Rawar Da Aikin TurkAkim Zai Taka Wajen Zaman Turkiyya Cibiyar Makamashi ta Duniya

Mun sake kasancewa tare da Ferfesa Erdal Tanas KARAGOL daga sashen siyasa da tattalin arziki a jami'ar Yıldırım Beyazıt.

Rawar Da Aikin TurkAkim Zai Taka Wajen Zaman Turkiyya Cibiyar Makamashi ta Duniya

A farkon wannan makon shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sunka halarci taron shirin kammala kataɓaren shinfida bututun iskar gas a cikin teku  ta shekarar 2019  a birnin Istanbul. Wannan aikin bututun iskar gas a cikin teku ta Rasha da zata ratsa Turkiyya zuwa nahiyar Turai, zata inganta dangantakar Turkiyya da Rasha musamman a fannonin makamashi da tattalin arziki da ya kamata mu yi sharhi akai. A ɗayan barayin kuma bayyana soke shinfida bututun iskar gas na yamma sabili da matsalar siyasa dake tsakanin Rasha da Yukiren lamari ne da ka iya sauya lamurkan cinikin makamashi a yankin baki ɗaya. Wannan kataɓaren aikin da aka ƙaddamar wanda zai samar da iskar gas na mitakub biliyan 31.5 a shekara wacce ta ratsa ƙasar Turkiyya daga Rasha zata inganta lamurkan kasuwancin iskar gas a yankunan baki ɗaya.

Turkiyya na daɗa ƙara zama babbar cibiyar samar da iskar gas da ake bukata a fadin duniya, ƙasashe na ƙara daukar wasu matakan samawa kansu makamashin da suke buƙata a ko wacce rana. Kamar dai yadda samar da tsaro keda muhimmanci ga ƙasa haka samar da makamashi ma keda muhimmanci, a dalilin hakan ne ƙasashe ke ci gaba da ɗaukar matakan samar da tsaro ga hanyar da za'a sama musu iskar gas din da suke buƙata.

Sabili da rikicin siyasa tsakanin Rasha da Yukiren ya sanya dakatar da aikin shimfida bututun iskar gas na yammaci inda aka mayar da himma ga bututun da zai ratsa Turkiyya daga Rasha zuwa nahiyar Turai. Wannan layin bututun iskar gas din kasar Turkiyya zai sauya na yammaci da aka dakatar. Haƙikanin gaskiya wannan aikin zai samawa Turkiyya iyakacin makamashin da take buƙata da ma ga yankin baki ɗaya.

A yau dai an riga an kammala shinfida bututun iskar gas din a cikin ƙasar Turkiyya, bututun ya ratsa garuruwan Kirkale da Kıyıköy a ƙasar Turkiyya, ana dai tunanin kammala aikin da fara amfani dashi a cikin shekarar 2019.

Wannan kataɓaren aikin da zai samar da iskar gas na mitakub biliyan 31.5 zai amfanar da Turkiyya da kuma nahiyar Turai baki ɗaya. Daga ƙasar Turkiyya za'a rinƙa samawa ƙasashen nahiyar Turai makamashin.

Haka kuma lamari ne da zai samawa ƙasar Turkiyya dukkan yawan iskar gas da take buƙata, musamman a yankin Marmara dake da yawan kanfuna.

Muna sane da, wannan aikin zai fa'idanci dukkanin ƙasashe, masu samar da iskar gas din dama masu buƙata, bugu da kari zai ƙara inganta harkokin tattalin arziki, cinikin makamashi da hurɗa mai inganci dake tsakanin Turkiyya da Rasha.

A cikin wannan halin, za'a ci gaba da bunkasa lamurkan cinikin makamashi da bunƙasa kasuwanci a ko wacce rana. Akan hakan ana hasashen kasuwancin Turkiyya da Rasha zai habbaka da kusan dala biliyan 100 a nan zuwa gaba. Anan ya kamata mu tuna da yarjejeniyar da Turkiyya ta yi da Rasha domin samar da cibiyar makamashin nukiliya ta Akkuyu

A sanadiyar wannan aikin shimfida bututun iskar gas da ake daf da kammalawa, zai sanya Turkiyya ta zama wata cibiyar samar da iskar gas da kuma ci gaba da daidaita lamurkan makamashi a yankin baki ɗaya.Labarai masu alaka