Najeriya ta goyi bayan mayar da ofishin Jakadancin Amurka zuwa Birnin Kudus

Kafafan yada labarai da suka je Kudus sun fitar da jerin sunayen kasashen duniya da suka hada da Najeriya wadanda suka halarci bikin mayar da ofishin jakadancin Amurka da ke Tel Aviv zuwa Birnin Kudus. Amma daga baya Aljazeera ta janye sunan Najeriya.

A jerin sunayen kasashen da tashar Aljazeera sashen Turanci suka fitar ta nuna akwai kasashen duniya 32 da suka tura wakilansu zuwa wajen bude ofishin.

An bayyana Kasashen kamar haka: 

Albaniya, Angola,Ostiriya, Kamaru, Kongo, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Ivory Coast, Jamhuriyar Chek, Jamhuriyar Dominican, El Salvador, Itopiya, Jojiya, Guatemala, Honduras, Hungary, Kenya, Myanmar, Makedoniya, Panama, Peru, Filifins, Romaniya, Ruwanda, Sabiya, Sudan ta Kudu, Tailan, Yukren, Vietnam, Paraguay, Tanzaniya da Zambiya.

An kashe mutane kusan 60 a rikicin da ya barke tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ila a lokacin da Amurka ke bikin mayar da ofishin jakadancinta a Isra'ila zuwa birnin Kudus.

Turkiyya ita ce kasa kan gaba wajen nuna adawa da wannan mataki da Amurka ta dauka wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.Labarai masu alaka