“Ko Tarwatsawa ko Adalcin Dunya”

Muna gabatar muku da sharin Shugaban tsangayar Nazarin Siyasa dake jami’ar Yildirim beyazit Farfesa Kudret Bulbul.

“Ko Tarwatsawa ko Adalcin Dunya”

Matsalolin Kasashen Duniya: 44

Karni na 20 karni ne da dan adam ya fuskanci matsaloli mafiya muni. A wannan lokacinne aka samu yake-yake mafiya muni wajenzubar da jini. Kuma na dauke da bama-baman kare dangi da suka hallaka bani adama.

Tsarin da aka kafa bayan yakin duniya na 2, da irin darussan da aka dauka, ba tsari ba ne da zi samar da zaman lafiya na gaba daya. Tsari ne da yake kare manufofin mutanen da suka yi nasara kawai. Tsarin Bretton Woods da ya ke kare martabar Dalar Amurka  da mayar da ita kudin da ake amfani da su a duniya baki daya, tsarin Majalisar Dinkin Duniya ma tsari ne da ya ke yin hidima ga wadannan kasashe da suka yi nasara.

A lokacin yakin cacar baki tsarin Bretton Woods da aka kawo ya yi illa,irin wannan illar tsarin majalisar Dinkin Duniya ke yi a yanzu.

Asali dai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na raba karfi ne tsakanin kasashe mambobinsa na dindindin da suka hada da Rasha, Amurka, Ingila, Faransa da China.

Bayan kawo karshen duniya ta rabu gida biyu, amma wasu bangarorin daban kuma sun ci gaba da tabbatar da wancan tsarin da ake da shi a baya. Hadin kan kasa da kasa na ci gaba da wannan ta’asa a kasashen Iraki, Afganistan, Bosniya, Cremea, Siriya, Arakan wanda hakan ke kara nuna mana yadda suke da zubin aiyukansu.

Tsarin duniya na yau da yake wani cigaba na zamanin yakin cacar baki, kuma a lokacinda duniya ke hadewa waje gıdana ana suka ga wanan tsari saboda matakin da yake a kai. A saboda haka ne a duk lokacinda Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya samu dama ya ke cewa, duniya ta fi kasashe 5 girma. Haka kuma irin kıdaden da ake kashewa saboda rashin adalcin da ake yi yau a duniya na kara daduwa a koyaushe. Tsarin cacar baki ba zai ci gaba ba a lokacinda ake kallon ana ta nuna rashin adalci da danniyakarara bayan ana iya samun dukkan bayanai.

A yau muna rayuwa a wani zamani ne na rashin tabbas da ke komawa ga “tsohon halinsa”. Matsayin da aka zo a yau shi ne anda a yaren Turkanci ake kira “Tsohon hali, ko a ce koa samar da sabo yanayi ko adalcin duniya.” Eh, kudaden da ake kashe wa wajen cigaba da aiwatar da tsohon tsarin da ake kai na daduwa. Amma manyan masu taka rawa a duniya kamar yadda yake babu a tarihinsu,  to suna amfani da makaman kare dangi wajen karar da bani adam da ma dabbobi daga ban kasa. Kamar yadda ake iya tsinkaye a yau, a lokacinda tsarin rashin adalc, yake tabbata a bangaren shugabanci, to hakan na nufin dukkan duniya na karkashin barazana. A tsarin da ake suka da tuhumar tsarin zamanin cacar baki amma kuma aka gaza samar da sabon tsari mai kyau, to ba za a samar da wani tsari dai zai taimaka wajen  samar da zaman lafiya da aka yi niyyar samarwa ba bayan yakin cacar baki.

Domin samun adalci a duniya akwai bukatar a yi tunani sama da kasashe kawai. Dole ne a nuna kokarin samar da dalaci a dukan wasu bangarori na duniya da za a tabbatar da an tabo dukkan bangarori da suka hada da na wasanni, aksuanci, jami’o’i, ‘yan kasuwa, kungiyoyin masu sana’a, kungiyoyin lauyoyi da na fararen hula saboda suna da muhimmiyar rawar takawa. Da fara za a kara kokarin ganin sun san juna tare da kara yawan hadin kai da aiyykan dake tsakaninsu. A baya a lokacin yakin cacar baki ba za a iya tsayawa a gaban wata kafar yada labarai ananeman mafita ba.Amma a yau saboda cigaban da aka samu a bangaren fasahar sadarwa, karuar wayewar dan dama da budewar idanuwansa ya sanya a kasashe daban-daban kuma a tsakanin mutane mabambanta ana samun hadin kai. Idan ka dauki dalibai za ka samu akwai na ksa da kasa. In ka dauki bangaren ‘yan kasuwa za ka samu suna da tasu kungiyar ta kasa da kasa. Dole ne mu zama a yanayi na neman mafita ta irin wannan hanya.

A lokacinda da barazana take kara yawa, ake ta samun rusau a kusa da duniya dukka, to ba za a iya samun mafita ba. Musulmi, Kirissta, bayahude,Bamaguje, Mabiyin Budha, da ma ko wanne irin addini, tunani, imani, to ,dan muka kalli halin da muke cik, za mu ga akwai bukatar hada kai, zama tare don warware matsalolin dake damun mu.

Lokaci zuwa lokaci, wannan tsrin yana samun nasara. Yadda a lokacinda Amurka ta dauki mataki ita kadai kan kudus kasashen duniya suka mayar mata da martani a zauren Majalisar Dinkin Duniya, da yadda kasashen suka yi wa Saudiyya caaa kan kisan gilla ga kashoggi na sanyaya zukatanmu kwarai.  

Abu mai kama da wannan shi ne, hadin kan kasashen duniya zai iya zama ginshikin tabbatar da adalci. Za a iya daukat hada kai wajen yaki da nuna wariya, kyamar baki da ‘yan gudun hijira, magance ra’ayin Nazi, kyamar Musulunci da nuna wariya na iya zama misali.

Dole ne kowanne bangare ya yi kokarin ruwa rashin adalci na duniya. Dole mu takura wajen neman adalci a duniya. Ko ma daga wanne addini, launin fata, tunani ka ra’ayi muka fito, ko waye ya zo da zalunci dole mu hadu mu magance shi a matakin kasa da kasa ba to ba za a taba rasa rashin adalcin ba. Saboda babu wata kasa ita kadai da za ta iya kare kanta daga barazanar zaluncin duniya. Dole a hada kai waje guda.

A yau muna wani zamani da ba a tabbatar da tsarin adalci a cikinsa ba. Kusan a ce duniya na rayuwa a tsaka mai wuya. Muna da damar samar da duniya da za ta tabbatar da adalci. Dole a matsayinmu na dan adam mu tashi tsaye wajen aiki don tabbatar da gaskiya da dalci a doron kasa. In ba haka ba, a lokacinda aka samar da tsari irin na baya mara adalci, ko kuma daya daga cikin manyan kasashe dake rawar hantsi a duniya, za ta harba makaman kare dangi ta haifar da Kiyama ta karfi da yaji.Labarai masu alaka