"Gidan Adalci"

Sharhin da Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim Beyazit da ke Ankara ya yi mana.

"Gidan Adalci"

Matsalolin Kasashen Duniya: 40

A makon da ya gabata shugabannin duniya sun taru a wajen Taron Kolin Majalisar Dinkin Duniya. Sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar ta nuna adawa da dunkulewar duniya, irin amsar da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya mayar ga Trump na kare hadin kan duniya, Fadin “duniya ta fi kasashe 5 girma” da kira ga adalci da Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi da kuma yadda Firaministar Niyuzelan Bayan Ardern ta je wajen Taron da jinjirinta dan wata 3 ne suka fi jan hanklin duniya game da taron.

A wannan rubutun, ba wai zan mayar da hankali kan abubuwan da Shugabannin suka tabo a taron ba ne, a a zan mayar da tunanina kan kiran da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi na a samar da adalci. Shugaba Erdogan ya tunatar da “Gidan Adalci” wanda al’adar Musulunci da Turkawa ce tun tsawon zamani. Ya ja hankali da irin gibin da ake da shi a duniya game da dalci. Ga abubuwan da Erdogan ya fada “A wayewarmu akwai abunda muke kira Gidan Adalci wato al’uma da ta ke da adalci, ta ke da tsari na doka da gaskiya wajen gudanarwa. Dukkan wadannan abubuwa da ke cikin wannan Gida na Adalci, an yi musu kaca-kaca a wurare da dama a duniyarmu ta yau. A duniyar siyasarmu ta yau, zamantakewa da tattalin arziki, wannan abu ne ya janyo rikice-rikicen da ake samu. Dole mu yi aiki tare don tabbatar da adalci wanda shi ne abun da zai ba mu damar rayuwa tare cikin farin ciki da zaman lafiya. A yau arzikin da mutane 62 da suka fi kowa arziki suke da shi a duniya, sun mallaki abunda rabin al’umar duniya na biliyan 3.6 suke da shi, ka ga kenan akwai matsala a nan. “

Idan ana so a fahimci kiran adalcin da shugaba Erdogan ya yi, to sai an kalli irin tarbiyya da tsarin rayuwa na yammacin duniya. Bayan yakin duniya na biyu, yammacin duniya da ya dinga tutiya game da kare hakkokin dan adam, ‘yanci, daidaito da sauransu, amma a yau sun nisanci duk wadannan abubuwa. A yanzu kusan za a iya fadin cewar nuna wariya ga ‘yan gudun hijira da rashin adalcin da ake yi wa Musulmai a Yammacin duniya ya zama ruwan dare kuma an mayar da shi ba komai ba. Yadda jam’iyyu masu tsaurin ra’ayi suke samun kuri’u, tare da hadin gwiwar kafa gwamnati, ya sa bakaken maganganun da ake fada wa baki ya zama ba komai ba. A wasu kasashen Turai, jam’iyyu suna samun kuri’u da damar kafa gwamnati saboda kalaman nuna kyama ga ‘yan gudun hijira. Kasashen Turai na kafa rundunonin tsaron kan iyaka saboda tsaron masu neman mafaka. A wajensu da ma a ce ‘yan gudun hijira sun zauna sun mutu a kasashensu ko kuma su tafi kasashe irin Turkiyya to da babu wata matsala. A yau muna wata duniya da Yammacinta ya rasa duk wasu darajoji da ake nema.

Idan aka kalli wannan abu ta mahangar Turkiyya, za mu ga cewa adalci ne tushen imaninmu, wayewarmu da tarihinmu. Da fari sai an samu adalci sannan za a samu ‘yanci da daidaito. Tsawon zamanunnuka, an yadda da abinda ya ke rubuce a kotunanmu na ce wa “Adalci shi ne jigon mulki.” Mulki ba wai na dukiya ko kaya ba ne kawai, yana nufin tsari, kasa da dokoki ne. A bukatar adalci da ala’umarmu ke yi ya sanya aka samar da tsarin “Gidan adalci” tare da tabbatar da shi a aikata da hukumance. Gidan Adalci yana fara wa tare da kare wa da tsari mai inganci na siyasa, zamantakewa, harkokin kudi, kasuwanci, tattalin arziki da sauransu.

Idan muka kalli aikin da Yusuf Has Hacib na shekarar 1069 da na Kinalizade Ali Efendi da ya yi a 1564 kan halayya, za mu ga yadda aka yi bayanai game da “Gidan Adalci”. Abin da ake kira “Gidan Adalci sh, ne idan aka ce adalci shine tushen duk wani abu na al’umarmu, sannan kuma idan aka rasa shi to babu mulki ma gaba daya, sannan babu wani farin ciki da al’Uma za su yi. Adalci ne ya ke samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umar duniya. Abu na 2 kuma shi ne kamanta duniya da wani lambau maikatanga, na 3 shi ne dokoki ne suka tabbatar da kasa. Na 4 she idan ba a samu shugabanni ba to ba za a iya aiki da dokoki ba. Na 5 shi ne ana bayyana idan da babu sojoji da shugabann ba su samu damar yin shugabancin kasa ba. Sannan kuma ana fadin da babu haraji wato kudi da ba a iya tattara sojoji ba. Sannan kuma al’uma ce za ta tara dukiya ga kasa. A daki na karshe na gidan adalci akwai kiran tabbatar da adalcin. Saboda idan ana son al’uma ata bayar da haraji dole sai ta zama tana da aikin yi Fasdin Shaikh Edebali na “Raya mutum sai kasa ta rayu.” ya zama kamar kalmomin da bayani kanalakar adalci da daula.       

Idan za a tuhumi tsarin da duniya ta ke tafiya a kansa a yau, idan za a bukaci yi wa Majalisar Dinkin Duniya kwaskwarima kamar yadda Shugaba Erdogan ya ke yin kira, to da an magance matsalar da jama’a suke fuskanta a kofofin wasu kasashe inda suke gudu daga wannan nahiya zuwa waccan, wannan tsarin ba zia ci gaba a haka ba. Jarirai da aka kashe saboda rashin samun mafita, idan za a tambayi meye laifinsu, to hakan ba zai zama abin kunya ba ga dukkan bani adama? Kiran adalci da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi, kira ne da zai kawo karshen dukkan zaluncin da ake yi a duniya tare da kubutar da Turai. Saboda Wazirin Daular Selçuk Nizamul Mulk ya yi nuni shekaru 1000 da suka ce”Mulki na wanzuwa da kafurci amma ba da zalunci ba.”Labarai masu alaka