Nazari da Binciken Kasashen Gabas Kan Gabashin Duniya

Kan wannan Maudu’i mun sake kasancewa tare da farfesa Kudret Bulbu Shugaban tsangayar nazarin Siyasa a Jami’ar Yildirim beyazit dake Ankara.

Nazari da Binciken Kasashen Gabas Kan Gabashin Duniya

Yadda masu bincike na yammacin duniya da ‘yan mulkin danniya suke kallon al’uma, siyasa, zamantakewa, Addini da yanayin rayuwar gabashin duniya, shi ake kira da Orientalism wato nazari kan gabashin Duniya ta kowanne fanni. Ba a wai ana kallon gabashin duniya daga sama ba ne, a a ana musu kallon kaskantattu marasa iko wanda hakan ke dauke da suffofi marasa kyau.

Aiyuka da rubuce-rubuce game da Orietalism ba su zama kamar yadda suke da ma’ana a duniyarmu ta yau ba. Amma kuma mafi yawan tunanin ya sauya sosai. Kamaryadda ake yi da fari, masu bincike na gabashin duniya, ba sa zuwa ga gabashin duniya su gane wa idanuwansu kafin yin wani rubutu na bincike. Saboda masu bincike na gabashin duniya suke kira da su je kasashensu na yamma su gabatar da makaloli.  

Hikayarmu ta bacin rai ta shekaru 200

Kusan shekaru 200 kasashe irinsu su Turkiyya da japan da sakafar Yammacin Duniya ta sha gabansu suke aika masu bincike, dalibai, kwararru da malaman jami’o’i zuwa  yammacin duniya. A yau ma kasashen Afirka, Asiya, Latin Amurka, Balkans, China da Indiya na amfani da irin wadannan hanyoyi. A wadannan kasashe ba wai daga jami’o’İ kawai ne ake aika mutane zuwa Yammacin duniya ba, a har daga ma’aikatun gwamnati, hukumomi da masana’antu. Su je su ga me Yamma take da shi, wanne irin tsari take a kai, sanna su dakko abin ci gaba da za su iya dauka zuwa kasashensu. Kasashe na kashe kudade da yawa wajen ganin sun tabbatar da wannan manufa tasu. To shin suna cimma wannan manufa kuwa? A loakc,inda tsawon shekaru 200 ake ci gaba da aika mutane zuwa Yammacin Duniya, abin kamar ba haka ba ne. Tsawon shekaru ‘yan jami’a na Japan sun dauki dabaru da fasahar kere-kere zuwa kasashensu, amma namu mutanen saisuka zama mawaka tare da dawowa gida. Wakar Sezai Karakoc mai ‘ya’ya 7 ta ba mu bayani game da zuwa Yamma da dawowa.

Tafiya yamma da yi wa kasarsa aiki

Abu ne mai ban takaici da bacin rai yadda ake tura mutane zuwa Yammacin Duniya don su koyo su dawo su habaka kasarsu, amma sai masu binciken, malaman jami’ar, daliban da kwararrun da ake aikawa yamma su dawo babu komai. Jami’o’İn kasashen da suka tura su, hukumomin gwamnati idan suka ce a yi wani dan karamin bincike to za a tabbatar da hakan.

Yawanci masu bincike, dalibai, ma’aikatan gwamnati da kwararru dake barin wasu kasashe su tafi yammacin duniya, idan sun je suna yi aiyuka ne game da kasashensu ba wai game da kasashen da suka je ba. Ina matukar bakin ciki idan na ga wannan abu a duk lokacinda da na hadu da wani da ya je kasar Yamma ko wanda ya dawo daga Yammacin duniya zuwa Turkiyya.

Saboda kasarsa ba don Yamma ba, don yamma don zama Kwararren Turkiyya

Al’umun da ba na yamma ba kuma suka je yammacin duniya da manufar neman ilimi, suna samun sakamako wanda mafi yawan ba shi kasashensu suke so ba. Hakan ya sanya wadannan kasashe na kai arzkinsu da kansu zuwa Yammacin Duniya. Masu zuwa ba wai suna daukar batutuwa da suka shafi yammacin Duniya ba ne, yadda suke zuwa su y, bincik kan abubuwanda Yamma take so, zai rufe hanyoyin amfanar da kasashensu bayan sun dawo gida. Suna zama kwararru a kan abubuwan da Yamma ke bukata ne ba wai wanda Kasashensu suke bukata ba. Idan za a bayar da misali a Turkiyya, za a ga cewar duk da tun shekaru 200 muke aika mutane zuwa yammacin Duniya, amma ba mu da kwararru kamar na kasashe irinsu Faransa da Jamus. Kuma za a ga cewa, wadanda suke karatu da kudin Turkiyya a kasashen Yamma suna zama kwararru game da Turkiyya din ba wai Yammacin duniya ba. A lokacinda yake da wahala a samu kwararru game da Yammacin Duniya, amma ana ganin yadda a Rediyo, Talabijin da Yanar Gizo ake da kwararru kan Turkiyya a yammacin duniya.

A lokacinda mutanen da suka je kasashen Yamma don bincike amma kuma suka karkata kan zamantakewa, harkokin rayuwa, take hakkin dan adam, nuna wariya da bamnaci tsakanin kabilu da ake da shi a kasashensu, to su sani ba wai kasasensu suke amfanarwa ba, suna amfanar da Yammacin duniyar ne. Saboda ga mutumin Yammacin duniya ya koyi wani yare tare da gudanar da bincike a cikinsa, hakan zai masa wahala da kashe kudi sosai. Amma ga shi a bagas ana yi masa binciken. Amma idan wani ya je yamma da kudin kasarsa tare da bincike kan wani batu da ya shai yammacin duniya kuma ta mahangar kasarsa, to kudin da za a kashe da lokaci a bayyane suke karara. A ce wani mutum ya dauki kudin kasarsa ya tafi Yammacin Duniya tare da zama kwararre na kasarsa ba wai na yamma ba, to hakan ya zama bauta kenan.

Matsalar shin daga kasar da ak je ta ke farowa? A mako mai zuwa za mu kalli sakamakon yadda mutum da kansa yake bincike tare da mayar da kasarsa abin binciken Yammacin Duniya. Bari mu fadi cewar wannan matsala ko wani bangare nata na faruwa ne daga Yammacin Duniya.Labarai masu alaka