Saudiyya ta kai Iran kara a zauren Majalisar Dinkin Duniya

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya bayyana cewa, kasar ta kai karar Iran zauren Majalisar Dinkin Duniya sakamakon karya dokar shiga yankunanta da suke teku masu albarkacin man fetur.

A shekarar 1968 ne Iran da Saudiyya suka sanya hannu tare da fitar da iyakokinsu a tekun Basra inda suka amince da kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu.

Wakilin Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya Abdullah bin Yahya Al-Mu'allim ya ja hankalin zauren majalisar da cewa, duk da mika wa Sakatare Janar Antonio Guterres korafinsu amma Iran na ci gaba da shiga iyakarsu a teku wadda ta saba wa yarjejeniyar da suka yi.

Mu'allim ya ce, an dauki matakan rigakafi da suka kamata kuma duk wata matsala da aka samu laifin gwamnatin Iran ne.

Har yanzu Iran ba ta ce komai kan wannan batu ba.Labarai masu alaka