Trump ya yi amai ya lashe game da Koriya ta Arewa

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi amai yalashe game da matakin da zai dauka kan Koriya ta Arewa da kuma yarjejeniyar Saurin Yanayi ta Faransa.

Trump ya yi amai ya lashe game da Koriya ta Arewa

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi amai yalashe game da matakin da zai dauka kan Koriya ta Arewa da kuma yarjejeniyar Saurin Yanayi ta Faransa.

A baya dai trump ya ce, a shirye ya ke da ya shafe Koriya ta Arewa daga ban kasa, amma a yanzu ya ce, kofarsu ta tattaunawa a bude ta ke.

Trump ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in.

A yayin tattaunawar Trump ya ce, a lokacin da ya dace kuma akarkashin sharudda nagartattu zai iya tattaunawa da Koriya ta Arewa.

Trump ya kuma yi ishara da cewa, akwai yiwuwar ya janye ra'ayinsa game da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Faransa wadda ya ce Amurka ta fita daga ciki a shekarar da ta gabata.

A lokacinda ya bayyana fitar su daga yarjejeniyar, Trump ya ce, yarjejeniyar na da illa ga tattalin arzikin Amurka.Labarai masu alaka