Turkiyya ta yi nasarar ba wa 'yan gudun hijirar Siriya mafaka

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana da juna jim kaɗan bayan kammala taron Sochi.

Turkiyya ta yi nasarar ba wa 'yan gudun hijirar Siriya mafaka

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana da juna jim kaɗan bayan kammala taron Sochi. Shugabanin biyu sun aminta akan tsabtace yankin ldlib daga dukkanin makamai, a ɗayan barayin kuma ma’aikatan harkokin tsaron Rasha ta fitar da sanarwar cewa ba zata kai hari ba a yankunan ldlib.

Wannan matakin tsagaita wutar; ya samu tagomashi ne kasancewar irin kwarjinin da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya nuna akan hakan. Wannan dai wata nasara ce ga ƙasar Turkiyya. A ƴan kwanakin nan rundunar sojan Turkiyya ta dauki matakai kwarara a yankin ldlib inda ta tura makamai iri daban-daban a yankunan lumana 12 da ta kafa a yankin. Turkiyya dai tana mai fadakarwa ga Rasha, lran, gwamnatin Asad da hukumomin shi’a a yankin akan irin matakan da suka dace a ɗauka a yankin, a yayinda Turkiyya ke daukar matakan diflomasiyya domin samar da lumana a kasar, bata kuma bar matakan soja a gefe guda ba. Kasancewar yadda Rasha da lran ke bukatar daukar matakan soja na bai daya a ldlib na nuni da cewa Rasha ta ja baya akan yarjejeniyar Sochi. Ƙungiyoyin da lran ke goyawa baya ma sun kai hare hare a yankunan Cisr Sugur da arewacin Hama.

Turkiyya na daukar muhimman matakai domin dakatar da rigingimun dake ƙasar Siriya da kuma samar da lumana mai dorewa. Bugu da ƙari, Turkiyya na daukar nauyin fiye da ƴan gudun hijira miliyan uku daga kasar Siriya. Sabili da wadannan nasarorin da aka samu ya kamata shugaba Erdoğan ya jinjinawa rundunar soja da hukumar leƙen asirin dake ƙasarsa, domin sun dauki matakan kauda cin zarafin bil adama da dama a kasar Siriya.

Akan yarjejeniyar da aka aiyanar ya zama wajibi ga Turkiyya da Rasha su dauki matakan kauda dukkanin kungiyoyin dake dauke da miyagun makamai daga yankin. Sabili da haka akwai aiki ja akan kasashen biyu, haka kuma a daidai lokacin da ya kamata su jawo hankalin kungiyar Shi'a dake yankin zuwa ga lumana ya kuma kamata su warware matsalolin kungiyoyi kamar su Hayet Tahrir a yankin.

Ya ɗoru akan Turkiyya data yi yunƙurin kauda makamai a fadin yankin a kallan da tsawon kilomita 15-20, haka kuma ya zama wajibi a kanta data jagoranci samar da lumana a yankin baki daya. Haƙiƙa ya ɗoru akan wuyar Turkiyya da Rasha da su ɗauki dukkanin matakan kauda kungiyoyin dake yankin da kuma tsabtace yankunan baki ɗaya daga miyagun makamai musanman a yankunan lumanar da suka kafa.

A yarjejeniyar tsagaita wutar an aminta akan buɗe hanyoyin M4 da M5 domin dawo da hada-hadar kasuwancin Siriya musamman a yankin Lazkiye da Damascus zuwa Halep.

Yarjejeniyar Turkiyya da Rasha nada muhimmanci sosai ga yaƙar ta'addanci da Turkiyya ke yi. Kungiyar ta'addar PKK-YPG sun so su yi amfani da harin da aka yi niyyar kaiwa a ldlib domin mamayar Afrin, a halin yanzu, yarjejeniyar da aka aiyanar wacce ta dakatar da kai hari a ldlib ya kange muguwar manufar yan ta'addar, bugu da kari, Turkiyya zata iya amfani da wannan damar domin ci gaba da fatattakar ƴan ta'addar PKK-YPG dake haifar da jidali a yankin.Labarai masu alaka