Nasara a Gurbataccen Zamani

Za mu gabatar muku da sharhin Farfesa Kudret Bülbül na tsangayar ilimin siyasa na jami'ar Yıldırım Beyazit na Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.

Nasara a Gurbataccen Zamani

Matsalolin Kasashen Duniya: 43

Za mu gabatar muku da sharhin Farfesa Kudret Bülbül na tsangayar ilimin siyasa na jami'ar Yıldırım Beyazit na Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.

Aliya: Nasara a Gurbataccen Zamani

Karni na 20 miladiya, lokaci ne na tabarbarewar lamurra a duniyar Islama,zamanin da aka mamaye kasashen Musulmai daya bayan daya,lokacin mace-mace,tsangwama da na yaduwar bakin ciki da ukuba tamkar ruwan dare gama duniya.A irin wannan karnin, Aliya İzzetbegoviç na daya daga cikin sanannun sunaye masu wuyan samu,wadanda kuma ke iya dora duniya kan kyaukyawan tafarki.Shi ne jagoran da a wannan zamanin da Musulunci ya daina zama daya daga cikin hanyoyin madadi,ya sadaukar da rayuwarsa da kuma kara kaimi wajen gabatar da Islam a matsayin mafita ga bil adama.

Shekarun Kuruciya da na rayuwar kurkuku na farko: Kungiyar Mladi Müslümani

An haifi Aliya İzzetbegoviç wanda aka rada wa sunan kankansa a shekarar 1925.Takwaransa Aliya ya samu horonsa na soja a yankin Üsküdar na birnin Santambul,inda ya auri wata Baturka mai suna Sıddıka Hanım.Watakila shi yasa,a kulli yaumin nake jin wani shauki na lullube ni a garin Aliya da kuma daya daga cikin muhimman unguwannin Santambul,wato Üsküdar mai kayan Tarihi da kuma yaanayi: Nutsuwa, dattijantaka,girma da kuma kyan birnin sun samo asali ne daga tarihin yankin.Ranar haihuwa da kuma kuruciyarsa, wato karshen yakin duniya na farko da kuma yakin duniya na biyu sun kasance lokuta mafiya wahala.Wadannan lokutan masu cike da tashe-tashen hankula da rashin tausayi, sun jefa Musulmai,musamman ma na yankin Balkans, cikin halin ha’ula’i.A karshen yankin duniya na farko, Yammacin duniya wacce ta kawo karshen Rashar Stalin da ke karkashin inuwar Kwaminisanci da kuma rassanta,wato Nazi da kuma Farkisanci,ne suka yi galaba.

Bayan durkushewa da kuma rugujewar daular Usamnaniya,Musulunci ya daina zama hanyar madadi tsawon shekaru 200.A cikin irin wannan yanayin ne, Aliya da abokansa na makarantar Sakandari suka kafa kungiyar Matasa Musulmai, “Mladi Müslümani”.Wannan kungiyar ta yi kokarin samar da kyawawan tunace-tunacen Musulunci, a daya bangare kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen kauda kuncin da yake-yake suka haifar a zukatan jama’a.

Amma gwamnatocin Zidikanci da na Kwaminis wadanda su ne ke mulki a yankunan da suke, ba su yi maraba ba da yunkurin nasu.Abinda yasa Aliya ya share shekaru 5 a kurkuku tun a farkon kuruciyarsa.

Aliya na tsakar Gabas da Yamma

Bayan ya fito daga kaso, Aliya ya ci gaba da gudanar da aiyyukansa don fa’idantar jama’a.Yayin da yake ci gaba da fadi tashin gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum, a daya gefe kuma ya kasance a gwagwarmayar samar da sabbin hanyoyin magance matsalolin da duniya ke fama da su a karninsa.A aikinsa mai taken ”Musulunci,tsakanin Gabas da Yamma”,ya bada ra’oyinsa kan gabashi da kudancin duniya ta mahangar Islama,inda ya kira wadannan sassan duniyan biyu da su koyi zama tare.

A soke-soken da ya yi kan yammacin duniya, Aliya ce: “ A duk lokacin da na kuduri zuwa Turai,ba ni shakkun komai.Saboda mu ba mu kashe yara, mata da kuma tsaffi ba.Haka zalika ba mu rushe tsarkakkun wurare ba.Alhali ko su, sun aikata dukannin wadannan laifukan a gaban idon Yamma. Da suna wayewar Yamma”.

A cewar Aliya, manyan matsalolin duniyar Islama, su ne rarrabuwar kanu,jahilci da kuma gaggarumin bambancin da ke akwai tsakanin aiyuka da kuma lafuzzan baki. Fadar Aliya ta ”A ganina, Islam ta fi mun komai, tunda ita ce asilin komai”, wani babban kira ne ga Musulmai da su gyara halayensu.Aliya ya ci gaba da cewa: “ Babu makawa Musulunci shi ne addini mafi a’ala,amma mu kan ba mu kasance mutane mafi a’ala ba.Wadannan ababe ne biyu da muka kasa bambantawa kawo yanzu”.Amma sai ya ce ga mafita :” Idan muna son mu zama malami a doron duniya, to ya kamata mu zama dalibin samaniya”.

Zamaninnikan Yaki…

Kafin sake yin gunduwa-gunduwa da yankin Balkans,Aliya ya tsinci kansa a gidan wakafi,inda ya share shekaru 14, sabili da littafinsa mai suna “İslam Manifestosu”.Bayan shekaru 5, wato a shekarar 1988 sai aka yi masa afuwa.A shekarar 1990 ya kafa jam’iyyar “Party of Democratic Action”.Zaben da aka gudanar a wannan shekarar ya ba shi damar hawa kan karagar mulki a matsayin shugaban kasarsa na farko.A shekarar 1992, Bosna Hersek ta ayyana cin gashin kanta daga Yugoslavia.Kamar yadda ta saba, munafukar Turai ta rufe idanunta kan kisan kiyashin da Sabiyawa suka yi Bosniyawa, duk da cewa a baya ita ce ta mara wa al’umomin kasashen Croatia and Slovenia baya wajen ballewa daga Yugoslavia.Wanda hakan ya yi sanadiyar daruruwan dubban rayukan mutane,jikkata, hijirce-hijirce,matsananciyar yunwa da kuma zubar jini.A karshen karni na 20 miladiya an tafka mafi mummunan kissan gilla ba tare da duniya ta ce uffan ba.A lokutan yake-yake Aliya ya zama daya daga cikin sannanun shugabannin duniya.Duk da wahalhalu da kuma tashe-tashen hankula da ake fama da su , ya yi nasarar nuna wa duniya,musamman Musulmai, hanyar da zasu bi don kubuta daga halin ni 'yasun da suke ciki,inda ya yi amfani da kwarewar da ya samu cikin walaha da kuma tsangwama.Aliya yayi na’am da yunkurin Bosniyawa na daukar fansar kashe-kashen mata,yara da kuma dattijansu da Sabiyawa suka yi,amma ya ce kamata yayi a gudanar da yaki ta hanyar bin doka da oda da kuma jan hankali jama’a da su guje wa tunace-tunacen yin tawaye.Kamar yadda ya bayyana, ga muhimman ka’idojin yaki:

“Muna bin makiyanmu bashi daya tak: Adalci”

“Sabiyawa ba malamanmu ba ne”

“Ba a sa’ilin da aka ci mu yaki ba, a lokacin da muka yi kama da makiyanmu ne ake galaba kanmu”.”Littafina ya haramta mun yin haka” ita ce amsar da ya bai wani mai rahoton Jamus wanda ya yi masa tambaya kamar haka: “Shin me yasa ba ku dauki fansa ba, duk da zalunci da aka yi muku? Shin ko wayewarku ta Gabashin duniya ce ta yi muku hani da hakan ?”.Wannan wata babbar ishara ce da ke nuna yadda Aliya ya martaba tunace-tunacen da suka ginu kan karantarwar Islam.Kin rungumar ra'ayoyin Bosna Hersek,ba wai yana nufin tunace-tunacensa guragu ne ba.Wannan ita ce irin mu’alamar da Amurka da kawayenta na karnin da muke ciki ke yi wa wadannan Musulman da ke tsakiyar Turai.

Tarihi…

"Sun binne mu,fakat basu fahimci cewa ba mun tsiro".Wannan kalami ne da Aliya ya furta game da al'umar Balkans,duk cewa ya shafi tarihin Musulmai wanda ke da tsawon shekaru 200. A wadannan karnoni biyu masu cike da bakin ciki da koma baya,ba a samu irin wadannan jaruman jagorori ba.Kamar a yadda muka dasa aya a makalan da suka gabata,inda muka ce: "Shin ko yaya zamu kusanci Yammacin Duniya ?", bai kamata ba mu dinka sukar lamiri ko kuma wakiltar Yammacin Duniya a makance ba,abu mafi a 'ala shi ne kusantar ta cikin hikima da hangen nesa.Shugabannin masu irin wannan halayen ne ke iya warware matsalolin al'umominmu.Kamar Said Halim Pasha, İkbal, Akif da kuma Rashid El Gannushi, Aliya ma ya kasance daya daga cikin gwarzayen duniyar Islama,wadanda suka daura damarar daga martabar Islama a karninsu.

Shugabannin da ke tsunduma al'umominsu daga wannan halaka ya zuwa wancan,duk da zaluncin da suke fuskanta, wadanda ke jagorantar su kan tafarkin karya, masu furta kalamai marasa tushe, masu da'awar bambancin kabilu,wadanda basu tunanin karsarsu da al'umarsu, ba zasu taba amfanar kowa ba.

Kamar Aliya, wanda duk da tsangwama da kuma zalunci da ya dinka kacibus da su, bai yi tunanin daukar fansa ba, ya dukufa wajen tabbatar da adalci a ko ta halin kaka duba da karantarwar Islama, kana ya iya yin tsokaci ta hanyar amfani da kwarewa, dattijantaka,ilimi,basira, hikima, da kuma addininsa,su ne irin shugabannin da ake bukata ba a kasashen Islama ba,kai har ma da sauran sassan duniya.

 Labarai masu alaka