Yarjejeniyar Sochi a Idlib, Damarmaki da Wahalhalu

Yarjejeniyar da aka aiyanar a Sochi; muhimmiyar mataki ce da aka dauka domin warware matsalolin ldlib da suke ciwa kowa tuwo a kwarya a cikin ƴan kwanakin nan.

Yarjejeniyar Sochi a Idlib, Damarmaki da Wahalhalu

Yarjejeniyar da aka aiyanar a Sochi; muhimmiyar mataki ce da aka dauka domin warware matsalolin ldlib da suke ciwa kowa tuwo a kwarya a cikin ƴan kwanakin nan. An dai nemi dakatar da kai hare-haren da gwamnatin ƙasar ke kaiwa yankin ldlib mai mazauna fararen hula miliyan 3.5. Ƙoƙarin da Turkiyya ta yi na dakatar dakai hare-haren soja a yankin ya kasance wata muhimmiyar mataki da duniya ta yi amanna dashi.

A yarjejeniyar da Turkiyya ta yi da Rasha akan ldlib, sun aminta akan kauda makamai daga wani bangaren yankin mai faɗin kilomita 15 zuwa 20. Dukkanin ɓangarorin da suka haɗa da dakarun gwamnati da yan adawa  zasu ajiye makamansu a yankin, haka kuma za'a fattataki ƴan ta'adda daga yankin baki ɗaya. Za'a kuma buɗe hanyoyin M4 da M5 da suka haɗa Lazkiye da Shami Halep domin sufurin fararen hula. Sai dai duk da irin fa'idar dake tattare da yarjejeniyar da Turkiyya ta yi da Rasha a Sochi akwai ƙalubale da ka iya kawo cikas akan gudanar da yarjejeniyar.

Babban matsalar Rasha game da tabbatar da yarjejeniyar Astana ita ce: ƙungiyar shi’ar da lran ke goyawa baya, musamman yadda lran bata halarci taron Sochi ba ka iya sanya ta zama ƙalubale akan gudanar da yarjejeniyar. Duk da cewa lran da gwamnatin Asad sun bayyana goyon bayansu ga yarjejeniyar Sochi suna da wata manufa ta daban a ldlib. Rasha dai nada jan aikin shawo kan kungiyar shi'ar da lran ke goyawa baya domin mutunta yarjejeniyar ta Sochi.

Kasancewar yadda jami'an gwamnatin kasar suƙa ƙi janyewa daga yankin da kuma kai hare-haren da suka dinga yi a yankunan da ke hannun masu adawa da ita, sun sanya Rasha cikin wahalar iya daukar kwararan matakai a ldlib.

Haka kuma, dangane da kaddamar da yarjejeniyar Shoci, ita kuwa Turkiyya na fuskantar matsaloli ne kasancewar yadda manyan kasashen yankin basa aiki kamar yadda Turkiyyar ta tsara. Duk da dai Turkiyya wacce keda sojoji mafi yawa a yankin ldlib tana gudanar da aiyukan ta tare da haddin gwiwar sojojin yankin masu zaman kansu, tana da kokonto akan aiyukan lran, Rasha da gwamnatin Asad a yankin.

Babban matsalar Turkiyya akan aiyanar da yarjejeniyar Sochi a ldlib ita ce: ƙungiyoyin tada zaune tsaye dake yankin. A yankin ldlib akwai kungiyoyi guda biyu, da farko dai akwai Heyet Tahrir el Sham, na biyun kuwa sun hada da wasu kanana da manyan kungiyoyin dake yankin. Kungiyar Heyet Tahrir el Sham na kokarin jan ra'ayin mutanen yankin domin gudanar da ayyukan ta. Bugu da kari tana kuma kokarin yaɗa akidun ta a yankin. Kasancewar yadda kungiyar bata fitar da ra'ayin ta akan yarjejeniyar Sochi a fili ba nada muhimmanci saboda za'a iya shawo kanta domin goyon bayan yarjejeniyar da kuma ajiye makamai dama ƙauracewa yankin baki ɗaya.

Sai dai kash, a yankin kuma akwai wata kungiyar tada ƙayan baya mai suna Hurrash Ed Din wacce da haɗin gwiwar Alƙaida tayi fatali da ababen da aka aminta dasu a Sochi, a sabili da haka ya zama wajibi ga Turkiyya ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da sauran kungiyoyin yankin dake bin umurnin ta domin kauda kungiyoyin dake tada zaune tsaye a yankin.

Turkiyya wacce ta kauda wasu ƴaƴan ta'addar DEASH da PKK-YPG daga wasu yankunan Siriya, tare da bin ka'idodin yarjejeniyoyin Sochi da kuma ta ƙasarta ya kamata ta kauda dukkanin nau'o'in ta'addanci daga ldlib. Yaƙar ta'addanci da Turkiyya ka iya yi zai samar da kwanciyar hankali da lumana ga al'ummar Siriya dake ldlib baki ɗaya

 

Wannan sharhin Mal. Yazar Can ACUN ne daga cibiyar nazarin siyasa da tattalin arziki wato SETA dake nan Ankara babban birnin ƙasar Turkiyya.Labarai masu alaka