• Bidiyo

China ta karyata wai za ta gina sansanin soja a Afganistan

Majalisar tsaron kasar Afganistan ta musunta labarin dake cewa kasar da hadin gwiwar China za ta gina sansanin soja a jihar Badhshan a iyakokin Tajikistan.

Kamar yadda majalisar ta sanar " Bazai taba yiwu ba kasar Afganistan ta kulla wa ta yarjejeniyar soja da kasar waje ba tare da amincewar shugaban kasa, majalisar tsaro da majalisar dokokin kasar ba"

A inda suka kara da cewa babu zancen kasancewar sojojin China a kasar Afganistan.

A watan Janairu ne aka yada cewa hukumomin Beijin da Kabul zasu gina sansanin soja a jihar Badhshan dake kusa da Tajikistan.

Ma'aikatan tsaron kasar China ma ta karyata wannan labarin kamar yadda ministan tsaron kasar Wu Qian ya bayyana cewar ba gaskiya bane wai China za ta gina sansanin soja a Afganistan.

 Labarai masu alaka