Kenya ta haramta zanga zangar adawar siyasa a fadin kasar

Kenya ta haramta dukkan nau'in zanga-zangar adawar siyasa da aka kwashe kwanaki ana gudanarwa a fadin kasar.

Kenya ta haramta zanga zangar adawar siyasa a fadin kasar

Kenya ta haramta dukkan nau'in zanga-zangar adawar siyasa da aka kwashe kwanaki ana gudanarwa a fadin kasar.

An dai suma zanga-zangan ne bayan dantakaran shugaban kasa a jam'iyyar adawar kasar Raila Odinga ya bayyana janyewar shi daga shiga zaben da za'a sake, inda yake neman a canja tsarin zaben kasar.

A wannan dalilin ne magoya bayansa suka dinga gudanar da zanga-zangar kira ga gwamnatin kasar na ta sake tsarin zaben. Inda suke cewa bazasu yarda a gudanar da zabe idan ba^'a saurari korafin su ba.

Hukumar 'yan sandar kasar tace zanga-zangar ka iya jefa kasar cikin halin kakanikayi saboda haka ya zama wajibi a haramtashi. Labarai masu alaka