Sabon Babi a Rayuwar Al’umar Turkmen dake Siriya

Mun sake kasancewa da sharhin da Dr Cemil Dogac Ipek malami a sashen nazarin kasa da kasa dake jami’ar Karatekin a nan Turkiyya.

Sabon Babi a Rayuwar Al’umar Turkmen dake Siriya

A ‘yan kwanakin da suka wuce al’umar Turkmen dake Siriya sun gabatar da wani babban taro a garin Coganbey.

A wannan makon a cikin shirin namu za mu duba wannan taro da kuma yadda ya shafi manufofin Turkiyya a kasashen ketare.Al’umar Turkmen dake Siriya wadanda tun shekarar 2011 suka fara gwagwarmayar neman ‘yanci da girma sun kai wani mataki a yau. Al’umar Turkmen dake Siriya sun zama daya daga cikin masu taka rawa wajen tafiyar da al’umar da karfin ikon soji a Siriya ko ma a ce a Gabas ta Tsakiya baki daya. A yau Majalisar Wakilan Turkmen dake Siriya wadda take kare manufofinta na siyasa da diplomasiyya na ci gaba da gwagwarmaya kare al’umarsu tare da tabbatar sun samu tsaro.

A gwagwarmayar da jama’ar Turkmen ke ci gaba da yi suna son tabbatar da ganin cewar sabon kundin tsarin mulkin da za a rubuta a Siriya ya san da su, ya bayyana su waye su, ya bayar da kariya gare su tare da tsare mutunci da martabar kasar Siriya baki daya. Ina tunanin a wannan gabar za a bayyana al’ymar na Turkmen a kundin tsarin mulkin a matsayin “Al’umar da aka samarwa da tsaro”

A kokarin ganin sun cimma wannan buri nasu, al’umar Turkmen sun bayyana cewar a  shirye suke a nan gaba su zauna da kowanne bangare don tattanawa tare da samar da zaman şlafiya mai dorewa a Siriya. Babban abinda jama’ar Turkmen suka fi damuwa da shi kan wannan batu shi ne, kar su zama a sahu daya da ‘yan ta’addar dake yi wa Siriya da Turkiyya barazana. Wannan mataki na bayyana cewar ba daidai ba ne a dukkan wasu taruka da za a yi a Siriya a gayyaci kungiyoyin ta’adda masu alaka da wani addini ko yare ba. Al’umar Turkmen sun ce, ba za su taba amincewa da duk wani yunkuri na raba kasa ko samar da wani yanki a cikin Siriya ba. Wannan mataki ne mai kyau da suka dauka. Saboda haka an ga irin tasiri mara kyau da duk wani yunkuri na ba wa wasu ‘yancin Tarayya ko zaman kansa a Iraki. Wannan ne babban dalilin da ya fito da kungiyar ta’adda ta Daesh a Iraki. Al’umar Turkmen ba sa neman wani ‘yancin kafa kasa ko zama yankn Tarayya saboda hakan mataki ne raba Siriya. Su kawai suna son a samar da tsari guda day da zai kare hakki da martabar kowa a kasar.

A gefe guda kuma, rayuwa na ci gaba da tafiya yadda ya kamata a yanunan da Turkiyya da kubutar daga hannun ‘yan ta’adda. Kungiyoyin fararen hula na kara girma da habaka. Mun ga misalin hakan a kwanakin da suka wuce. Jama’ar Turkmen dake Siriya, sun gabatar da wani babban taron tabbatar da shugabancin majalisarsu a garin Coganbey. A yayin taron an samu halartar ‘yan Turkmen da suke rayuwa a yankunan Aleppo, Idlib, Bayır-Bucak, Rakka, Hama, Homs, Tartus, Dera, Golan da Sham.

Jama’ar Turkmen da suke cikin ‘yan adawar Siriya na amfani da tutoci daban-daban tsawon wani lokaci. Sun kasance suna shiga kunigiyoyi da dama donsu samu wakilci a cikin ‘yan adawar Siriya. Kungiyar Majalisar Turkmen ta dauki matakin gabatar da babban taron ne don ganin sun cimma wannan manufa ta hanyar demokradiyya.

A wajen taron mambobin Majalisar Turkmen; Shugabannin jama’ar Turkmen masu fada a ji; Kwamandojin Sojin Turkmen; ShugabanninKungiyoyin Fararen Hula na Turkmen da ma mazauna yankunansu daban-daban ne sula samu damar halarta.

Bayan an jefa kuri’a tsakanin zabar tutoci tara, sai aka amince da tsayar da tutar jama’ar Turkmen. A jikin tutar akwai kalar Shudi dake nufin Turkiyya, akwai ja dake nufin jinin Shahidai sai farin launi dake nufi da darajojin dan adam na duniya. Wata da tauraron dake jikin tutar kuma na nufin Musulunci. Wannan taro na nufin zaman lafiya a yankin kuma ana sa ran cewar albarkacinsa jama’ar Turkmen da dama za su koma gidajensu daga Turkiyya.

Al’umar Turkmen da suke a Siriya tun karni na 7 na ci gaba da rayuwarsu a kasar. Turkmen sun yadu sosai a yankunan Siriya da dama. Aleppo, Lazkiye, Idlib, Bayirbucak, Homas, Hama, tartus, Rakka, Dera, Sham da Golan na da jama’ar Turkmen da yawa a cikinsu. Turkmen na gwagwarmayar kare marataba da matsayinsu a kasar da suke rayuwa tsawon daruruwan shekaru a cikinta.

Tsawon shekaru daruruwa a Siriya, al’umar Turkmen na zama wata al’uma daban. Akwai jama’ar Tuekmen kusan miliyan 1.5 da suke magana da yaren Turkanci a Siriya.Idan aka hada da Turkmen da suka manta da Turkanci to akwai su sun kai miliyan 3.

Al’umar Turkmen dake Siriya su ne kabila ta biyu mafi girma da yawa bayan Larabawa. Sannan kuma a lokatuan da suka wuce sun fi kowa cutuwa a kasar Siriya. Al’uma ce da ba ta taba shiga wata kungiyar ta’adda ba kokuma zama mai nuna wariyar harshe a kasar, kuma a yau tana ta gwagwarmayar kare ‘yancinta da kanta.

A yau a matakin da muka zo, idan aka ba wa jama’ar Turkmen cikaken hakkinsu ba tare da tauyewa a Siriya, to hakan zai zama wani babban matakan zamar da zaman lafiya. Dadin dadawa, jama’ar Turkmen za su saukaka alakar Turkiyya da ma duniyar Turkiyya a sabuwar Siriya mai demokradiyya da ake shirin samarwa a nan gaba.Labarai masu alaka