Alkiblan dangantakar Turkiyya da Amurka a shekarar 2019

Abubuwan da suka faru a cikin makonni biyu da sunka gabata sun nuna cewa shekarar 2019 na tattare da dama da kuma ƙalubale ga dangantakar dake tsakanin Turkiyya da Amurka.

Alkiblan dangantakar Turkiyya da Amurka a shekarar 2019

Abubuwan da suka faru a cikin makonni biyu da sunka gabata sun nuna cewa shekarar 2019 na tattare da dama da kuma ƙalubale ga dangantakar dake tsakanin Turkiyya da Amurka. Idan muka dubi lamurkan makami kirar S400-F35 da kuma lamurkan ƙasar Siriya a cikin ƴan kwanakin nan zamu ga cewa ƙasashen biyu zasu kasance makusanta juna tare da ƙara yawan musayar bayanai a ƴan kwanakin dake gaba.

        Lamurkan da sunka faru a cikin shekaru huɗun da sunka gabata, musamman matsalar YPG sun haifar da hawa da sauka a dangantakar dake tsakanin Turkiyya da Amurka. Lamurkan da sunka faru a cikin shekaru huɗu wadanda sunka haifar da matsaloli a dangantakar kasashen biyu, sun dauki sabon salo a sanadiyar abubuwan da sunka faru a cikin makonni biyun da sunka gabata. Lamari na farko da zai taɓa dangantakar Turkiya da Amurka a shekarar 2019 shi ne lamarin makamin S400. Gwamnatin Amurka dai ta bayyana zata sayarwa Turkiyya da makamin mai tsarin Patriots a ɗan lokacin dake gaba. Haƙiƙa wannan lamarin na tattare da abubuwan da basu da tabbas. A lokacin da ma'aikatar harkokin waje ta fitar da wannan sanarwar, masu hannu da tsaki a ɓangarorin biyu sun yanke hukuncin za'a fara zaman cinikayya domin daidaitawa. Amma sai gashi babu tabbacin cewa ko Amurka zata sayarwa Turkiyya da wannan makamin na S400. Idan har Amurka ta bayyana cewar ba zata sayarwa Turkiyya da makamin S400 tsarin Patriots ba, ko shakka babu dangantakar ƙasashen biyu zata sake kasancewa cikin matsala. Bugu da ƙari, ldan har Amurka ta sake ɗaukar salon da ta ɗauka a lokacin da Turkiyya ta sayi makami kirar F35  akan makamin S400 dangantakar dake tsakanin kasashen zai sake ɗaukar sabon salo.

Baya ga lamarin S400 wasu lamurkan da zasu taɓa dangantakar ƙasashen biyu kuma su ne lamarin CAATSA a Amurka da kuma aikin samar da kamfanin tsaro da Turkiyya ta ƙulla da Rasha, musamman kasancewar yadda anka kakkaɓawa wasu daga cikin ƙasashen dake cikin haɗakar takunkumi.

Sabili da waɗannan lamurkan dangantakar kasashen biyu zata kasance cikin matsatsi a fannin samar da tsaro. Duk da dai Turkiyya ta bayyana matsayarta akan sayen makamin S400, kawo yanzu bata fahimci matsayar Amurka ba akan lamarin. Baya ga maslahar S400, wani muhimmin lamarin da Amurka ta fitar shi ne janye sojojinta daga ƙasar Siriya. Duk da dai wannan matakin ya samu karɓuwa a ƙasashen waje, wannan lamari ne da ya janyo wasu cikas a cikin ƙasar ta Amurka. Da farko dai baya ga ministan harkokin tsaron ƙasa Mattis, wakili na musamman akan yaƙi da DEASH McGurk ya yi murabus. Wannan muhimmin mataki da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya ɗauka ya haifar da wata dama da zai inganta dangantakar kasashen biyu. wato Turkiyya da Amurkan.

Bayan janyewar da Amurka zata yi daga Siriya, Turkiyya da Amurka zasu ƙulla wata haɗakar ci gaba da yaƙar kungiyar DEASH a yankin. Bayanan da shugaba Trump ya yaɗa a shafinsa ta twitter bayan tattaunawar shugabannin biyu ya nuna cewa Amurka zata bayarda gudunmowar kayyayakin sufuri da haddin gwiwa da Turkiyya domin kauda DEASH da kuma bin hanyar lumana domin warware matsalolin ƙasar Siriya. Wannan dai hanya ce da zata inganta dangantakar kasashen biyu ƙwaran gaske.

 

Sai dai, idan ba'a aiyanar da hurɗa mai kwari da kuma tabbatar da lamurkan da ake buƙata tare da Turkiyya a lokacin ƙaddamar da wannan matakin ba, hakan zai haifar da ƙalubale babba a dangantakar ƙasashen biyu. Duk da kasancewar dakarun ƙasashe masu ƙarfi a yankin na yankunan, kungiyoyin ta'addanci kuma na sheƙe ayarsu, lamarin dake dagule samar da lumana a yankin baki ɗaya. Hurɗar da Amurka ke yi da kungiyar ta'addar YPG babban lamari ne dake sanya ka-ce-na-ce tsakanin ƙasashen biyu, kuma lamari ne da zai iya ci gaba da gurɓata dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu. Kasancewar waɗannan ƙalubaloli dake fuskantar ƙasashen biyu, yana da kyau ƙasashen biyu su ƙulla zamantakewa mai kwari a matakan haɗin gwiwar da zasu ɗauka a yankin, a yayin hakan kuma, akwai bukatar su inganta tare da faɗaɗa lamurkan musayar bayanai a tsakaninsu.Labarai masu alaka