Saudiyya ta ce za ta yi hukunci na adalci ga Yarimomi da Manyan 'Yan kasuwa da ta kama

Wakilin Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya Abdallah Al-Mu'allimi ya shaida cewa, za a yi hukunci na adalci a gaban kotu ga Yarimomi da Manyan 'Yan Kasuwa da Jami'an gwamnatin kasar da aka kama bisa zargin Cin hanci da Rashawa.

A yayin taron menama labarai da Al-Mu'allimi ya gudanar a zauren majalisar ya yi bayan game da batutuwan kasashen Yaman da Labanan da kuma kamun da aka yi wa manyan mutane a kasarsa.

Da ya ke bayani game da kamun, Al-Mu'allim ya ce, zai iya tabbatar da cewa, za ayi wa mutanen Shari'a bisa adalci.

Ya kuma kare wanzuwar Saudiyya a Yaman inda ya ce, kasarsa ba ta saka takunkumi ba ko kuma yin kawanya ga Yaman din.Ya ce, sun dauki matakin wucin gadi wajen rufe wasu iyakokinsu na sama da na ruwa ga Yaman saboda harba makamai masu linzami zuwa Riyadh da ake yi.

Ya ce, a cikin awanni 24 za a bude tashoshin jiragen ruwan da aka rufe. Kuma akwai bukatar kara tsaurara tsaro a wuraren da 'yan tawayen Houthi suke rike da iko da su musamman tashar jiragen ruwan Hudeyde.

Al-Mu'allim ya kara da cewa, ba za a bude tashar jiragen ruwan hudeyde ba, inda ya zargi kayan da ake wuce wa da su da cewa, makamai ne akae sayarwa da 'yan tawayen Houthi ta barauniyar hanya.Labarai masu alaka