Jiragen sama samfurin Hurkus daga Vecihi Hurkus

Muna gabatar muku da sharhin Tarkan Zengin, shugaban bayar da horo na kungiyar kwadago ta masana’antar kera makaman yaki ta Turkiyya.

Jiragen sama samfurin Hurkus daga Vecihi Hurkus

Daga ranar 20 zuwa 23 na watan Satumban da ya gabata,a karo na farko an gudanar da bikin baja kolin fasahar kere-keren jiragen sama “TEKNOFEST İSTANBUL” ,wanda ma’aikatar magajin garin birnin Santambul tare da hadin gwiwar kungiyar bunkasa fasaha ta kasar Turkiyya suka dauki nauyi. A bayanin da shugaban tawagar, kana wakilin  T3, Selçuk Bayraktar a taron gabatar da bikin na bana,ya ce yunkurin habbaka fasa abu ne matukar muhimmanci.Wasanni,baja koli,gasanni,taruka da aika-aikace da aka yi a Santambul,sun nuna hakan.
Çünkü başkalarının kanatlarıyla uçmaya çalışanlar 'Hürkuş' olamazlar." Bugün Türkiye, savunma alanında kendi kanatlarıyla uçmak için inançla geleceğe yürüyor.

A bikin an yi baja kolin jiragen sama samfuran HURKÜŞ, wadanda suka dinka wasanni a sararin samaniya.Yayin da nake kwallon wadannan jiragen sai na tuno da hikayar matukin jirgin saman  Turkiyya Vecihi Hurküş,wanda ya tanadi wani matsayin na musamman a tarihin fasahar samaniya na kasar.Ganin kokarin da matasanmu suka yi a yau wajen daukar hanyar wannan fasihin da ya taka rawar a zo a gani ta hanyar gudanar da ingatattun aiyukan a lokacin kuruciyarsa,na nuni da cewa kasarmu na da kyaukyawar makoma.Tallafin da gwamnati ta bayar wajen bunkasa fasahar Vecihi Hurküş,wata babbar dama ce ga fasihan matasanmu.Daman Vecihi na ambatar wannan lamarin kamar haka :”A kasashen da na ziyarta, ina da cikakken tarihin yadda suka fara aiyukan sufurin sama.Kafin komai,yardar al’uma da aiki tukuru, shi ne hanya daya tilo wajen cimma nasara.Cin gashin kai,halayyarmu nagari da ‘yancin zaben makomarmu, su ne ababen da ba za a taba kwace su daga hannenmu.Ina bukatar wadannan ababen don cimma nasara.Ni Vecihi Hurküş,babbar alfarma ce a gare ni in dinka amfani da wannan sunnan, ganin yadda na bai wa kasata fika-fikai.Na saudakar da yarda da kuma nacina kan cewa cin gashin kan kasata, ’yancina da kuma makomar Turkiyya na da nasaba ne da bunkasa masana’antu”.

An haifi Vecihi Hurküş a shekarar 1896 a birnin Santambul.Gyatuminsa ya bar duniya tun yana da kankani.Bayan kasancewarsa daya daga cikin fitattun sunayen da suka kafa tarihi a Turkiyya, Vecihi ya gaji wata rayuwa mai cike da kunci da Jarumtaka.Ya tanadi nasorori dama a fannin sufurin samaniya.Al misali, a shekarar 1917, yayin da yake aikin sa kai a fagen dagar yankin Kafkasiya,Vecihi ya kasance matukin jirgin sama Baturke na farko wanda ya yi raga-raga da jiragin saman makiya.Haka zalika, shi ne mutum ne farko da fara kera jiragen sama masu dauke da sunansa,kana shi ya fara gina makarantar sufurin samaniya ta farko da kuma horas da mace ta farko wacce ta tuka jirgin sama.Baya ga haka, shi ne mutumin da ya gina kamfanin jiragen sama da kuma makarantar sufurin samaniya ta farar hula ta farko a Turkiyya.Vecihi Hürkuş, shi ne Baturke na farko da ya tuka jiragen yaki da sufurin farar hula samfura daban-daban su 102.Daga shekatrar 1916 zuwa 1967, ya tuka jiragen sama tsawon awanni dubu 30,000.Ya halarci yakin kwato ‘yncin kai na “Kurtuluş” a matsayin dan sa-kai.Dukannin wadannan nasarorinsa suka sa, Babbar Majalisar Dokokin Turkiyya ta karrama shi da lambar yabon “’yancin kai”.

Vecihi Hurküş ya kera jirginsa na farko samfarin K VI, kana ya yi shawagi da shi a shekarar 1925.Ya kera jrigin yayin da yake da shekara 29 a lokacin da yake karmin karfi.Amma a zamanin, maimakon a ba shi lambar yabo, aka yanke masa hukuncin dauri na kwanaki 10,sabili da tayar da jirgin sama da ya yi ba da izini ba da kuma yanke rabin albashinsa.Ya yi tsokaci kan wanna lamarin a shekarar 1954 a sa’ilin da ya wallafa wani rubutu inda ya ce: “Mun taka doka da oda ta hanyar mantanawa da kasncewarmu sojoji.A shekarar 1954 ma,irin wannan lamarin ya faru da shi,sakamakon ya gina kamafanin sufurin sama na farko a Turkiyya mai suna “Hurküş Hava Yolları”.Ya gina wani gareji don gyara jiragen da kamfanin kasar Turkiyya Turkish Airlines ta daina amfani da su.An hana wa jiragensa tashi babu gaira babu dalili,an yi masa zagon,an shirya masa tugu,kana an hana shi ci gaba.

A wani shagon da ya yi haya daga hannun wani mai sayar da itace na yankin Kadıköy, Vecihi ya kera jirgin sama samfarin “Vecihi XIV” a watanni uku kacal.Ya tayar da wannan jirgin a shekarar 1930.Da zummar samun takardar hakkin mallakar fasarar jeragen saman da ya kera, Vecihi ya mika bukatarsaga ma’aikatar cigaban tattalin arzikin kasar Turkiyya. Amma ta hana shi wannan takardar inda ta ce, ta yi hakan ne,“Saboda ta kasa samun kwararren da zai gwada wadannan jiragen saman”.A hakannin gaskiya, wannan amsar da aka bai wa Vecihi,ita ce umma’aba’isar tsayawa cak da aiyyukan kere-kere masana’antun kasar.

ABUN HAWAN SAMA NA FARKO NA TURKİYYA: HURKÜŞ

Huküş ya kasance abun hawan sama na farko da kamafanin aiyuka da kuma sufurin samaniya na Turkiyya,TUSAŞ ta samar.An fara samar da jiragen sama na horo samfarin Hurküş a watan Maris na shekarar 2006,sakamakon wata yarjejeniyar da masana’antun tsaro da  kamafanin TAI suka rattaba wa hannu.An yanke shawar kaddamar da wannan aiki da ummar biyan bukatan ma’aikatar tsaro kasar Turkiyya da kuma sayar da jirage sama na horo a kasuwannin duniya.

A yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a ranar 26 ga watan Satumbar shekarar 2013,aka fara kera jiragen sama samfarin Hurküş da zummar gabatar da su a kasuwannin duniya.A ranar 26 ga watan Disamban shekarar 2013 kuma,aka sa hannu a yarjejeniyar kera jiragen sama samfuran Hurküş-B.Jirgin Hurküş A shi ne abun hawan sama na farko wanda aka samar da lasisinsa duba da ka’idojin EASA da CS-23.An samar da Hurküş-B ta hanyar da amfani dukannin ingattatu kana tabbatun fasahohin da ake da su wajen kera jiragen sama.Hurküş-C kuma,An samar da shi don biyan bukatun da ke nasaba, kaifin hangen nesa, horo,kananan farmakai,leken asiri da kuma amfani da kudaden kalilan.

Ana sa ran za a mika jiragen sama samfuran Hurküş,wadanda aka cimma muhimman nasarori yayin gwaje-gwajen da aka yi musu, ga sojojin saman kasar Turkiyya a watan Nuwamna mai zuwa.Sojojin zasu fara amfani da wadannan ababen hawan, bayan da mika musu jiragen farko,wadanda a tsawon watannin 3 za a zurfafa bincike kan su. Idan a tsawon wannan loakcin,an gano wasu matsaloli game da wadannan ababen hawan, za a dauki matakan da suka dace don kara bunkasa fasaharsu.Za a fara mika wa sojojin kasar Turkiyya jirage 15, har ya zuwa watanni 6 na farko na shekarar 2019.

A cewar bayanan da Hukumar TAI ta bayar game da jiragen, an babbar nasara yayin gwaje-gwajen nagarta da na kwari da aka yi wa jiragen sama,wadanda aka tayar sau biyu.an hada kusan muhimman takardu 545 game da wadannan jiragen saman don aika wa Hukumar sufurin samaniyar tarayyar Turai EASA da kuma Hukumar sufurin samaniya na farar hula SHGM.Bayan dukannin wadannan aiyukan, a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 2016, an yi nasarar mallakar lasirin kera wadannan sabbin samfuran jiragen na Hurküş “TT32” daga Hukumar SHGM.A daidai wannan ranar kuma, aka samu lasisin “TİP” daga hukumar EASA.Hukumomin biyu, sun tabbatar da cewa wannan lasisi za a iya amfani da a dukannin wata kasar Turai.Abinda yasa Hurküş ya zama jirgin saman kasar Turkiyya na Farko wanda ya samu lasisi daga manyan hukumomin Turai.Wadannan ababen hawan na da matukar muhimmanci a Turkiyya.Haka zalika,namijin kokarin Kamfanin Vecihi Hurküş wacce ta kasa cimma manufarta a shekarar 1925,sakamakon shekaru 29 da aka kwashe wajen hana shi tasowa ma,muhiimin abu ne.Labarai masu alaka