Muhimman Sabbin Matakai a Masana'antun Tsaro na Turkiyya

Game da wannan batu mun sake kasancewa da sharhin da Shugaban Kungiyar Kwadago a Bangaren Samar da Kayan Yaki ta Turkiyya Turkan Zengin ya yi mana.

Muhimman Sabbin Matakai a Masana'antun Tsaro na Turkiyya

A masana’antun tsaro na Turkiyya ana daukar muhimman matakai daya bayan daya. A kowanne wata sai an samu wani sabon matakin ci gaba da aka dauka. Ana ta gwada sabbin kayan tsaro cikin nasara a kasar. Haka zalika ana kuma sanya hannu kan wasu muhimman aiyukan da take gudanarwa. A kwanaki 10 na farkon watan Nuwamban da muke ciki, mun shaida aiyukan tsaro da dama da aka yi.

A ranar 1 ga watan Nuwamban 2018 Hukumar TUKITAK karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan ta yi gwajin layin dogo na TUBITAK SAGE (HABRAS). An yi gwajin PULAT mai yin barna inda aka samuna nasarar gwada aikin Ishin. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a yayin bikin Cigaban Fasahar kere-Kere ya bayar da busharori da dama game da wadannan gwaje-gwaje da aka yi cikin nasara.

A ranar 4 ga watan Nuwamba an mika jirgin ruwa na uku samfurin TCG Burgazada F-513  ga rundunar sojin ruwan Turkiyya. A ranar 8 ga Nuwamba 2018 an Hukumar Cigaban masana’antun Kayan Tsaro (SSB) ta sanya hannu kan yarjejeniyar samar da injin jirgin yaki na gida da za a samar samfurin (MMM).  A ranar 9 ga Nuwamba 2018 kuma an sanya hannu kan yarjejeniyar samar da tankokin yaki samfurin ALTAY wadanda za a mika su bayan watanni 18. Za a samar da tankokin har guda 250. Yadda a cikin kankanin lokaciaka gabatar da wadannan aiyuka na nuni da ir,n kokarin bangaren samar da kayan tsaro na Turkiyya ke da shi.

HABRAS, PULAT, Aikin Isin da SIPER

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya halarci Babban taron Cigaban Fasahar Sadarwa ta kasa inda ya shaida gwaji cikin nasara na abubuwa da aka iinda ya kuma bayar da busharori da yawa. A jwabinna Shugaba Erdogan ya ce, "A yau mun hadu a wannan wajen don gwajin aiyukan kayan tsaro na ksa da muka samar. Muna tabbatar da ana kashe dukan kudade da basira da fasahar da muke da ita a cikin gida. Tare da Fara aiki da HABRAS, masana’antun tsaornmu za su zama suna da abubuwanda wasu ‘yan kasadhe ne suke da su a duniya. Daya daga cikin sakamakon da wannan abu ya samar shi ne PULAT wanda ake samar da tsaro da shi. Wannan na samar da kyakkyawan tsaro da kayan aiki ta hanyar vayar da tankoki ga dakarunmu. Wani abu sabo da masana’antun tsarinmu suke samarwa ta hanyar amdani da fasahar cikin gid shi ne “Ishin” wannan wata fasaha ce ta amfani da hasken wuta. A nan gaba kadan za a fara amfani da wannan fasaha a jiragen sama na yaki da na ruwa.” A jawabin na Shugaba Erdogan ya kuma bayar da busaharar cewa an fara aikin samar da SIPER wannda kayan tsaro ne na sama mai nisan zangıo. Ya ce za a kammala aikin a shekarar 2021.

An samar da bigiren farko na jirgin Aydinreis mai kunna nutso

A karkashin aikin MILGEM, Turkiyya ta samar da jirgin ruwanta na yaki na farko a sansanin soji da ke Istanbul. A ranar 4 ga watan Nuwamba Shugaba Erdogan ya halarci bikin kaddamar da jirgin ruwan na 3 samfurin TCG Burgazada F-513 inda aka mika wa rundunar sojin ruwan Turkiyya shi nan take. Jirgin na da tsayin mita 99.5 da fadin mita 14.4. yana da nauyin tan dubu 2,400. Jirgi ne da zai iya tafitar kilomita dubu 6 da 485 kuma zai iya zama a cikin teku na kwanaki 10. Jirgin na da fasahar tsaro a sama, kan ruwa da karkashin teku.

A lokacinda ake bikin mika jirgin ruwan na Burgazada, Shugaba Erdogan ya ce, an samar da bigiren farko na samar da jirgin ruwan Aydinreis mai kunna nutso. Jirgin zai iya kunna nutse a teku ba tare da shan mai ba. Zai iya zuwa Ameri,ka ya dawo nan da nan. Sannan jirgin na da fasahar yadda zai dinga tafiya ba tare da fitar da wani sauti ba. Zai bayar da babbar gudunmowa ga dakarun ruwan Turkiyya wajen tabbatar da tsaro. Jirgin na karkashin teku na da tsayin mita 68, da fadin mita 13 sannan yana da nauyin tan dubu 1,850.

Shirin samar da injin jirgin saman yaki na cikin gida

Kamar yadda aka sani, ana ci gaba da aikin samar da jirgin yaki na cikin gida ga dakarun sojinm Turkiyya. Ana gabatar da wannan aikin a karkashin manufar rundunar sojin sama na samun jiragen yaki daga cikin gida nan shekarar 2030. A yanzu haka Hukumar masana’antun tsaro ta Turkiyya na aikin samar da injin wanna jirgi na musamman. A ranar 8 ga watan Nuwamba aka sanya hannu kan yarjejeniyar samar da wannan inji.a karkashin yarjejeniyar an amince da fara aikin nan da nan. Ana da manufar samar da jirgin da kayan cikin gida da fasahar Turkiyya. Aikin na kuma da manufar yadda babu wata kasa da ta taba samar da irin wannan inji na jirgi. Ana da manufar komai na jirgin da hakkin mallakarsa ya zama na Turkiyya ba tare da hannun wata kasar waje ba.

Samar da Motar Igwa mai suna Altay

Tsawon lokaci ana ci gaba da gabatar da aiyuka da nufin sbiyar bukatar sojojin kasa na Turkiyyainda ake kokarin samar da tankokin yaki na ALTAY. A ranar 9 ga watan Nuwamba aka sanya hannu kan yarjejeniyar samar da motocin yaki na Igwa samfurin ALTAY guda 250. Bayan watanni 18 za a mika wa dakarun kasa na Turkiyya wannan mota a karon farko.

A bayanan da aka fitar game da wannan mota ta yaki ta ALTAY, an bayyana irin siffofinta da yadda za ta yi aiki. Ita ce motar Igwa ta farko da Turkiyya za ta samar da kanta. Tana kuma da karfin harba bam daga cikinta. Tana da karfin tafiya inda za ta zama motar yaki mafi karfi da dakarun Turkiyya za su yi amfani da ita. Ana tsara motar da fasahar bayar da duk wata irin kariya da ake bukata. Tana da sulke, kuma za ta iya aiki a wajen da ake da barzanar Nukiliya ko Radioktif.Labarai masu alaka