Siriya Bayan Babban Taron Kasashe 4

A taron da aka gudanar a birnin lstanbul da ya samu halartar shugabanin ƙasashe huɗu da suka haɗa da na Faransa, Rasha, Jamus da Turkiyya an ɗauki matakin samar da zaman lafiya a Siriya ta kafa kwamitin kafa kundin tsarin mulki a ƙasar.

Siriya Bayan Babban Taron Kasashe 4

A taron da aka gudanar a birnin lstanbul da ya samu halartar shugabanin ƙasashe huɗu da suka haɗa da na Faransa, Rasha, Jamus da Turkiyya an ɗauki matakin samar da zaman lafiya a Siriya ta kafa kwamitin kafa kundin tsarin mulki a ƙasar.  Duk da irin muhimmin matakin da aka dauka dai, ƙasar Siriya na cigaba da fuskantar matsaloli da dama. Idan muka dubi iyakokin Siriya da lraƙi zamu ga cewa ƙungiyar ta'addar DEASH da YPG na ci gaba da baje kolinsu tare da faɗace-faɗace da kuma tada zaune tsaye a yankunan. Haka kuma ganin yadda ƴan ta'addar YPG suke gudanar da hare-haren ta'addanci da ya sanya rundunar sojin Turkiyya kai masu farmaki da tarwatsa sansaninsu na karantar da cewa akwai bukatar ƙara daukar wasu matakan da zummar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Siriyar.

Shugabanin Ƙasashen huɗu da suka gudanar da muhimmin taro a lstanbul sun dauki kwararan matakai domin samar da zaman lafiya a Siriya. Musamman yadda suka kafa kwamitin da zai samar da kundin tsarin mulkin da aka jima ana tattaunawa akai. Duk da dai sabuwar kundin tsarin mulkin da za'a samar nada muhimmanci ga ƙasar ba zai taɓa zama matakin warware rikicin dake addabar ta ba. Bayan ma kammala rubuta kundin tsarin mulkin samun karɓuwarsa ga al'ummar Siriya lamari ne da zai dauki lokaci kuma mai ma wuyan gaske. Miliyoyin ƴan ƙasar Siriya na zaune ne a kasashen waje, haka kuma da yawansu sun yi ƙaura daga gidajensu inda wasunsu saboda matakan gwamnatin Asad suka kasa samun takardar shedar ɗan ƙasa kamar Pasaport da makamantansu lamarin da ka iya hana su samun damar kaɗa kuri'a idan lokacin zaɓe ya zo.

Duk da haka, an dai dauki muhimman matakan da suka haɗa da tsagaita wuta a yankin ldlib, ci gaba da fatattakar ƴan ta'addar. Bugu da kari wannan mataki ne muhimmi da Turkiyya ta ɗauka ta hanyar diflomasiyya domin kauda kungiyar ta'addar YPG dake ƙalubalantar zaman lafiya a kasar Siriya.

Idan muka dubi lamurkan ƙasar Siriya a halin yanzu, zamu ga cewa a iyakokin Siriya da lraƙi kungiyar ta'addar YPG da DAESH na ci gaba da tada zaune tsaye a yankin. Tare da goyon bayan dakarun ƙasashen Amurka da Faransa na musamman kungiyar YPG ta Soma kai hare-hare a yankunan Haji dake ƙarƙashin DAESH a watannin da suka gabata.

 Kungiyar DAESH kuwa ta yi amfani da guguwar da ke addabar yankin inda ta karɓe ikon yankin da YPG ke mallaka, bayan kungiyar DAESH ta karɓe yankin gwamnatin lraƙi ta soma ɗaukar matakan kare hare-haren da kungiyar ke kaiwa inda ta tura dakarun Hashdi Shabi a yankunan. Duk da irin taimakon da kungiyar YPG ke samu daga wasu ƙasashe bai iya bata karfi dakatar da mamayar da Ƙungiyar DEASH ke yiwa yankunan ba. Akwai alamun tambaya akan yadda YPG ke ƙoƙarin nuna ingancin ta da kuma daukar matakan kauda DEASH.

Ƙungiyar YPG ta ɗanɗana kuɗanta a lokacin da take yunkurin ƙalubalantar DEASH  a kudu maso gabashin Siriya. Rundunar sojin Turkiyya ta dauki matakan magance kungiyar YPG da suke ƙara tada  ƙayan baya a arewacin Siriya dake da makwabtaka da Turkiyya, haka kuma rundunar sojin ta lalata maɓuya da mafakar kungiyar a yammacin Ayn el Araba, haka kuma a Taka Abayd anyi bata kashi tsakanin kungiyar da dakarun kasar Turkiyya. A kwanakin baya kungiyar YPG ta harba wata roka daga sansanoninta zuwa yammacin Ayn el Arap. Yadda kungiyar YPG ke neman Turkiyya ta dakatar da hare-haren da take yi a yankunan na nuni da ƙalubalantar da take yi wa DEASH a yankin Haji tana yi ne kawai domin ƙashin kanta.

 Wani lamarin da zamu duba kuma shi ne; rigingimu dake faruwa a yankin ldlib. Yarjejeniyar Sochi da aka ayyanar ya ɗan dakatar da hare-haren da ake yi a yankin. A ƴan kwanakin da suka gabata dai munga yadda rikici ya barke tsakanin kungiyar Tahrir Ush Sham da ta Nureddin Zengin. Duk da dai ƙalubalantar da masu adawa da gwamnatin Siriya suka yi wa kungiyar Tahrir Ush Sham bai ɗauki tsawon lokaci ba; na nuni ga irin rashin zaman lafiyar dake yankin. Domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Siriya, akwai bukatar a samar da zaman lafiya da warware rikicin yankin ldlib.Labarai masu alaka