Musuluncin Turai?

Muna gabatar muku da sharihin Farfesa Kudret Bulbul Shugaban Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim beyazit dake Ankara.

Musuluncin Turai?

Matsalolin Kasashen Duniya: 45

A wani tsawon lokaci ana ta cacar baki game da Musulunci a nahiyar Turai. Yawancin cacar bakin da ake yi an fi alakanta ga Musulmai inda dukkan bangarorin da suka hada da malaman jami’o’i, kasashen Turai da jagororinsu da marubuta suke ta cece -kuce da musayar ra’ayi.

Asali wannan cece-kuce ba wai cece-kuce ba ne da ba ya isa. A lokacinda duniya ke hadewa waje guda mutanen dake da addini, Al’ada, da yanyin rayuwa mabambanta na cakuduwa waje daya tare da rayuwa. A lokacinda wannan lamari ya za a kasashe da yawa, kamar yadda yake a daular usmaniyya, amma a wajen yammacin duniya sabon abu ne. A shekarun baya akwai alaka tsakanin aksashen Turai da suke mulkin mallaka da kuma kasashen da ake mulkn mallakar, kuma za a iya cewa a wannan lokacin jama’ar kasashen na tashi su tafi zuwa Turai. A wannan lokacin ne ake fuskantar matsaloli na kasashe saboda yadda suke haduwa a waje guda.

Al’adar Trurai da ta dace da Musulunci

Irin sakamakon da jama’a da suke zaune tar ewadanda suke da tarihi, Addini da al’ada daban-daban zai haifar, hakika zai shafa tare da tasiri kan kasashe, hukumomi, ilimi da ake da su. Idan ana maganar Musulunci a Turai ba wai ana maganar wani sabon Musulunci da ya zo Turai na daban ba ne, kawai dai yadda a cikin Turai din aka samu wasu al’adu da dabi’u da ake su tafi tare da dacewa da Musulunci. İdan aka so bayyana Turai tare da Musuluncin dake nahiyar, ta mahangaryare da al’ada za a ga ia abinda ake iya hange ne a Musulunci. Idan aka gkalli haga za a ga tushen da Musuluncin Turkiyya da na gabas mai nisa, na kasashen Balkan da Asiya duk guda daya ne. Amma kuma za a ga suna da bambanci wajen aikata su. A karkashin wannan za a ga Musulman Turai ba suna ta Musuluncin bakin da suka je kasashensu ba ta yadda zai dace da dabi’unsu, idan har za su zauna a cikin Musulunci, to dole ne lallai a samu al’adu da fahimta ta Turai da ta dace kokuma za ta tafi daidai da Musulunci. Kamar yadda al’adu, zamantakewa, Adabi, hikayoyi da labarai na Afirka, gabas ta tsakiya da na gaba mai nisa suke, haka a ma Turkiyya a an yar da da su tare da amincewa, amma a Turai kuma ba a yarda da irin wannan abu. Kowacce al’uma na kokarin gani duk wani bako da yazo wajenta ya saje a ita tare da aiki da al’adunta.

Al’adar Turai da ta dace da Musulunci ba wai ta shafi iyakacin wadanda suka je Turai ba ne, akwai bukatar a kalli batun duba da ita kanta Turai din. Idan muka ce al’adar Turai da ta dace da Musulunci, to muna maganar a yi watsi da munanan al’adu na Turai da suka hada da nuna kyama da wriya da ma akidar Nazi.

A wasu lokutan da ake karfafa batun Musulunci a Turai, ana amfani da maganar mutanen da suka je Turai wadanda ba su da al’adai dabiu da halayya irin na mutanen Turai. In haka ne za a iya cewa a kusa Turai ta nesanta daga wadannan dabiU. A yanzu masu neman mafaka na fuskantar nuna wariya da kyama daga Turawa. A binciken da ake yi ana gani abubuwan tsoro da fargaba inda ba ma sa son masu neman mafakar su makwabce su.

Musulunci mai tsaro ba wai mai’yanci ga Turai ba

A rubutun da aka yiyyi za a ga yadda ake cacar baki kan Musulunci a Turai ta karkata ga batutuwa da ba su shafi al’adu, zamantakewa ko dabi’un jama’a ba. Kasashen Turai na bibiya da kallon wannan cece kuce ta fuskar tsaro. Shi ya sa da ma ba a aiyukan ta fuskan-r al’adu ko zamantake, an fi mayar da hankali ga bangaren tsaron kasashen.  Idan akwai wata matsalar tsaro, to aa daukar matakan rigakafi nan da nan. Wannan abu ne da ba za a yii cece kce game da shi ba. Idan za a ce a bangaren tsaro ne kawai za a kalli bautruwan da suka shafi al’uma to akwai matsala sosai. Dole ne a yi kokarin sananin hakan, inda kasashen Tıraisuke ta kokarin suke daukar matakan da ba su dace ba wajen kafa hukumomin kula da Musulunci a kasashensu. Kuma kamata ya yi wadannan hukumomi a ba wa Musulmai fararen hula damar kula da su ba a wai a ba wa jami’an tsaro ba.

Nauyin dake kan Musulmai...

Game da alakar musulunci da Turai, ba daidai ba ne a soki wasu kasashe game da nauyin da ya hau kan al’umar musulmi. A YAU İDAn akwai matsalolin tattalin arziki, zamantakewa, siyasa da ilin Musulmai a duniya, dan laifuka suka yawaita, sannan babu al’adar aiki da yawa, to akwai rikici a tsakanin Musulmai da kungiyoyi da dama.

Akwai bukatar Musulmai su zayyana irin matsalolin da suke fuskanta a kasashensu.  

Mahukuntan wadannan aksashe kuma akwai bukatar su yi aiki tare a waje guda, tare da hada kai domin tafiyar da irin tsoro da fargabar da aaka samar.

Musulunci da ya rasa zamantakewa me zai kara wa Turai?

A wani bangan-ren abinda Turai mai Msulunci take son cimmawa si ne Musulunci wanda yake ba shi da duk wasu abubuwa da ake ikirari. Idan haka ne, to ba za a iya kwatanta irin zina da dangi, yaran marasa iyaye, auren jinsi da ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauran sassan duniya ba. Idan aka kalli batun darajojin dan adam za a ga cewar komai babu shi ya kare cikin sauri. Yadda ake ta samun matsalolin tattalin arziki abun ya zama kamar wata gobarar daji. Musuluncin da za a ce yana rasa insaniyya ba wani abu yake janyowa ba sai rusa Turai.

Kiristoci da Yahudawa dole ne su taimakawa Musulmai

Irin wannan Musuluncin babu wani abu da zai haifar, kuma mun ga yadda Musulmai da Kiristoci suke rayuwa da abubuwan da suka same su. Ina tunanin yadda a yau dabi’u suke lalacewa, ake rasa daraja da kima da nuna son kai, abu ne da yake damun Kiristoci da Yahudawa su ma. Haka ma wadanda ba su da Addini suna damuwa da irin wannan abu. Saboda haka akwai bukatar Kiritstoci da Yahbudawa su nuna damuwa game da wannan abu da ake rasawa.

Dole ne Musulman Turai su jagoranci manufofinsu

Duk sama da wadannan abubuwan, dole Musulmai a Afirka, a Gabas ta tsakiya, a Amurka, a Turai da ma ko’ina su kasance suna shugabanta tare da jagorantar manufofinsu. Yaya ne? Bari mu dakata a nan sai mu ci gaba a mako mai zuwa.Labarai masu alaka