An yanke wa Shugaban Kungiyar Hadin Kan Malaman Musulunci hukuncin daurin rai da rai

Kotun soji a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Babban Malami kuma Shugaban Kungiyar Hadin malaman Musulunci ta Duniya Yusuf Alkaradawi.

An yanke wa Shugaban Kungiyar Hadin Kan Malaman Musulunci hukuncin daurin rai da rai

Kotun soji a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Babban Malami kuma SHugaban Kungiyar Hadin malaman Musulunci ta Duniya Yusuf Alkaradawi.

Kotun ta yankemasa wannan hukunci tare da wasu mutane 17 da aka tuhuma da yunkurin kashe Kanal Wa'il Tahun a birnin Alkahira a shekarar 2015.

An yane wa Karadawi hukuncin bisa tuhumarsa da yunkurin kisan kai, tunzura jama'a da kuma yada labaran karya.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 26 ga wasu mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi da suka hada da Abdurrahman el-Berr, Mahmud Gazlan, Taha Vahdan da Said Uleyva. 

An kuma janye karar mamban kungiyar Muhammad Kamal sakamakon mutuwa da ya yi.Labarai masu alaka