Kashi na biyu na takunkumi ga Iran

Mun sake kasancewa tare da ferfesa Erdal Tanas KARAGÖL dake sashen Siyasa da tattalin arziki a jami'ar Yıldırım Beyazıt.

Kashi na biyu na takunkumi ga Iran

Sake kakkaɓawa lran takunkumi da Amurka ta bayyana yi ya kasance kanun labaran wannan makon. Ta dai janye takunkumin ƙasa da ƙasa da aka sakawa lran sanadiyar yarjejeniyar nukiliyar da aka aiyanar a shekarar 2015. Yarjejeniyar na dauke da cewa lran zata tsagaita lamurkan makaman nukiliyarta lamarin da zai sanya a janye mata takunkumin ƙasa da ƙasa da aka kakkaɓa mata. Gwamnatin Donald Trump da bata gamsu da wannan yarjejeniyar ba, a watan Agusta ta bayyana cewar zata sake kakkaɓawa lran takunkumi, a halin yanzu dai ta sake kakkaɓawa lran takunkumi karo na biyu. Wannan takunkumin zai tauye tattalin arzikin lran da kuma kange kasuwancin ƙasar da sauran ƙasashe. A ɗayan kuma, akwai ƙasashen da suka kasance cibiyar kasuwancin iskar gas da man da lran ke sanarwa, abin tambaya anan shi ne, ko ta ya ya wannan takunkumin zai shafe su? Ya ya  kuma ƙasashe ke kallon yadda Turkiyya ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe 8 da takunkumin ba zai shafa ba?

Lamarin sake kakkaɓawa lran takunkumi ya biyu bayan yadda gwamnatin Trump ke ganin cewa yarjejeniyar da aka yi da lran bai hanata gudanar da lamurkan makaman nukiliya ba. Ya dai kamata mu yi sharhi akan yadda baya ga Amurka sauran ƙasashen da aka yi yarjejeniyar dasu da suka haɗa da China, Faransa, Rasha, lngila da Jamus keda zummar ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Tabbas, duk da kasancewar matakin nada fuskar siyasa bai sanya da yawan kanfanonin ƙasa da ƙasa rashin yin ko oho ba da lamarin. Jim kaɗan bayan bayyanar da saka takunkumi da yawan kanfunan ƙasashen da suke ci gaba da mutunta yarjejeniyar sun fice daga kasuwar ƙasar lran. Hakan na nuni da  matsayar lran ta fuskar diflomasiyya a duniya nada bambanci da matsayin da take dashi a tsakanin kanfunan  masu zaman kansu.

ldan muka duba zamu ga cewa tun daga ranar 7 ga watan Agusta da aka ɗauki matakin sake kakkaɓawa lran takunkumi, gwamnatin lran ta haramta siyar zinari ko kasuwanci da dala hakan dai bai ƙara komai ba face ƙara katse kasuwancin ƙasa da ƙasa a ƙasar.

A halin yanzu dai an tabbatar da sake kakkaɓawa ƙasar takunkumi karo na biyu. Wannan matakin dai bai kasance ba face yunkurin ƙara rage ƙarfin tattalin arzikin kasar lran, haka kuma zai rage yawan kuɗaɗen shigar ƙasar da kuma kasancewa babban ƙalubale ga harkokin sufurin jiragen ruwa a kasar.

lran wacce take ɗaya daga cikin manyan ƙasashe dake da ɗimbin arzikin gas da man fetur, kasancewarta cikin wata matsala ka iya shafuwar lamurkan makamashin yankin baki ɗaya. Daga bisani kuma matsalar ka iya shafuwar kasuwar makamashin a duniya.

Ƙudaden dake shigowa ƙasar lran ta kasuwancin man fetur nada muhimmanci ga tattalin arzikin kasar. Za'a ma iya cewa lran na ɗaya daga cikin ƙasashen da tattalin arzikinsu ya dogara akan man fetur, sabili da haka ƙalubalantar sashen zai sanya ƙasar cikin wani irin hali.

Ya dai kamata mu dubi manyan dalilan da suka sanya Amurka ɗaukar irin wannan matakin akan lran. Da farko dai kasancewar lran mai dinbin arzikin man fetur da iskar gas kasace da zata iya kasancewa mai ƙarfi a yankunanta. Ƙarfin da zata samu tare da makaman nukiliya da take akai ka iya zama ƙalubale da barazana ga Amurka da ƙawayenta.

A ɗayan barayin kuma, kasancewar yadda lran ke ikon yankin Hurmuz da ake sufurin kaso 30 cikin ɗari a ake sarrafawa a duniya, na ƙara baiwa lran wata dama mai gwaɓi a harkokin hada-hadar duniya.

A ƙarshe dai, a ranar Litini zamu yi sharhi akan ƙasashe 8 haɗi da Turkiyya da aka bayyana cewar takunkumin ba zai shafesu ba. Ya dai kamata mu bayyana irin fa'idar afuwar da aka yi wa wasu ƙasashe da suka haɗa da Turkiyya dake gudanar da kasuwanci har na dala biliyan 10.6 da lran akan rashin shafuwarsu da takunkumin ba zai yi ba.

 Labarai masu alaka