• Bidiyo

Kudus: Hukumar Kula da Alamuran Addinai ta Turkiyya ta soki Donald Trump

Hukumar Kula da Al'amuran Addinai ta Turkiyya Diyanet ta bayyana matakin ayyana Kudus da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi a matsayin abu da ba za a amince da shi ba, abun bakin ciki da kuma lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban Hukumar Farfesa Ali Erbash ya bayyana cewa, Kudus waje da ya ke Mallakin dukkan Msulman Duniya.

A sanarwar da Shugaban na Diyanet ya fitar ya ce "Kudus ba wani bangare ne na wata kasa ba ko al'uma. Wannan mataki ya saba wa tunani mai kyau tare da lalata kwakwalwar dan adam. Wannan mataki ne da ya ke tafiyar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Gian zaman lafiya na nema ya koma gidan rikici sakamakon daukar wannan mataki."

Erbash ya kara da cewa, matsayin Kudus ba na siyasa ba ne kawai.

 Labarai masu alaka