu”  kallon, wani sabon salo na akidar jari hujja wacce aka samar da nufin kara bunkasa manufofin mulkin mallaka tare da durkusar da ‘yantattun kasashe.Yawancin masu sukar lamiri ba hangen nesa ba waiwaye ne suka yi.Halin da suka nuna, bukata ce ta kare kai.An yi tuya an manta albasa, saboda ayar tambayar da ya kamata a ce an dasa, amma kuma aka yi kasa a gwiwa ita ce, shin idan “Duniya a Tafin Hannu” sabon salo ne na akidar jari hujja, to mene matsayinta game da tsohon salonta,wacce ke da’awar kare Al’uma da kuma ‘yancin cin gashin kan kasashe.

Abinda da ya wakana

A jajibirin shekarar 2020, bayan shekaru 30 sun shude, zamu iya la’kari da tabbatuwar wadannan tunace-tunace da fargabar da aka dinka yi a 1990,a sauwake.A matakin da muka cimmawa a yau, Yammcin Duniya ba bugun gaba da akidar “Duniya a Tafin Hannu”.Saboda babu wata ribar a zo a gani da suka samu.Sakamakon rashin wadatuwa da wannan akidar, kasashen Yamma,wadanda a sahun farko har da Amurka,na ci gaba da kare da ra’ayoyin da kasashe masu tasowa suka gabatar a shekarar 1990 don yakar akidar “Duniya a Tafin Hannu”.Babu kasa daya tak da ke ambatar dage iyakokin siyasa tsakanin kasashe, zirga-zigar mutane da na hajojinsu, kin kare hakkin mallakar fasaha,bunkasa cinikayyar kasa da kasa ba tare an karbi ko anini ba, bai wa kamfanoni damar kafa ka’idoji kasuwanci kamar yadda suka ga dama.Sake dawo da hannayenta da ke ketare,gida da kuma ci gaba da karbar milyoyin daloli na harojoji daga kusan kowace kasa, na daga cikin ababen da ke kara tabbatar da cewa,tuni Amurla ta yi watsi da wannan akidar.Shin a shekarar 1990, wa zai taba tunanin cewa,wata rana Amurka za ta samar da runduna mai sojoji dubu 10 don hana bakin haure kwarara kasarta? A yau,Amurka da kasashen Yamma na ci gaba da ja da baya don rungumar akidojin kishin kai.Yayin da a daidai wannan lokacin kuma,kasashen da suka ribantu da akidar “Duniya a taffin Hannu”, suka maye gurbin kasashe masu cigaban tattalin arziki a a shekarar 1990.Kasashe kamar su Sin, Indiya,Barazil da kuma Turkiyya sun cim ma gaggarumar nasara ta hanyar amfani da wannan akidar.A yau, ta yi wa kasashen Yamma fintinkau a wajen kare siyasoshin Globalization,inda Turkiyya kuma ta taka rawar a zo a gani a karshen shekarar 2000, saboda ta zama hanja da jini da sauran kasashen duniya.Demokradiyya da kuma ‘yancinta suka bunkasa haika, tattalin arzikinta ya habbaka,kana kasafin kudin kasar wanda a da, ya  dalar Amurka dubu 2000 ne, ya ninka sosai.Yana daga cikin ababen da suka haifar baraka tsakanin Turkiyya da kasashen Yamma,cigaban tattalin arziki, karfin fada a ji da kuma dogaro da kai da kasar take nunawa a kulli,wanda hakan yasa Turai da magoya bayanta suka fara shakkun damawa da ita.

Kamata yayi kwararrunmu su yi watsi da hardarsu

Kawo yanzu akwai wasu kwararru a Turkiyya da ma sauran sassan duniya,wadanda sun kasa hangen yadda karshen akidar “Duniya a tafin Hannu”  zai kasance,da kuma tasirinsa zai yi kan makomar Yammacin duniya da alakar da ke tsakanin ta da sauran kasashe.A shekarar 1990, sun ci gaba da zuba gabatar da ababen da suka haddace.Sun kasa gani ko kuma sun ki su gane wa idanunsu yadda a yau, Yammacin duniya ke ci gaba da fusata,saboda ta kasa fa’idantuwa da Globalization,inda ta ware kanta tare da ja da baya don sake rungumar akidar kishin kai.A yau ba kasashen Yamma ba, wadanda suka ci ribar akidar “Duniya a tafin hannu” ne gwagwarmayar kare tsare-tsare bude iyakokin duniya da kuma mika hannyensu ga kowace kasa.Ko da yake, a hakinannin gaskiya,wasu kasashe masu tasowa sun fi ribantuwa da akidar fiye da wasu.Da yiwuwar akwai kasashen da suka yi asara sosai.Saboda tsare-tsaren wannan akidar, basu dora manufofi ko kuma bukatun kowace kasa a sikeli daya ba.Abin nufi a nan shi ne, inda har komai ba gudana ba kamar yadda aka tsara,babu wata kasa da ke iya hasashen riba zata samu ko kuma asarar da zata yi. Shi yasa,kamata ya yi mu zama masu nazari ba masu suka ba, ba masu yin watsi ba, masu hikima, ba masu hadda ba a makance, mu kasance masu zurfafa bincike.Yawan suka,muguwar guba ga bai yin ta.

“Tufafin yau ba zasu taba bushewa da hasken ranar jiya”.Musamman ma kwararru,manyan ma’aikata,shugabanni,’yan kwadago, da kuma mutane masu cikakken hankali na ketaren Turai,kamata ya yi su sake zurfafa bincike game da ababen da suwakana a shekaru 30 da suka gaba.Ya ci a ce sun gane cewa, a wannan duniyar,inda sani ke mazan tsufa,da wuya a warware bakin zaren matsalar yau ta hanyar amfani da ilimin bara.Yadda tsare-tsare Globalization wadanda suka ci karo da “Fadi,yawan aiki da kuma gaggawa” ke ci gaba da sauyawa a cikin kiftawar ido, ba wai mastalolin gobe ba,ba zasu ishi warware ko na gobe ba.

 Labarai masu alaka