Kasar da aka nufa ita ce Iran

Ƙalubalantar da Amurka ta yi wa  lamurkan makaman nukiliyar kasar Iran a lokacin mulkin Ahmedinejad ya janyo cikas ga harkokin tattalin arzikin ƙasar.

Kasar da aka nufa ita ce Iran

A shekarar 2013 lokacin da aka zaɓi shugaba Hasan Ruhani mai sassaucin ra'ayi, al'umar ƙasar lran sun kasance cikin masu fatan samun sauyi mai inganci. Yarjejeniyar da Ruhani ya aiyanar tare da ƙasashen P5+1 ya haifar da janye takunkumin da aka kakkaɓawa ƙasar ganin yadda ta amince da ta ja baya daga harkokin makaman nukiliya. Wannan matakin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta jagoranta ya sakewa tattalin arzikin kasar lran mara a wannan lokaci. Sai dai bayan hawa kan karagar mulki da Donald Trump ya yi a Amurka tattalin arzikin kasar lran ya sake kasancewa cikin ƙalubale musamman bayan janyewar da Amurka ta yi ita tilo daga yarjejeniyar lran a ranar 8 ga watan Mayis ɗin shekarar 2018.

Haƙiƙa, janyewar da  Amurka ta yi daga yarjejeniyar lran ya haifar da matsalolin tattalin arziki ga kasar ta lran. Duk da matakan da lran ta dauka na yanke karancin yadda za'a rinka canja kundin ta da dala a riyal dubu 42, dalar Amurkan na ci gaba da hauhawa a ƙasar.  Faɗuwar darajar riyal din ƙasar lran da ya soma a watan Janairu, a halin yanzu darajar ta zube har na yawan kaso 150 cikin ɗari. A yayinda a watan Janairun 2018 ake canja dalar Amurka ɗaya da riyal din lran dubu 44 , a cikin ƴan kwanakin nan ya taɓa haura riyal dubu 110.

Kafin sake kakkaɓawa lran takunkumi, tattalin arzikin kasar ya ɗan yi tagomashi , lamarin da ya sauya bayan sake aiyanar da takunkumin. Bayan zuwan shugaba Trump kan karagar mulki da kuma canjin mulki da aka samu a ƙasar lran. Ƙasar ta ja baya daga harkokin yaɗa manufofin ta a gabas ta tsakiya. Haka kuma matakan da Amurka da lsra'ila suka dauka domin kange Iran daga yaɗa manufofin ta a yankin gulf bayyane suke. Waɗannan matakan dai sun takurawa lran inda ta rage bada tallafi ga wakilanta dake kasashen yankin.

Takunkumin da Amurka ta sake kakkaɓawa lran ya kunshi na daloli, zinari da sauran ma'adanai da suke gudanar da kasuwanci dasu. Duk da takunkumin ba zai kunshi jiragen sama da kayyakinsu ba, zai haɗa da motoci, musamman manyan motoci. Bayan sake kakkaɓawa lran takunkumi kamfanonin manyan motoci a kasar sun sami tsaiko a harkokinsu na yau da kullum. Kamar yadda Trump ya yaɗa a shafinsa ta twitter duk kamfanin da ya ci gaba da aiyanar da kasuwanci da lran bayan takunkumin da aka sake kakkaɓa ma ta, Amurka zata dakatar da dukkan hurɗar kasuwanci da ita.

A ɗayan barayin kuma, duk da zafafan kalaman shugaba Trump ƙasashen Tarayyar Turai sun ƙalubalanci takunkumin. Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Mass ya fito ƙarara ya nuna ci gaba da goyawa kanfunan nahiyar Turai dake gudanar da aiyuka a lran baya. Maas da ya yi alƙawarin baiwa kanfunan nahiyar Turai dake ƙasar Iran gudunmawar kudi ya nuna bakin cikinsa akan takunkumin da Amurka ta sake kakkaɓawa lran. Heiko Mass ya bayyana cewar dangantakar ƙasashen su da lran bai ta'alaƙa ga cin riba ba, yana da nasaba ne da buƙatar da kasashen ke dashi na rage dogaro ga man fetur da iskar gas din Rasha, ministan ya ƙara da cewa kasancewar yadda Amurka ta fice daga yarjejeniyar da aka ƙulla da ita da wasu ƙasashen nahiyar Turai akan lran ka iya sanya dangantakar Amurkan da nahiyar Turai samun tangarɗa.

Ganin yadda Amurka ke ƙara ɗaukar matakan kakkaɓa takunkumi a fadin duniya na nuni ga sauyin hurɗar ƙasar da sauran ƙasashen duniya. Kamar yadda Amurka ta yi wa Turkiyya barazanar kakkaɓa mata takunkumi akan lamarin Brunson, haka kuma ta kakkaɓawa Rasha takunkumi. Bugu da ƙari, ƙara haraji akan wasu kayyayakin da China ke shiga dasu Amurka ma, wani nau'i ne na ci gaba da kakkaɓa takunkumi a ƙasashen duniya. Amurka, wacce ke ci gaba da daukar matakan da suka saɓawa Majalisar Dinkin Duniya akan Falasɗinu, matakan takunkumin da take ƙalubalantar ƙasashe dasu zasu amfanar da ita ne kawai na ɗan lokaci, a haƙiƙanin gaskiya wannan sabon salon Amurkan zai jefa ta cikin ƙaƙanikayi in tafiya ta yi nisa. Amurka dai ta kama hanyar zama ita ɗaya tilo a harkokin ƙasashen duniya.


Tag: Takura , Nufi , Iran

Labarai masu alaka