Amurka za ta sake duba yarjejeniyar nukiliyar Iran

Amurka za ta yanke hukunci akan ko yarjejeniyar da ta ratabawa hannu da Iran akan makaman nukiliya zai ci gaba.

Amurka za ta sake duba yarjejeniyar nukiliyar Iran

Amurka za ta yanke hukunci akan ko yarjejeniyar da ta ratabawa hannu da Iran akan makaman nukiliya zai ci gaba.

Sakataren ma'aikatar wajen Amurka Steve Golstein a lokacin da aka tambayeshi ko Amurka za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta yi da Iran, ya bada amsa da cewa: 

"Za'a tattauna akan lamarin, kuma za'a dauki matakin daya dace"

Goldstein ya tabbatar da cewa shugaba Donald Trump zai gana da sakataren harkokin wajen Amurkan Rex Tillerson da ministan tsaron kasar Jim Mattis a cikin wannan makon inda za su yanke hukunci akan lamarin.

Tillerson, a baya ya shaidawa kanfanin dillancin labaren AP da cewa ko dai ayiwa yarjejeniyar kwaskwarima ko kuma a soke yarjejeniyar baki daya.

 Labarai masu alaka