Shugaban Kasar Uganda na son dawwama a kan mulki

Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da kasancewa a kan mulki bayan ya cika shekaru 75 inda ya fara yunkurin sauya kundin tsarin mulkin kasar.

A yayin wani taro da aka yi a fadar shugaban kasar na Uganda Museveni ya shaida wa lauyoyi da 'yan majalisar dokoki cewa, kasashe da dama da suka samu canji tare da ci gaba na karkashin shugabanni masu shekaru da yawa.

Lauyoyi da 'yan majalisar dai na duba yiyuwar sauya dokar da ta kayyade shekarun zama shugaban kasa a Uganda.

Museveni ya bayyana Tunisiya a matsayin misali.

Shugaban ya hau mulki tun shekarar 1986 wato shekaru 31 da suka shude kuma a shekarar 2021 da za a sake zaben shugaban kasar zai cika shekaru 75 da haihuwa.Labarai masu alaka