Isra'ila ta ce ba za ta karbi Mambobin Majalisar Tarayyar Turai da suke shirin ziyartar kasar ba

Isra'ila ta sanar da cewa, ba za ta karbi Mambobin Majalisar Tarayyar Turai da suke shirin ziyartar kasar a mako mai zuwa ba.

Ma'aikatar harkokin cikin Gida ta Isra'ila ta ce, ba za a bayar da izinin shiga kasar ba ga wasu mutane 20 Mambobin Majalisar Tarayyar Turai ba.

Ma'aikatar ta ce, dalilin daukar wannan mataki shi ne yadda mutanen suka goyi bayan juya wa Isra'ila baya da kaurace wa kayanta.

A watan Maris ne Majalisar Dokokin Isra'ila ta samar da wata doka da ta hana bayar da izinin shiga kasar ga duk mutanen da suka goyi bayan juya mata baya.

A shekarar 2005 ne aka kirkiri "Gwagwarmayar Juyawa Isra'ila baya" wadda kuma har yanzu ake ci gaba inda ake neman Isra'ila ta bar yankunan da ta yi kaka gida tare da mamaye wa, sannan kuma Larabawa Falasdinawa su koma kasarsu.Labarai masu alaka