Trump ya sake tafka abin kunya

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya sake tafka abin kunya a lokacin da ya ke gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Norway Erna Solberg a Fadar White House da ke Washington.

Kalaman na Trump sun ba wa kowa mamakin inda ya ce a watan Nuwamba suka fara mika wa Norway jiragen yaki na F-52 da F-35, sai hakan ya sa ake ta cece-kucen me Trump ya ke nufi da wannan kalami nasa.

Babban abun kunyar shi ne yadda Amurka ba ta kera wani jirgi samfurin F-52 amma kuma a watan Nuwamba ta sayarwa da Norway jiragen yaki na F-35.

Da ya fahimci ya yi kuskure sai ya waske tare da cewa, sun sayar wa da Norway F-35 guda 52 kan kudi har dalar Amurka biliyan 10.

Wannan abu ya sanya ana ta zolayar Trump a shafin Twitter.

Ba wannan ne dai karo na farko a Trump ya ke aikata abin kunya ba a yayin kalamansa.

Tag: Norway , Kunya , Trump

Labarai masu alaka