Aiyukan hukumomin kasar Turkiyya a kasashen ketare

A wannan shirin zamu rinka kawo muku sharhi akan hukumomin kasar Turkiyya dake gudanar da aiyuka daban-daban a fadin duniya

Aiyukan hukumomin kasar Turkiyya a kasashen ketare

Barkanmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirinmu mai taken “Hukumomin ci gaban Turkiyya.”

A wannan shirin zamu rinka kawo muku sharhi akan hukumomin kasar Turkiyya dake gudanar da aiyuka daban-daban a fadin duniya. Wadannan hukumomin sun hada da Hukumar Yunus Emre, Hukumar bayar da tallafin karatu ga daliban kasashen waje, Hukumar bayar da agajiin gaggawa ta kasar Turkiyya da kuma hukumar kula da bunkasar tattalin arzikin Turkiyya wato TIKA.

Da farko dai zamu fara da tarihin TIKA a yau daga bisani kuma mu zayyana ire-iren aiyukan da hukumar ke gudanarwa a fadin duniya.

An kafa hukumar TIKA ce a shekarar 1992 bayan kammala yakin cacar baki wato cold war da kuma rushewar daular Soviet a shekarar 1991. An dai kafa hukumar ne domin kulla karfafan zamantakewa da haddin gwaiwa da wasu yankuna da kuma wasu kasashe da kasar Turkiyya. 

TIKA wacce daga shekarar 1992 zuwa 2002 tanada ofis 12 tare da gudanar da aiyuka har 2500 a fadin duniya ta kasance wacce a ko wace rana tana ci gaba da bunkasa aiyukanta ba ja da baya. A yau dai TIKA nada ofisoshi 61 a kasashe 59 tare da gudanar da aiyuaka ire daban-daban a kasashe har 170. TIKA, wacce ke gudanar da muhimman aiyuka a kasashe da dama ta kasance wata gadar samar da zaman lafiya da Turkiyya ke amfani da ita a doron kasa.

TIKA, wacce shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyanata amtsayar “ hukumar da hannunta ya isa a ko ina, takan isa a guraren dake da matsala ta bayar da gudunmowa tare da warware matsalar a matsayar kasar Turkiyya”  TIKA zata ci gaba da kara yawan aiyuka da gudunmowar da take bayarwa a ko wacce shekara tare da kara fadada yankunan da take gudanar da aiyukanta. TIKA, a duk inda ta isa takan bayar da gudunmowa da tallafi tun daga fannin ilimi har izuwa fannin lafiya. Hakika tana ci gaba da bayar da tallafi ga ci gaban rayuwan al’umman tun daga haihuwa har mutuwa babu sashen da hannunta bai kai ba. Wadannan katabarorin aiyukan kungiyar zata ci gaba da habbakasu da kuma bunkasasu.Labarai masu alaka