An kashe yara kanana akalla dubu 1,400 a Yaman

Yara kanana akalla dubu 1,400 ne suka rasa rayukansu a kasar Yaman a cikin shekaru da suka gabata sakamakon rikici da mayakan Houthi, masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Yaman Ali Abdullah Salih da kuma mayakan gwamnatin kasar.

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, tun daga watan Maris din shekarar 2015 an jikkata yara kanana sama da dubu 2,400 a kasar ta Yaman.

Haka zalika akwai yara miliyan 7 a Yaman da ke bukatar a kula da lafiyarsu, inda wasu miliyan 14 ba sa samun tsafataccen ruwan sha.

Akwai kuma yara miliyan 1.7 da ba sa samun isasshen abinci.

A bangaren ilimi kuma an rushe makarantu sama da dubu 2 a kasar.Labarai masu alaka