Netanyahu: Kudus zai zama Babban Birnin Isra'İla ba tare da wasu sharuddan zaman lafiya ba

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, Kudus zai zama Babban Birnin Isra'İla ba tare da wasu sharuddan zaman lafiya ba.

Netanyahu ya halarci taron Gala da aka shirya don murnar mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Kudus daga Tel Aviv.

A jawabin da netanyahu ya yi ya gode wa shugaban Amurka DOnald Trump bisa wannan mataki da ya dauka inda ya nuna yadda alakar Amurka da Isra'ila ta yi karfin da ba ta taba yi ba.

Netanyahu ya kuma yi kira ga sauran kasashen duniya da su mayar da nasu ofisoshin Jakadancin zuwa Kudus.

Ya ce, kudus birnin yahudawa ne tun dubunnan shekaru da suka wuce.

Netanyahu ya sake jaddada gamsuwarsu kan fitar Amurka daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran da aka kulla a 2015.Labarai masu alaka