Pakistan ta yi kira ga Indiya kan su sasanta junansu

Sabon Firaministan Pakistan Imran Khan yayi kira ga takwaransa na Indiya Narendra Modi da su koma teburin tattaunawa don sasanta tsakaninsu.

Pakistan ta yi kira ga Indiya kan su sasanta junansu

Sabon Firaministan Pakistan Imran Khan yayi kira ga takwaransa na Indiya Narendra Modi da su koma teburin tattaunawa don sasanta tsakaninsu.

A wasikar da Khan ya aike wa da takwaran nasa na Indiya ya ce, akwai bukatar sake sabar da teburin sulhu don warware matsalolin da ke damun kasashen 2.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce, an rubuta wasikar ne don bayar da amsa ga wasikar taya murna da Modi ya aike wa Khan.

A wasikar an bayyana cewar yankunan da za a yi sulhu a kansu su ne, Kashmir, Sir Creek da Siachen.

Khan ya bayyana cewar yana son gana wa da Modi a Babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a a New York.Labarai masu alaka