Firaministan Isra'ila Netanyahu ya shiga tsaka mai wuya

'Yan sandan Isra'ila sun kammala binciken da suka fara game da zargin cin hani da ake yi wa Firaministan Kasar benjamin Netanyahu.

Firaministan Isra'ila Netanyahu ya shiga tsaka mai wuya

'Yan sandan Isra'ila sun kammala binciken da suka fara game da zargin cin hani da ake yi wa Firaministan Kasar benjamin Netanyahu.

Sanarwar da 'yan sandan Isra'ila suka fitar ta ce, a binciken daka yi wa Firaministan an same shi da laifukan cin hanci da rashawa.

'Yan sandan sun shawarci lauyoyin gwamnati da su shirya takardun tuhuma ga Netanyahu bisa aikata laifukan cin hanci da rashawa da kuma amfani da ofishinsa ta mummunar hanya.

Ana bayyana cewa, idan aka tabbatar da Netanyahu ya aikata cin hanci to zai yi murabus daga kujerarsa.Labarai masu alaka