Alakar Turkiyya da Kirgizistan

Za kuma mu gabatar da sharihin malami a sashen Nazarin Alakar Kasa da Kasa dake Jami’ar Karatekin a nan Turkiyya Dr. Cemil Dogac Ipek.

Alakar Turkiyya da Kirgizistan

Alakar Jamhuriyar Kirgizistan dake da muhimmanci a tsakanin kasashen tsakiyar Asiya da Turkiyya na ci gaba da habaka a bangarori daban-daban. A wannan makon za mu kalli wannan alaka a cikin shirin namu da kuma irin tasirinta kan manufofin Turkiyya a kasashen waje.

A ranar 16 ga watan Disamban 1991 ne Turkiyya ta zama kasa ta farko a duniya da ta amince da samun ‘yancin kan Kirgizistan. A ranar 29 ga watan Janairun 1992 kasashen 2 sun kulla alakar diplomasiyya. A shekarar ta 1992 suka bude ofisoshin jakadancinsu a Bişkek da Ankara.

A yau alakar Turkiyya da Kirgizistan na a wani mataki mai matsayin gaske. Kasashen biyu sun kulla alaka a bangarori da dama da suka hada da na diplomasiyya, siyasa, tattalinarziki, raya al’adu, lafiya, sufuri da daisauransu. A karkashin wannan alaka an sanya hannu kan yarjeniyoyi sama da 200.

Shugaban kasashen 2 a shekarar 1997 sun sanya hannu kan yarjejeniyar abokantaka ta har abada. A shekarar 1999 an buga bayanan Turkiyya da Kisrgizistan: Karni na 21. A shekarar 2011 kuma an sanya hannu kan yarjejeniya kafa hukumar dabaru ta hadin kai tsakanin Turkiyya da Azabaijan. Wadannan ne takardun da suka zama tushen alakar kasashen 2 a yau. A tsakanin kasashen 2 an gabatar da ziyara musamman ma a matakin shugaban kasa.

Turkiyya na gabatar da aiyuka da dama a Kirgizistan. A shekarun baya ne Hukumar Hadin Kai da Cigaba ta Turkiyya TIKA ta bude asibitin da ta gina mai suna kawancin Turkiyya-Kirgizistan a Bişkek wanda na daya daga cikinn wadannan aiyuka. Hakan ya bayar da dama da za a iya kwantar da ‘yan kasar Kirgizistan kyauta har su 100 a lokaci guda a asibitin tare da ba su magunguna kyaut inda har yarjejeniya aka kulla a kan hakan. A karkashin yarjejeniyar an tanadi yadda duk shekara ‘yan kasar kirgizistan da ba su da lafiya za su iya zuwa asibitocin Turkiyya don duba lafiyarsu.

Kwai kuma Cibiyar Ilimi ta hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Kirgizistan wadda aka saka wa suna Jami’ar Manas. Jami’ar ta zama wani kwakkwaran misali kan kyakkyawar alakar dake tsakanin kasshen 2. A kowacce shekara ana waje dala miliyan 25 domin biyan bukatar daliban wannan jami’a. Turkiyya na bayar da tallafn karatu ga daliban Kirgizistan inda suke zuwa kasar tare da yin karatun digiri na daya, na biyu da na uku a fannoni daban-daban. Haka kuma TIKA na ci gaba da kaddamar da aiyuka a bagarori daban-daban a Kirgizistan. A kwanakin baya ne Shugaban Turkiyya Erdogan ya jagoranci bude Masallacin Juma’a na da Turkiyya ta gina a Bişkek a matsayin kyauta ga Kirgzistan.

A yanzu jarin kasuwancin dake tsakanin Turkiyya da Kirgizistan ya kai dala miliyan 400. Ama wannan adadi ba ya bayyana irin damar da kasashen 2 ke da ita. A nan gaba ana da manufar kara yawan jarin zuwa dala biliyan 1. A shekara dayan da ta gabata adadin jarin ya karu da kaso 26.7 cikin dari. Kasashen biyu na bayar da muhimmanci wajen habaka kasuwanci da hadin kai a tsakaninsu.

Shugaban kasar Kirgizistan Sooronbay Ceenbekov da ya yi nasarar lashe zaben ranar 15 ga watan Oktoban 2017, a jawaban da ya yi da dama ya bayyana irin yadda suka ba wa alakarsu da Turkiyya muhimmanci. Kamar yadda za a iya tunawa, Shugaban Ceen bekov da ya lashe zabe ya ce, za a ci gaba da kare manufarsu ta kasashen wajeinda ya ce “Za mu kara karfafa alakarmu da Tarayyar rasha. Za mu zurfafa dangantakarmu da makocyarmu China. Za ciyar da alakarmu gaba da kasashen tsakiyar Asiya ‘yan uwanmu. Za ci gaba da hulda da kasashen mambobin Tarayyar Turai. Haka ma alakarmu da turkiyya da Amurka za ta ci gaba sosai.”

A tare da zama mamban kungiyar cigaban tattalin arziki da Eurosia, za a iya cewa, Kirgizistan ba ta niyyar sauya akalarta a anan kudsa daga fuskantar rasha. A kwaskwarimar da aka y, wa kundin tsarin mulkin kasar a kwanakin baya, majalisar dokoki ta takaita karfin da shugaban kasa yake da shi wajen kasuwan ci da tsaro na kasa. A hakan ne Shugaba Ceenbekov yake takura sauya manufofin kasar karkashin shekaru 6 na mulkin tsohon shugaban Atambayev. Amma kuma za mu iya ganin yadda alakar kasar da Turkiyya ke ci gaba da habaka sosai.

A yau Turkiyya da  Jamhuriyoyin Turkawan Tsakiyar Asiya na ci gaba da kara karfafa dangantakarsu. Babban dalilin hakan shi ne magana da yare daya da suke yi. Babban marubucin Kirgizistan Cengiz Aytmatov ya ce “A wannan duniyar mai sauyawa komai na iya mutuwa ya tafi kamar yadda dokokin Addinai suka tanadar, amma abinda yake ba ya mutuwa shi ne al’ada.”wannan magana dta masani za a iya rubuta shafukka da ita na irin bayanan da ta kunsa. Saboda haka abban abinda yake rike al’umu a waje guda shi ne al’ada. A wannan bangaren ma akwai babbar alaka tsakanin Turkiyya da Kirgizistan. Ana bayar da fifiko a koyaushe a bangaren Ilimi da raya al’adu a huldar dake tsakanin kasashen 2.

A yauTurkiyya na bayar da muhimmanci ga Kirgizistan wadda ke ta kokarin ganin an samau zaman lafiya da walwala a yankin Tsakiyar Asiya. A karkashin hakan take bayar da taimako ga Kirgizistan a ddukkan wasu bangarori na kawo sauyi. A gefe guda kuma an san a’yan ta’addar FETO sun yi karfi a Kirgizistan. To idana na son alakar kasashen biyu ta kara inganta sosai sosai akwai bukatar kirgizistan ta yaki wannan kungiya a shari’ance.

 Labarai masu alaka