Za a bude sabon shafin samar da makamashi a Turkiyya

A makon jiya ne anka ƙaddamar da gina kanfanin matatar mai; mai suna STAR da za'a yi tsakanin Turkiyya da Azerbayjan.

Za a bude sabon shafin samar da makamashi a Turkiyya

Kanfanin da zai ƙara samar da mai a fadin duniya zai ƙara haɓakar da tattalin arziki tare da kuma nuna irin haɗin gwiwar dake tsakanin Turkiyya da Azerbayjan.

Tamkar dai haɗakar TANAP da aka ayyanar; wannan kataɓaren aikin tsakanin Turkiyya da Azerbayjan da ake ci gaba da ingantawa a ko wacce rana, zai ƙara samar da iskar gas dama man fetur. Wannan haɗakar da zai rage shigowa da man diesel a ƙasar Turkiyya, zai kuma magance naƙason kuɗaɗen da ake samu a shekara. Haƙiƙa matatan man Star babban jari ce ga ƙasashen biyu.

A wannan makon ma mun sake kasancewa tare da ferfesa Erdal Tanas KARAGÖL malaminmu a sashen siyasa da tattalin arziki a jami'ar Yıldırım Beyazıt.

 Daga cikin mafi yawan ababen da Turkiyya ke shigowa da su ƙasar ta daga ƙasashen ketare sun haɗa da gurɓataccen man fetur da kuma tatsettsiyar man fetur ɗin. A yayinda Turkiyya ke shigowa da gurɓataccen man fetur na ton miliyan 25 tana kuma siyar man fetur na ton miliyan 18 a shekara.

Matatan man Star zai samawa ƙasar Turkiyya kusan kashi 25 na nau'o'in man da take buƙata a shekara. Hakan na nuni ga anan zuwa gaba sanadiyar wannan matatar man Turkiyya zata fara tace mai a cikin gida lamarin da zai rage shigowa da mai da take yi daga ƙasashen waje.

Haka kuma za ta magance matsalolin naƙason kuɗaɗen da take samu sanadiyar siyar man fetur daga ƙasashen ketare, haka kuma wannan mataki ne da zai rage dogaro ga kasashen waje da Turkiyya ke yi domin siyar man fetur. Hakan na karantar da cewa wannan matatar Star zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Turkiyya.

A sanadiyar wannan matatar naƙason kuɗaɗe har na dala biliyan 1.5 da ake samu a fagen kasuwanci da sauran ƙasashe zai ragu. Hakan dai wata mataki ne daga cikin matakan da ake dauka ko wacce rana domin inganta lamurkan tattalin arzikin kasar.

Wannan matakin akan man fetur mai daraja, zai ƙarawa Turkiyya ƙarfin gwagwarmayar kasuwanci da sauran ƙasashe, haƙiƙa wannan matakin zai rage naƙason kuɗaɗen, samar da aikin yi da kuma inganta lamurkan makamashi a cikin ƙasar baki daya.

A yau dai, Azerbayjan dake yunkurin fara fitar da iskar gas din Hazar zuwa Nahiyar Turai, na da buƙatar ƙasar Turkiyya ta ko wacce fani. Domin ta ƙasar Turkiyya ce za'a iya bi da bututun, haka kuma za ta iya neman tallafin ƙuɗaɗe daga Turkiyya domin gudanar da ayyukan. Bugu da ƙari, Azerbayjan ka iya neman tallafin Turkiyya domin ayyukan kanfuna, saka hannun jari da makamantansu daga ƙasar Turkiyya.

Zamu iya ganin yadda wannan haɗakar gina matatar mai ta Star tsakanin Turkiyya da Azerbayjan ke ci gaba da samun tagomashi a ko wacce rana.

Waɗannan ƙasashen biyu sun haɗa ƙarfi da ƙarfe domin inganta lamurkan gas din yankin a yayinda suke gudanar da ayyukan inganta lamurkan hannayen jari a tsakaninsu.

Turkiyya dake yunkurin kasancewa cibiya samar da iskar gas da makamashi na ƙulla wata babbar haɗaka da Azerbayjan tamkar yadda take yi da sauran ƙasashen yankin masu dimbin makamashin.

A yau dai wannan kataɓaren matakin da aka dauka domin inganta lamurkan, saka hannayen jari da tattalin arzikin kasashen biyu. Anan zuwa gaba zamu yi sharhi akan yadda za'a ci gaba da gudanar dashi, bunƙasa shi da kuma inganta shi cikin tsanaki.Labarai masu alaka