Za'a kafa kwamitoci uku domin duba matsalolin dake tsakanin Turkiyya da Amurka

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya Hami Aksoy ya bayyana cewar za'a kafa kwamiti uku domin duba matsalolin da suka ki ci suka cinyawa tsakanin Turkiyya da Amurka.

Za'a kafa kwamitoci uku domin duba matsalolin dake tsakanin Turkiyya da Amurka

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya Hami Aksoy ya bayyana cewar za'a kafa kwamiti uku domin duba matsalolin da suka ki ci suka cinyawa tsakanin Turkiyya da Amurka.

Hami Aksoy ya ƙara da cewa za'a fara taron duba lamurkan da samar da sabbin tsarukan aiki ne da aka aminta akai bayan ziyarar da ministan harkokin wajen Amurka ya kawo Turkiyya. Ministan harkokin wajen Amurka Rex Tillerson zai jagoranci kaddamar da taron a Washington yayinda takwaransa na Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu zai jagoranci taron a  Ankara.

Za'a dai fara wannan taro ne nan bada jimawa ba, da kwamiti na farko zai tattunawa akan lamurkan kungiyar FETO da maslahar ofisoshi jakadanci.

Kwamiti na biyu kuwa zai tatauna akan lamarin ta'addanci a Siriya da kuma barayin 'yan ta'addar PKK watau YPG dake yankin Menbich.

Kwamitin na uku kuwa zai duba yakin da akeyi da 'yan ta'addar PKK ne.

Kwamitocin za su kunshi ma'aikatar ma'aikatan tsaro, harkokin cikin gida, leken asiri, shari'a da sojoji.

Aksoy ya bayyna cewar ana fatar tarukan su haifar da da mai ido. A yayinda aka tambayeshi ko ministan tsaron Amurkan ya amince da cewa kungiyar PYD barayin PKK ne? Ya kada baki ya ce: dayawan mutanen Amurka sun amince da cewa kungiyar PKK nada hurda da PYD.

Kakaki Aksoy, ya kara da cewa a niyyar ci gaban taron Sochi kashi na farko da shugabanin kasar Turkiyya Tayyip Erdoğan, na Rasha Vladimir Putin da na  İran Hasan Ruhani suka gudanar a ranar 22 ga watan Nuwamba za'a gudanar da na biyunsa a watan Afirulu a kasar Turkiyya, kafin hakan ministocin harkokin wajen kasashen za su gana a Astana a ranar 16 ga watan Maris.

 Labarai masu alaka