Koriya ta Arewa ta yi barazanar soke ganawar da shugabanta zai yi da Trump

Koriya ta Arewa ta sa kafar hagu ta yi watsi da taron kolin da yakamata ta gudanar da Koriya ta Kudu, a yayinda kuma ta yi barazanar za ta soke ganawar da shugaba Kim Jong-un zai yi da shugaban kasar Amurka Donald Trump.

Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya rawaito cewa Koriya ta Arewa ta soke ganawar da ya kamata ta yi da Koriya ta Kudu a ranar Laraba tare da kuma yin barazanar janyewa daga ganawar da aka shirya tsakanin Kim da Trump a kasar Singapore a watan gobe.

Hakan dai ya biyu bayan wata atasayen sojoji da sojojin Koriya ta Kudu suka gudanar da hadin gwiwar sojojin Amurka a yankin lamarin da baiwa Pyongyang dadi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa KCNA ya rawaito cewa ya kamata Amurka ta yi taka tsantsan akan ganawar shugabanin biyu, domin wannan atasayen sojojin da ake gudanarwa ka iya kange aiyanar da taron.Labarai masu alaka